Rasha na bincike kan mummunan harin 'yan bindiga a Moscow

Jami'an tsaro a Moscow

Asalin hoton, OTHERS

Hukumomin Rasha sun ce sun fara gudanar da bincike kan wani harin da 'yan bindiga suka hallaka akalla mutum sittin da jikkata daruruwa a harin da aka kai wani zauren raye-raye da ke kusa da Moscow.

Har yanzu Rasha ba ta ce ga wanda ta tabbatar yake da alhakin kai harin ba, amma ta danganta shi da ta’addanci, duk da cewa kungiyar masu ikirarin jihadi ta IS ta bugi kirjin kai shi.

Amurka ma ta ce tana da bayanan sirri da ke iya alakanta harin da IS.

Kwamitin bincike na Rasha, wanda shi ke gudanar da bincike kan manyan laifuka, ya ce ya fara gudanar da bincike a kan harin karkashin dokar yaki da ta’addanci.

Svetlana Petrenko ita ce mai magana da yawun hukumar binciken:

''Sakamakon abin da ya faru a zauren Crocus City babbar hukumar bincike ta kwamitin bincike na Rasha ta fara gudanar da bincike na mugun laifi a karkashin doka ta 205 ta miyagun laifuka ta kasar Rasha. An tura jami’ai masu bincike na babbar hukumar ta rasha zuwa wurin,’’ in ji ta.

Wasu hotunan bidiyo na harin da aka sanya a shafukan sada zumunta da muhawara sun nuna wasu mutum hudu sanye da kayan soji na rawar daji sun bude wuta a lokacin da suke shiga zauren da abin ya faru.

Kafofin yada labarai na Rashar sun ruwaito cewa an ji fashewa daga bisani sannan kuma wata wuta gangaganta ta mamaye ginin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Harin wanda shi ne mafi muni a kusan shekara ashirin a Rasha.

Gwamnatin Amurka ta ce sau da dama an sanar da hukumomin Rasha cewa ‘yan bindiga da ke da alaka da kungiyar IS na shirya kai hari a kasar.

A farkon watan nan ofishin jakadancin Amurka a Moscow ya fitar da wani gargadi na yuwuwar kai hare-hare kuma musamman ma ya ambaci wuraren raye-raye.

Sai dai ‘yan kwanaki hudu da suka gabata Shugaba Putin ya yi watsi da wannan gargadi, inda ya nuna cewa wani yunkuri ne na dasa tsoro da rikita kasar.

Tun da farko Ukraine wadda Rasha ke yaki da ita ta nesanta kanta daga harin.

Har yanzu Shugaba Vladimir Putin bai yi jawabi ga ƴan ƙasar kai-tsaye ba kan harin sai dai kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ce ya yi wa wadanda suka jikkata a harin fatan samun sauƙi.

Kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da harin da ya kira da mummunan harin ta'addanci, wanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasar.

Tun da farko ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi kira ga duniya da ta yi Allah- wadai da harin.