Likitoci za su auna girman raunin Osimhen

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Likitoci za su auna girman raunin da dan wasan tawagar Najeriya da Napoli, Victor Osimhen ya ji a karawar sada zumunta da Saudia Arabia.

Ranar Juma'a Super Eagles ta buga wasan sada zumunta da Saudia Arabia da suka tashi 2-2 a Portugal.

Osimhen ya fita daga filin a minti na 55 a fafatawar da aka yi a filin wasa na Portimao da ke Portugal.

Kociyan Super Eagles, Jose Peseiro ya sanar cewar likitoci za su auna girman raunin da Osimhen ya ji.

Watakila ba zai buga wasan sada zumunta da Super Eagles za ta fafata da Mozambique ranar Litinin ba.

Super Eagles za ta buga gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2024, an hada ta rukuni da mai masaukin baki Ivory Coast.

Osimhen ya ci kwallo shida kawo yanzu a Serie A a kakar nan a Napoli, shi ne kan gaba a wannan bajintar.

Napoli ce ta lashe Serie A na bara, kuma dan wasan Najeriya shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a raga.