Yadda sa-in-sar Trump da Elon Musk ke ƙara tsananta a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Anthony Zurcher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America Correspondent
- Aiko rahoto daga, Washington DC
- Lokacin karatu: Minti 5
Me ya faru a lokacin da attajirin duniya da ɗan siyasar da ya fi kowa iko a duniya suka faru sa-in-sa tare da jan daga?
A yanzu duniya na ƙoƙarin gano - haƙiƙanin abin da ya shiga tsakanin manyan aminan biyu. Trump da Musk na da kyakkyawar alaƙar amintaka, amma a yanzu sun fara sa-in-sa da juna, saboda rashin jituwar da ya rikiɗe ya zama yakin cacar-baka.
Trump ya yi wa kasuwancin Elon barazanar cewa gwamnatin tarayya za ta kawo tarnaƙi ga shirin Elon, wanda kuma shi ne ginshinƙin rayuwar shirinsa na sararin samaniya.
''Hanya mafi sauƙi ta tara kuɗi ga kasafin kuɗinmu, domin samun biliyoyin daloli, shi ne ta hanyar kawo ƙarshen bai wa ayyukan Elon tallafi,'' kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa sada zumunta.
Idan har Trump ya yi amfani da ƙarfin gwamnati kan Elon Musk, to ba shakka attajirin zai ji a jikinsa. Yanzu haka hannun jarin kamfaninsa na Tesla ya faɗi da kashi 14 cikin 100 a ranar Alhamis.
Ba a nan kaɗai gizo ke saƙar ba. Bayan haka, Musk ya yi kiran a tsige Trump, idan har ya kuskura ya yanke kuɗaɗen da ake ba wa kamfanoninsa, ya kuma soke shi da cewa yana yunƙurin dakatar da shirin kumbonsa na Dragon, wanda Amurka ta dogara da shi wajen kai 'yan sama jannatin Amurka da kayayyakin aiki zuwa tashar sararin samaniya ta duniya.
Musk yana da damarmaki marasa iyaka don mayar da martani, ciki har da tallafa wa waɗanda za su ƙalubalanci jam'iyyar Republican a zaɓukan shekara mai zuwa da na fidda gwani. Kuma da yammacin ranar Alhamis, ya ce yana iya "fasa kwai" - ya kuma bayyana cewa Trump ya bayyana a cikin wasu takardu da ba a fitar ba da suka shafi tsohon mai laifin jima'i, marigayi Jeffrey Epstein (sai dai bai bayyana wata shaida game da hakan ba).
Sakatariyar yaɗa labaransa, Karoline Leavitt ta soki Elon Musk game da zarge-zargen nasa.
"Wannan abu ne da bai kamata ba daga Elon Musk, wanda ke fushi da ɗaya daga manyan ƙudurori, saboda kawai bai ƙunshi tsare-tsarensa ba,'' in ji ta.
Ba lallai Musk ya yi nasara a yaƙi da gwamnatin Trump ba, amma zai iya yin tasiri kan siyasa da dangantakarsa da Trump da ma jam'iyyar Republican.
Watakila Trump na sane da hakan, shi ya sa ya son yin magana game da batun, musamman lokacin da ya bayyana a taron yaba wa ƴansanda da aka gudanar da fadar White House ranar Alhamis.
Sannan kuma ya wallafa saƙo a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce ''Sukar da Musk'' ke yi masa ba ta dame shi ba, amma ya yi kaicon ina ma Musk ya fice daga ƙunshin gwamnatinsa watanni da dama suka gabata.
Daga nan ya himmatu wajen haɓaka harajin da ya bayayana da "babban abu mai kyau" da dokokin kashe kuɗi.

Asalin hoton, Getty Images
Musayar kalamai da barazana
Rikicin dai ya faro ne da zafinsa cikin makon da ya gabata, inda aka fara guna-guni a ranar Laraba, ya kuma zama cikakken cacar-baka a ranar Alhamis a ofishin Shugaban ƙasar.
Yayin da sabon shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz - baƙon ranar - ya zauna cikin alamun damuwa, shugaban ya ɗan yi kamar bai ji daɗi ba.
Ya bayyana mamakinsa game da sukar da Elon Musk ke yi wa dokokin.
Ya mayar da martani kan iƙirarin da Musk ya yi cewa in da ba don taimakon biliyoyin daololin da ya bayar ba, da nasara a zaben shugaban ƙasar da ya gabata ba.
Yana mai cewa Musk ya ɗauki sabon matsayin sukarsa ne saboda kamfanin ƙera motocinsa masu amfani da lanki na Tesla, zai fuskanci fara biyan haraji.

Asalin hoton, Truth Social
Ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ''Hanya mafi sauƙi ta samar da kuɗaɗen da za a yi amfani su a kasafin kuɗinmu ita ce gwamnati ta daina bai wa kamfani da ayyukan Elon tallafi. A kullum ina mamakin yadda Trump ya kasa yin hakan''.
Bayan saƙon na Trump, nan take Elon ya mayar da martani a shafinsa na X, mai mabiya miliyan 220, yana mai cewa ''Koma mene ne'' ba mu damu da tallafin motocin da muke ƙerawa ba, ya ce yana so ne ya rage basussukan ƙasa, wanda a cewarsa barazana ce ga al'umma. Ya dage cewa da 'yan Democrat sun yi nasara a zaɓen bara ko da ba da taimakonsa ba. "Irin wannan rashin godiya," kamar yadda ya shaida wa Trump.
Daga nan ne kuma attajirin ya fara wallafa jerin saƙonnin suka da duka ranar, lamarin da ya ƙara rura wutar saɓanin nasu.

Asalin hoton, X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Musk da Trump sun ƙulla wani ƙawance mai ƙarfi, lamari da ya sa attajirin ya samu babban matsayi - na lura da kashe kuɗin gwamnati - a ƙunshin gwamnatin Trump.
Hukumar da aka bai wa Musk wadda aka fi sani da Doge, ta kasance ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka bayar da kanun labarai a kwana 100 farko na gwamnatin Trump, saboda yadda ta kashe tallafin hukumomin duniya masu yawa tare da korar dubban ma'aikata.
Sai dai ba a je ko'ina ba, aka fara yaɗa jita-jitar taƙun-saƙar kan yaushe kuma ta yaya manyan aminnan za su samu saɓani.
An ɗan ɗauki lokaci, kafin wannan hasashe ya fara bayyana. Trump ya goyin bayan Musk - duk da cewa farin jininsa ya ragu - yayin da ya yi jayayya da jami'an gwamnati saboda yadda ya bayar da gudunmowa a zaɓukan da suka gabata.
A duk lokacin da ɓaraka ta kunno kai, Musk zai bayyana a ofishin shugaban ƙasa, ko zauren majalisar ministoci ko a ckin jirgin shugaban Amurka domin ɗinke ɓarakar.
A lokacin da Musk ya kawo ƙarshen kwana 130 a kan matsayinsa a makon da ya gabata, shi da Trump sun zanta a ofishin shugaban ƙasa, har da ƴar ƙwarya-ƙwaryar walima aka shirya masa a fadar White House, inda aka yi fatan wata rana aya sake dawowa kan muƙamin nasa.
'Rikici ne maras riba ga kowa'
Abin jira a gani yanzu sh ne inda rigimar za ta dosa. Zai iya yi wa ƴan wasu jam'iyyar Republican tsauri su ci gaba da goyon bayan ƙudirin Trump, saboda wataƙila Musk ka iya yin tasiri a kansu, watakila saboda tallafin da ya bai wa jam'iyyar.
Trump ya riga ya yi wa Musk barazana da kwangilolin gwmanati, amma kuma yana iya amfani da abokan aikin Musk a hukumar Doge, waje sake buɗe binciken da ake yi masa tun lokacin Biden kan harkokin kasuwancinsa.
A yanzu dai komai zai iya faruwa.
A gefe guda kuma jam'iyyar Democrats na kallo tare da tunanin yadda za ta mayar da martani. Wasu daga cikin na fatan sake karɓar Musk, wanda ama tsohon mai tallafa wa jam'iyyar ne, saboda abin da nan masu iya magan ke cewa ''maƙiyin maƙiyinka, abonkinka ne''.
"Rikicin ba shi da riba ga kowa," in ji Liam Kerr, matsanin dabarun Demokradiyya. "Duk wani abu da ya yi da zai ƙara kusanta shi ga Democrat zai iya cutar da 'yan Republican."
A nata ɓangare Jam'iyyar Democrats za ta yi farin cikin ganin manyan amininan byu na cacar baka, kuma idan ba a kawo ƙarshen saɓanin ba, hakan zai shafi siyasar Amurka.
Amma ba a tunanin zai zo ƙarshe a nan kusa.
"Saura shekara uku da rabi Trump ya ƙare mulkinsa," kamar yadda Musk ya rubuta a shafinsa na X, "amma ni zan kasance ina nan har nan da shekara fiye da 40 masu zuwa."










