An kama ƴar Najeriya da ta yi safarar jaririya zuwa Landan ta hanyar amfani da takardun bogi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sanchia Berg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, News correspondent
- Marubuci, Tara Mewawalla
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 6
A bazarar bara, an kama wata mata a filin jirgin sama na Gatwick bayan ta taso daga Najeriya tare da wata jaririya.
Matar ta kasance tana rayuwa a West Yorkshire ne tare da mijinta da yaranta, sannan kafin ta koma Afirka daga Birtaniya, ta ce tana ɗauke da juna biyu. Amma ashe ƙarya take yi.
A lokacin da ta koma tare da jaririya bayan wata ɗaya, sai aka kama ta bisa zargin safarar mutane.
Wannan lamarin na cikin irinsa da dama da BBC ta bibiya a kotun iyali, wanda ya ƙara fito da abin da masana suke kira da abin damuwa na yadda ake shigar da jarirai Birtaniya ta ɓarauniyar hanya - wasu jariran ma daga "gidajen ƙyanƙyashe jarirai" a Najeriya.
'Ba a ganewa idan ina ɗauke da juna biyu'
Matar wadda muka kira Susan a wannan labarin, ƴar Najeriya ce, amma mazauniyar Ingila tun daga watan Janairun 2023 tare da mijinta d yaranta.
Ma'aikaciyar raino ce, inda ta ce ta kasance tana ɗauke da juna biyu, amma sakamakon gwaje-gwaje suka nuna cewa ƙarya ta yi.
Susan ta nanata cewa tana da kwantaccen ciki ne, domin a cewarta ko haihuwar da ta yi a baya, ba a ganewa idan tana da ciki. Ta kuma ce takan samu shekararren ciki, inda ta ce ta taɓa samun cikin da ya yi wata 30 a baya.
A watan Yulin 2024 ne Susan ta tafi Najeriya, inda ta ce ta fi so ta haihu a can, sai ta kira asibitin da take zuwa a Landan ta bayyana musu cewa ta haihu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai likitocin suka shiga ruɗu, inda suka nemi sashen kula da ƙananan yara domin ƙarin bayani.
Da ta koma Landan tare da jaririyar - wadda za mu kira da Eleanor - sai ƴansandan Sussex suka tsare ta.
Bayan kamen, sai aka yi wa Susan da mijinta da Eleanor gwajin DNA.
"Idan gwajin ya nuna cewa ni ce mahaifiyar Eleanor, ina so a yi gaggawar dawo min da ita," in ji Susan.
Amma gwajin ya nuna cewa jaririyar ba ta da wata alaƙa da Susan ko mijinta, sai Susan ta buƙaci a sake gwajin - da sakamakon ya sake nuna babu wata alaƙa, sai ta canja bayani.
Sai ta ce an mata aiki ne na dashen ƙwayar haihuwa ta koma Birtaniya a shekarar 2023, inda aka dasa mata ƙwai, wanda a cewarta hakan ne ya sa gwajin bai zama ɗaya ba.
Susan ta nuna wata takarda daga asibitin Najeriya, wanda wani likita ya ce ta haihu a can, da ma wata wasiƙar da ke nuna dashen ƙwayar haihuwar da aka yi mata.
Ta kuma nuna hotuna da bidiyo waɗanda ta ce ta ɗauka ne a ɗakin haihuwa na asibitin, duk da a ciki ba a gane fuskokin waɗand suke ciki, ciki har da wata mata tsirara a yanayin haihuwa.

Asalin hoton, Alamy
Ba Susan ba ce ta haihu
Kotun iyali da ke Leeds ta tura Henrietta Coker domin ta yi bincike a Afirka.
Ms Coker, wadda ta bayyana sakamakon bincike a kotun, tana da ƙwarewar aiki na kusan shekara 30 a ɓangaren harkokin iyali, inda ta samu horo a Birtaniya, ta yi aiki a can kafin ta koma Afirka da aiki.
Ms Coker ta ziyarci asibitin da Susan ta ce an mata dashen ƙwayoyin haihuwa, amma babu alamar ta yi jinya a rubuce - ma'aikatan asibitin sun faɗa mata cewa takardar bogi ce.
Sai kuma ta je asibitin da Susan ta ce a can ta haihu, inda ta ga wani ɗan ƙaramin gida mai ɗaki uku, "cike da dauɗa."
Sai Coker ta samu "wasu ƙananan ƴanmata uku sanye da kayan ma'aikatan jinya."
Susan ta bibiyi likitan da ya rubuta takardar da Susan ta kai Birtaniya, wanda ya ce, "lallai akwai wata wadda ta haihu a wajenmu."
Amma da Coker ta nuna masa hoton Susan, sai ya ce ba ita ba ce.
"Harƙallar sayar da jarirai a nan ba sabon abu ba ne," in ji shi, inda ya bayyana cewa wataƙaila Susan "sayen jaririyar ta yi."

Asalin hoton, Supplied
Akwai wata harƙalla da ake yi a Afirka ta "ƙyanƙyasar jarirai" inda ake tara mata suna haihuwa ana sayar da jariran, kamar yadda Coker ta bayyana a kotun. Akwai aƙalla "cibiyoyin haihuwar jarirai" guda 200 da ake kulla a Najeriya a shekara biyar da suka gabata, in ji ta.
A cikin cibiyoyin ana tara mata da aka sato, ake musu fyaɗe, a tilasta su haihuwa, sai a ƙwace jariran.
"Wasu lokutan ana sakin ƴanmatan, wasu suna haihuwa wajen haihuwa," in i Coker.
Babu tabbacin ina aka samo Eleanor - amma likitan ya ce wataƙila kyauta aka ba Susan ita.
Amma Coker ba ta samu nasarar gano asalin iyayen Eleanor ba.
A lokacin da ake binciken, an gano wata lambar waya da Susan ta sanya wa suna "Mum of Lagos Baby" wato mahaifiyar jaririyar Legas.
Kimanin mako huɗu kafin ranar da Susan ta ce ta haihu, ta aika saƙon kar ta kwana zuwa ga lambar, inda da ta ce:
"Barka da yamma, ban ga kayan haihuwar ba."
A ranar kuma ita matar ta mayar da martani cewa:
"Maganin haihuwa naira 3.4 m
"Kuɗin asibiti kuma naira 170.
Jimillar wanannan kuɗin ya kai kusan fam 1,700 da kuma fam 85.

Asalin hoton, Getty Images
Susan ta yi ƙoƙarin yin bayani game da saƙonnin wayar, amma mai bibiyarta shari'ar mai suna Tyler ya ce lamarin zai yi wahala.
Ya ce Susan da mijinta sun yi ƙarya wajen bayyana yadda suka samo Eleanor, kuma sun yi yunƙurin yin rufa-rufa ta hanyar amfani da takardun bogi.
A watan Yuli, BBC ta halarci zaman ƙarshe na shari'ar Eleanor, inda lauyan Susan da mijinta suka buƙaci a mayar musu da Eleanor, yana mai cewa yaransu na samun kula sosai, don haka suke so su Eleanor irin wannan kulawar.
Amma Vikki Horspool, wai wakiltar sashen kula da yara daga cibiyar kula da ƙananan yara ta Independent Children and Family Child Advisory Service ba ta amince ba, inda ta ce akwai abin da Susan da mijinta suke ɓoyewa.
Sai alƙalin ya yanke hukuncin ajiye Eleanor a gidan kula da yara, inda ya ƙara da cewa ya san Susan da mijinta ba za su ji ba daɗi.
A sabon tsarin wanda alƙalin ya yanke, Eleanor za ta zama ƴar Birtaniya - amma matsalar ita ce wataƙila ba za ta taɓa sanin asalin iyayenta ba.
Ba Eleanor ba ce kaɗai ta shiga irin wannan halin, domin an taɓa tseratar da wata mai suna Lucy a Manchester a shekarar 2023 a hannun wanda ya ce shi ne mahaifinta.
'Sayar da jarirai'
Ms Coker ta ce ta yi amannar akwa jarirai da dama da aka shiga da su Birtaniya ta ɓarauniyar hanya daga ƙasashen Afirka ta Yamma. Ta ce ta bibiyi gomman matsaloli irin haka a baya, kamar yadda ta bayyana wa BBC.
"Ana haihuwar yara ana sayarwa sosai," in ji ta, inda ta ƙara da cewa, "ba a Afirka kaɗai ba, lamari ne da ya karaɗe duniya."
A shekarar 2021 Birtaniya ta taƙaita dauko ƙananan yara daga Najeriya saboda "zargin safarar ƙananan yara" a ƙasar.
Tun kimanin shekara 20 da suka gabata ne aka gudanar da irin wannan shari'ar a kotun iyali na Birtaniya.
An yi shari'a guda biyu a shekarar 2011 da 2012, inda aka gano wasu ma'urata da ba sa haihuwa, amma suka kawo yaron da suka ce sun haifa.
A shekarar 2013, ofishin jakadancin Najeriya da ke Legas ya hana tafiya Birtaniya da yara sai an yi gwajin DNA.
Coker ta ce akwai mutane da dama a Birtaniya da suke sane da harƙallar, sai dai ta ce hana lamarin yana da wahalar gaske, domin a cewarta, "hana harƙallar daga ƙasashensu na asali ya kamata a fara."
Shugabar ƙungiyar yaƙi da safarar yara ta ECPAT, Patricia Durr ta ce lamarin yana da ɗaga hankali ne, "suna hana yara samun damar hana yara sanin asalinsu.











