Osimhen zai yi jinyar mako hudu zuwa shida in ji Napoli

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Napoli ta sanar a ranar Litinin cewa Victor Osimhen ya ji rauni, lokacin da yake buga wa kasarsa Najeriya wasan sada zumunta da Saudiyya a ranar Juma'a.

Mai shekara 24, ya ji rauni a karawar da Super Eagles ta tashi 2-2 da Saudiyya a Portugal.

Ko da yake, Napoli ba ta fayyace ranar da zai kammala jinya har ya koma buga mata kwallo ba, amma ana cewar zai yi mako hudu zuwa biyar yana jinya.

Hakan na nufin Osimhen, ba zai buga wa Napoli wasan da za ta ziyarci Hellas Verona ranar Asabar ba a gasar Serie A, da kuma wasan Champions League tsakaninta da Union Berlin ranar 24 ga watan Oktoba.

Haka kuma dan wasan tawagar Najeriya, ba zai yi wa Napoli wasan Serie A da za ta kece-raini da AC Milan ranar 29 ga watan Oktoba ba.

Napoli tana mataki na biyar a teburin Serie A, yayin da Osimhen ke kan gaba a yawan cin kwallaye da fara kakar bana, inda yake da kwallo shida a raga.