Man United ta tashi 2-2 da Sevilla a Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta tashi 2-2 da Sevilla a wasan zagayen farko a quarter finals a Europa League ranar Alhamis a Old Trafford.
Tun kan tutu United ta ci kwallo biyu ta hannun Marcel Sabitzer a minti na 14, sannan ya kara na biyu minti bakwai tsakani.
Daga nan suka yi hutu, United tana gaba da cin kwallo 2-0.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Sevilla ta farke daya ta hannun Jesus Navas, bayan da ta taba kafar Malacia ta fada raga.
Ta biyun kuwa kyaftin Harry Maguire ne ya sa kai ta fada ragar United, wasan ya koma 2-2.
United ce ta biyu a Ingila da ta ci kanta kwallo biyu a wasan zakarun Turai, bayan Chelsea da ta yi hakan a karawa da Ajax lokacin Ten Hag a Nuwambar 2019.
Karon farko da United ta kasa nasara a gasar zakarun Turai, bayan ta fara cin kwallo biyu tun fafatawa da Basel a Satumbar 2011 da suka tashi 3-3.
Ranar 20 ga watan Afirilu za su buga wasa na biyu na quarter finals a Europa League a Sifaniya.
Wasa tsakanin kungiyoyin biyu:
Europa League Alhamis 13 ga watan Afirilu
- Man Utd 2 - 2 Sevilla
Europa League Lahadi 16 ga watan Agustan 2020
- Sevilla 2 - 1 Man Utd
Champions League Talata 13 ga watan Maris 2018
- Man Utd 1 - 2 Sevilla
Champions League Laraba 21 ga watan Fabrairun 2018
- Sevilla 0 - 0 Man Utd











