Abin da ya sa Nijar da Mali da Burkina Faso suka fice daga kotun duniya ta ICC

Lokacin karatu: Minti 4

Ƙasashen yankin Afirka ta yamma uku - Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sanar da ficewar su daga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Ƙasashen sun bayyana cewa matakin nasu zai fara aiki ne nan take.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, shugabannin sun zargi kotun da zamewa "ƴar koren masu mulkin mallaka" wadda take "nuna son zuciya wajen yin hukunci."

Sanarwar wadda shugabannin ƙasashen suka fitar ta kuma zargi Kotun Hukunta Manyan Laifukan ta duniya da hukunta mutane daga ƙasashe marasa ƙarfi, kuma ta nuna cewa "ta gaza" wajen hukunta laufuka mafi muni da ake tafkawa a doron ƙasa.

Wannan dai ɗaya ne daga cikin matakan da ƙasashen uku suka ɗauka a baya-bayan nan bayan ficewarsu daga ƙungiyar haɗin kan yammacin Afirka ta Ecowas, da kuma kafa ƙungiyar ƙasashen Sahle, wato AES.

A shekarar 2003 ne aka kafa kotun ta ICC wadda aka dorawa alhakin hukunta laifukan da suka shafi kisan kare dangi da cin zarafin biladama da laifukan yaki kuma tun lokacin da fara aiki kotun ta ICC ta saurari kararraki 33

Masu sukar kotun ciki har da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame sun zargi kotun da nuna son zuciya ko rashin adalci saboda ta fai maida hanakli kan kasashen Afrika. Sai daui magoya bayan kotun sun ce rashin tasirin fanin shariar kasashen Afrika ne ya sa mutane ko gwamnatoci ke neman adalci a kotun ta ICC

kasashen yannkin Sahel uku wadanda a halin yanzu ke fama da rashin tsaro sakamakon hare haren mayaka masu ikirarnin jihadi sun yanke alaka da wasu kasashen yamma da suka hada Fransa inda suka kula kawance da Rasha domin samun tallafin soji da kuma inganta cinikiya tsakaninsu

Kasashen 33 daga cikin 54 mambobi ne a kotun ta ICC kuma ta ta fara bincike a wasu kasashen Afrika da suka gada jamhuriyat tsakiyar afrika da jamhuriyar dimokradiyar kongo da Kenya da Libya da kuma Mali sauran sun hada da Sudan da Uganda da kuma Ivoyry cost

Yarjebiyar kafa

Yarjejeniyar da ta kafa kotun ta bai wa mambobinta damar janyewa, sai dai matakin zai fara aiki ne bayan shekara guda daga lokacin sanarwar.

A shekarar 2017, Burundi ta zama kasa ta farko kuma daya tilo daga Afirka da ta yi nasarar ficewa daga kotun ta ICC.

Mece ce Kotun hukunta manyan laifuka kuma mene ne aikinta?

Babban aikin kotun hukunta manayan laifuka shi ne gurfanarwa da kuma hukunta mutanen da ake zargi da aikata kisan kiyashi, da laifukan yaƙi da kuma sauran laifuakn cin zarafin bil'adama.

Haka nan kotun takan iya yin bincike tare da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata munanan laifuka da suka zamo abin damuwa tsakanin ƙasashen duniya.

Kotun takan kuma fafutikar da duniya ke yi na yaƙi da cin zarafi ta hanyar tabbatar da adalci.

Maƙasudin kafa kotun shi ne domin a tuhumi masu irin wannan laifuka da nufin zamewa darasi ga na baya ta yadda za a kauce wa faruwar irin waɗannan laifuka.

Kotun ita ce mataki na ƙarshe da za a iya bi, kuma ba an yi ta ne domin maye gurbin kotuna na cikin gida ba, sai dai domin ta taimaka musu.

An samar da kotun ne daga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasashen duniya, wadda ake kira 'Rome Statute.

Ita ce kotu ta farko ta duniya da aka ƙirkira domin hukunta manyan laifuka .

Kotun ICC na son ganin ƙasashe su amince da ita, domin samun ƙarfin yaƙi da cin zarafi da kuma kare faruwar hakan a gaba.

Yanzu haka kotun tana da ma'aikata sama da 900 daga kimanin ƙasashe 100 na duniya.

Kotun na amfani da harsuna shida a hukumance, wato Ingilishi da Faransanci da Larabci da yaren China da na Rasha da kuma Sifaniyanci.

Kotun ta ce ta bayar da sammacin kame 61 ta hanayar haɗin kai da ƙasashen duniya, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.

Haka nan ta samu nasarar tsare mutane 22 waɗanda ta gurfanar a gabanta.

Har yanzu akwai mutane 30 waɗanda ba ta samu damar kamawa ba, inda ta yi watsi da tuhume-tuhume kan mutum 8 sanadiyyar mutuwa.

Daga shekara ta 2002, alƙalan kotun sun bayar da sammacin kama mutum tara domin gurfana a gabansu.

Haka nan sun samu nasarar kama mutum 11 da laifi yayin da suka wanke mutum 4.