Yadda aka kashe ƴar TikTok a Mali saboda goyon bayan gwamnati

    • Marubuci, Basillioh Rukanga
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wasu da ake zargin masu iƙirarin Jihadi ne a ƙasar Mali, sun sace tare da kashe wata shahararriyar ƴar TikTok bayan sun zarge ta da taimaka wa sojojin ƙasar.

Mariam Cissé, mai shekara 20 da ɗoriya wadda ke da mabiya sama da 100,000 a shafinta na TikTok takan wallafa bidiyoyi kan rayuwarta a ƙauyenta na Tonka da ke arewacin yankin Tibuktu, kuma lokaci zuwa lokaci takan bayyana goyon baya ga sojojin ƙasar.

Kisanta ya girgiza al'ummar ƙasar wadda ke fama da ƴan aware tun daga shekara ta 2012.

Kafar yaɗa labaran gwamnatin Mali ta ce matashiyar na amfani da TikTok ne kawai wajen tallata garinta da kuma ƙarfafa wa sojojin ƙasarta gwiwa.

Mali na fama da matsalar toshe hanyoyin shigar da man fetur zuwa babban birnin ƙasar, wanda ƙungiyoyin mayaƙa na ƙasar ke aiwatarwa, lamarin da ya haifar da cikas ga rayuwar al'umma ta yau da kullum, inda ƙungiyar ƙasashen Afirka ta nuna damuwa a kai.

Wasu mutane ne suka sace Mariam a lokacin da take yin bidiyon TikTok kai-tsaye, wato 'Live' a wata kasuwa da ke wani gari mai maƙwabtaka da ƙauyenta, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta ƙasar Faransa ta ruwaito.

"A ranar Alhamis ne masu iƙirarin jihadi suka sace ƴar'uwata," kamar yadda ɗan'uwan Mariam ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP, inda suka ce tana faɗa wa sojojin Mali "wuraren da suke".

A cikin ƙarshen mako ne masu iƙirarin jihadin suka kai ta garin Tonka a kan babur, inda suka harbe ta a babban dandalin garin a gaban al'umma, ciki har da ɗan'uwanta, kamar yadda kamfanin AFP ya ruwaito.

Wata majiyar tsaro ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran cewa an kashe ta ne saboda an zarge ta da ɗaukar bidiyon masu iƙirarin jihadi domin amfanin "sojojin ƙasar Mali."

A cikin wasu daga cikin bidiyoyin da take dauka, tana sanya kayan sojoji, inda a ɗaya daga cikin bidiyon ta rubuta 'Vive Mali' ko 'Long Live Mali', wato Allah ja zaman ƙasar Mali.

Kisan nata na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fama da matsin rayuwa sanadiyyar tsoshe hanyoyin shigar da man fetur da masu iƙirarin jihadi suka yi.

Lamarin ya tursasa wa hukumomi rufe manya da ƙananan makarantu a tsawon makonni.

Tun a wata da ya gabata ne gwamnati ta umarce makarantu su rufe, inda ta ce za ta yi "duk mai yiwuwa wajen maganace matsalar" domin ganin an sake buɗe makarantun.

Sai dai matsalar na ci gaba da muni, inda a ranar Juma'a ma'aikatar harkokin waje ta Faransa ta shawarci ƴan ƙasarta su fice daga Mali tun ana samun jirage masu shiga da fita.

A ranar Lahadi, shugaban hukumar Tarayyar Afirka (AU), Mahmoud Ali Youssouf ya ce "ya damu da ci gaba da taɓarɓarewar tsaro cikin sauri, inda ƴan ta'adda suka toshe hanyoyin shigar kayan buƙata, lamarin da ya munanan halin rayuwar al'umma fararen hula."

Ya yi Allah wadai da "cuzguna wa fararen hula da ake yi da gangan", lamarin da ya haifar da "mummunan yawaitar rasa rayuka da rashin tabbas".

Ya ƙara da cewa a shirye Tarayyar Afirka take ta "tallafa wa Mali da ƙasashen Sahel a wannan yanayi na matsi da suke ciki".

A tsawon makonni, Mali na fama da matsanancin ƙarancin man fetur, musamman a Bamako, babban birnin ƙasar bayan da mayaƙa da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda suka toshe hanyoyi da kuma kai farmaki kan tankokin dakon man fetur a kan hanyoyi.

Mali ƙasa ce da ba ta iyaka da teku, hakan ya sanya hanya ɗaya tilo ta shigar da man fetur cikin ƙasar ita ce ta amfani da tankokin dakon mai daga ƙasashe masu maƙabtaka kamar Senegal da Ivory Coast.

A shekarar 2021 ne sojoji suka karɓe iko da ƙasar Mali, inda suka yi alƙawarin tabbatar da tsaro, to sai dai matsalar hare-haren mayaƙa masu iƙirarin jihadi ta ci gaba a yankunan arewaci da gabacin ƙasar, inda ba ya ƙarƙashin ikon hukumomi.