Real Madrid za ta gabatar da Endrick ranar Asabar

Endrick

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta sanar da cewar za ta gabatar da matashin ɗan wasan da ta ɗauka Endrick a gaban magoya baya ranar Asabar 27 ga watan Yuli a Santiago Bernabeu.

Shugaba, Florentino Perez ne zai yi wa ɗan wasan tarbar girma a birnin Madrid, daga nan zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida.

Bayan an gabatar da ɗan wasan ɗan kasar Brazil, daga nan zai gana da ƴan jarida a Bernabeu.

Shin wanene Endrick ne?

Endrick Felipe Moreira de Sousa ɗan kasar Brazil, ɗaya ne daga matasan da suke haskakawa a fannin tamaula a duniya a wannan lokacin.

Ya lashe lik a Palmeiras, kuma shi ne matashin da ya yi fice a babbar gasar tamaula ta Brazil.

Da yake yana da karancin shekaru, ya samu damar kafa tarihi a fannin tamaula da yawa.

Shi ne na farko da ya buga wa Palmeiras tamaula mai shekara 16 da wata biyu da kwana 15 da cin ƙwallo yana da shekara 16 da wata uku da kwana hudu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuma shi kaɗai ne da ya lashe kofuna a kungiyar da yawa mai karancin shekarun haihuwa.

Endrick ya taka rawar gani a 2022 da yin fice a babbar gasar tamaula ta Brazil, wanda ya ci ƙwallo uku ya bayar da ɗaya aka zura a raga a wasa uku, yana da shekara 16.

Ya kuma ɗauki Sao Paulo Junior Cup, wanda shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan wasa a gasar kuma shi ne zakara a fafatawar matasa ƴan kasa da shekara 20 a Brazil da ta ƴan kasa da shekara 17 da cin ƙwallo uku.

Ya fara daga makarantar koyon tamaula a Palmeiras tun 2016 lokacin da yake shekara 10, wanda ya ɗauki Paulista Championship ta ƴan kasa da shekara 11 da ta ƴan kasa da shekara 13 da kuma ta ƴan kasa da shekara 15.

Ya fara buga wa tawagar Brazil tamaula a Nuwambar 2023, yana da shekara 17 da haihuwa.

Endrick ya cika shekara 18 da haihuwa

Endrick ya cika shekara 18 ranar Lahadi 21 ga watan Yuli, wanda aka haifa ranar 21 ga watan Yulin 2006 a Brazil.

Ana sa ran zai fara buga wa Real Madrid wasanni a kakar 2024/25, wanda za a gabatar da shi a Santiago Bernabeu ranar Asabar 27 ga watan Yuli.