Me ya sa mata suka fi maza yawan yin fitsari?

Hoton ban-ɗaki

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Michelle Spear
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Conversation*
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zai yiwu a rayuwa ta yau da kullum mu lura cewa mata na yawan zagayawa fiye da maza.

Wasu za su iya tunanin cewa ko halittar mafitsara ta maza ta fi ta mata girma ne?

Amsar wannan ita ce: Ba haka ba ne. Wannan kuma bayani ne mai sarƙaƙiya kadan, wanda ya jiɓanci halitta da ɗabi'a da kuma yanayin tunani.

Zai yiwu mata su fi jin yin fitsari a kai a kai fiye da maza, to amma babu wani dogon bambanci tsakanin girman mafitsarar mace da ta namiji.

Mafitsara wata jakka ce mai kama da balan-balan da ake samu a marar ɗan'adam. Akwai fata biyu da suka samar da jakkar.

Fata ta farko ita ce ake kira 'detrusor' a turance, wadda take daga waje, sai kuma ta biyu da ake kira transitional epithelum, wadda take a ciki.

Fatar 'detrusor' wadda ke a waje tana da yauƙi, inda take iya buɗewa ko ta tsuke kamar balan-balan domin bai wa mafitsara damar adana fitsari mai yawa ba tare da mutum ya matsu ba. A lokacin da ta cika shi ne mutum kan ji ya matsu, kuma yana buƙatar zagayawa.

Ita kuwa fatar da ke ciki, wadda ake kira 'transitional epithelium' ita ma tana iya buɗewa domin karɓar ƙarin fitsari da ke taruwa, haka nan tana kare jikin mafitsara daga sinadarai masu cutarwa da ke a cikin fitsari.

Mafitsara na da halitta mai kyawu da kuma juriya ta yadda duk buɗewa da kuma tsukewar da take yi sanadiyyar ƙaruwa da raguwar fitsari a cikinta, ba ta hujewa ko fashewa har tsawon rayuwa.

La vessie des hommes et des femmes peut contenir confortablement entre 400 et 600 millilitres d'urine.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Halittar mafitsarar mace da namiji kusan ɗaya ne

A tsarin halitta, kamannin da ke tsakanin mafitsarar maza da ta mata ta fi yawa a kan bambancin da ke tsakanin su.

Dukkaninsu na iya ajiye fitsarin da yawan shi ya kai tsakanin mililita 400 zuwa 600. Fatar da ta kewaye mafitsara tana iya shafar yadda mutum ke matsuwa a lokacin da yake jin fitsari.

Za a iya cewa a nan ne bambancin yake.

A maza, mafitsara tana kasancewa ne a saman gammon mafitsara (prostate), kuma a gaban babban hanjin da ke gab da dubura.

A mata kuma, mafitsara kan kasance ne a wani loko da ke tsakankanin ƙashin kunkuru, inda take a wuri ɗaya da mahaifa da kuma al'aurar mace ta ciki.

A lokacin da mace ke da juna-biyu, ƙarin girmar mahaifa na takura mafitsara, abin da kan sanya mace ta buƙaci zuwa ban-ɗaki a kai a kai, kusan cikin kowane minti 20 a lokacin da cikin ya shiga wata uku na ƙarshe.

Maza na fitsari a ban-ɗaki

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ko a lokacin da mace ba ta da juna-biyu, rashin isasshen filin walawa a inda mafitsara take na iya sanyawa mace ta ji tana jin fitsari da sauri fiye da namiji.

Wasu bincike-bincike da aka gudanar sun nuna cewa wasu mata sun fi shiga yanayin jin fitsari cikin sauri sanadiyyar sauyin sinadaran jiki da kuma yanayin girman lokon kunkuru da mafitsara ke zaune a ciki.

Tsokar da ke ƙasan lokon kunkuru, inda mafitsara da mahaifa da kuma babban hanji ke zama a kai na da matuƙar muhimmanci.

A halittar mata, haihuwa da sauyi a sinadaran jiki ko kuma tsufa na iya raunanar da su, abin da ke iya kawo cikas ga yadda mafitsara ke riƙe fitsari.

Sai dai wani abu mai muhimmanci wajen riƙe fitsari shi ne zoben bututun fitsari wanda ake kira 'urethral sphincter' a turance. Wata tsoka ce mai da'ira wadda ke zama tamkar makullin mafitsara, wadda kan taimaka wajen hana fitar fitsari har zuwa lokacin da mutum ya samu inda zai tsuguna.

Sai dai kuma wani abin da ke iya haddasa yawan fitsari ga mata shi ne cutukan bututan fitsari (wadda ta fi yaɗuwa tsakanin mata saboda rashin tsawon hanyar fitar bawali), zai iya sanyawa mafitsara ta riƙa saurin ankararwa game da fitsari, kuma matsalar za ta iya ci gaba da faruwa ko bayan an yi maganin cutar.

'Je ki yi fitsari'

Ɗabi'ar ce wa yara mata su je su yi fitsari, musamman lokacin da suke ƙanana, inda kuma akan horar da su kan su guje wa shiga ban-ɗaki na kowa da kowa.

Hakan na haifar da yanayin tsane mafitsara kafin ta cika, wanda hakan ke daƙile damar mafitsara ta faɗaɗa.

Hoton mace mai ciki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A cikin watanni uku na ƙarshen juna-biyu, matsi kan ƙaru a kan mafitara ta yadda masu ciki kan yi saurin jin fitsari

A ɓangare ɗaya maza ba a cika matsa musu su yi fitsari ba lokacin da suke ƙanana.

Mafitsara kan saba da irin ɗabi'ar da aka horas da ita.

Horas da mafitsara, wani abu da hukumar lafiya ta Birtaniya kan ƙarfafa gwiwar a yi, ta ƙunshi tsawaita jinkirin da mutum ke yi tsakanin yin fitsari na yanzu zuwa fitsari na gaba.

Wannan na taimakawa wajen saita musayar bayanai da ake samu tsakanin mafitsara da kuma ƙwaƙwalwa, lamarin da kan rage samun yawan matsuwa.

Saboda haka nan ba lallai ne a ce mafitsarar mata ta fi ƙanƙanta ba, sai dai ba ta da isasshen wurin walawa.

Saboda haka yawan fitsari ga mata haɗi ne na halitta da ɗabi'a da kuma sauyin da akan samu lokaci zuwa lokaci a jikin mace.

Farfesa Michelle Spear malamar koyar da likitanci ce a Jami'ar Bristol da ke Birtaniya.