Abun da ya sa Putin ke samun ƙarfin iko fiye da kowane lokaci

Asalin hoton, Getty Images / BBC
Shugaba Vladimir Putin ya lashe zaɓe karo na biyar, inda zai ci gaba da jagoranci har shekara ta 2030.
A jawabin da ya yi bayan samun nasara, ya ce nasararsa za ta sanya Rasha ta ƙara samun karfi da kuma yin tasiri.
Ya lashe zaɓen ne da gagarumar nasara inda ya samu kashi 87 na kuri’un da aka kada, abin da ya zarce wanda ya samu a zaɓen da ya gabata na kashi 76.7 na kuri’un. Duk da cewa bai samu wani adawa mai karfi ba, fadar Kremlin ita ke iko da tsarin siyasar ƙasar, da kafafen yaɗa labaru da kuma zaɓuka.
Shugabannin ƙasashen yamma da dama sun yi Alla-wadai da zaɓen inda suka ayyana shi a matsayin mai rashin inganci, ciki har da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda ya kira Putin a matsayin mai mulkin kama karya wanda kuma giyar mulki ta buga, inda ya ƙara da cewa: "Zai iya yin komai domin ci gaba da zama a kan mulki."
Putin, mai shekara 71, wanda ya fara shugabanci a ranar karshe ta shekarar 1999 - ya kasance shugaban ƙasar mafi daɗewa kan mulki tun bayan Joseph Stalin, kuma a halin yanzu zai karya tarihin da mutumin mai mulkin kama-karya na tarayyar Soviet ya kafa a baya.
Duk da cewa ƴan Rasha na mutuwa a yaƙin da take yi da Ukraine, wanda ke shiga shekara ta uku da farawa, yayin kuma da Rasha take ƙara zama saniyar ware tsakanin ƙasashen yamma, ga wasu dalilai da suka sa Putin ya ke da karfin iko da ba a taɓa gani a baya ba.
Take ƴan adawa da ke sukar gwamnati

Asalin hoton, Getty Images / BBC
"Putin ya san yadda zai kawo karshen duk wata tattaunawa ta siyasa a ƙasar," in ji Andrei Soldatov, wani ɗan jaridar ƙasar Rasha wanda yake zaman mafaka a Landan tun bayan da aka tilasta masa tserewa a 2020. "Kuma ganin cewa ya kware a kan haka, yana kuma da dabara ta yadda zai cire abokan adawarsa na siyasa," in ji Andrei.
Wasu ƴan takara guda uku ne suka fito a takardar kaɗa kuri'a a 2024, kuma babu wanda ya nuna alamar ƙarawa da Putin. Dukkansu sun nuna goyon baya ga shugaban ƙasar da kuma yaƙin da ake yi a Ukraine.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk wanda ke da barazana ga shugaban ƙasar ya kasance ko an aika shi gidan yari, ko kashe shi ko kuma cire shi kan mukaminsa, duk da cewa Kremlin ta musanta hannu a haka.
Ƙasa da wata ɗaya kafin buɗe rumfunan zaɓe, babban abokin adawar Putin, mai shekara 47 Alexei Navalny ya mutu a wani gidan yari da ke wani yanki mai tsananin sanyi kamar yadda kamfanonin dillancin labarai suka ruwaito. Ya kasance yana ɗaure tsawon lokaci kan zargin rashawa, saɓawa kotu da kuma nuna tsassaurar ra'ayi, sai dai an soki hakan da cewa yana da alaƙa da siyasa.
"Putin ba ya sararawa abokan adawarsa,"in ji Soldatov. "Martaninsa kan mutumin da yake da muhimmanci a siyasa shi ne kisa, amma fadar Kremlin ta sha musanta kashe abokan adawa inda Putin ya ce me ya sa zan kashe su?' Kremlin na da wata ɗabi'a ta nuna cewa ba ta da hannu a kan irin waɗannan abubuwa."
Manyan masu kalubalantar Putin mutuwa suke yi kama daga ƴan siyasa zuwa ƴan jarida.
A bara, shugaban ƙungiyar sojojin hayar Rasha ta Wagner, Yevgeny Prigozhin ya mutu, a wani hatsarin jirgin sama watanni kalilan bayan yunkurin tawaye da suka yi. A 2015, aka harbe tare da kashe wani mai suka kuma dan siyasa, Boris Nemtsov, a kan wata gada kusa da Kremlin. A 2016, an samu gawar wani ɗan jarida a Moscow, wanda ya kasance mai suka kan yaƙin da ake yi a Chechnya, Anna Politkovskaya.
"Yana da haɗari rayuwa a ƙasar da ake kashe ƴan jarida da ƴan siyasa, su kuma ƴan gwagwarmaya a kashe su ko a ɗaure su a gidan yari," in ji Soldatov. "Mutane na son bin abin da Kremlin ta ce ba wai don suna so ko yin imani da shi ba, sai dai saboda muna son samun hanyar rayuwa da shi."
Putin ya kuma yi kokarin take mutanen da ke adawa da tsare-tsarensa a cikin al'umma. Tun 2022, bayan mamayar Ukraine, fadar Kremlin ta ɓullo da dokokin tace bayanai da kuma take duk waɗanda ke adawa da gwamnati, furta magana da zai zubar da kimar "sojojin Rasha" wanda hukuncinsa ya kasance ɗaurin shekara biyar a gidan yari.
Shugaban ƙasar ya ce za a hukunta masu zanga-zanga a wannan lokaci na zaɓe bayan kammala kaɗa kuri'a.
"Yanzu ba wai wasu rahotanni a tashar BBC ko Radio Free Europe ba" in ji Soldatov. "Magana ake kan mutanen da za su ga abu a kan titi sannan su wallafa shi nan take inda miliyoyin mutane kuma za su yaɗa shi.
"Putin yana son kare ƙasar daga karyewa, shiya sa ya yi imanin cewa akwai buƙatar ya yi komai domin danne masu adawa da shi kowane iri saboda sauyi na iya farawa daga kan mutum biyu ko ƴan mata uku da ke zanga-zanga a kan titi."
Yaƙin Ukraine

Asalin hoton, Getty Images / BBC
A wani taron manema labarai bayan zaɓe, Shugaba Putin ya sha alwashin ci gaba da fafata yaƙi a Ukraine.
Yaƙin da yanzu ya shiga shekara ta uku, abubuwan da suka faru ba su mutane da dama daga Rasha ke tsammani ba, sai dai Dr Ekaterina Schulmann, masaniya kan kimiyyar siyasa da ke zama a Berlin, ta bayyana cewa Putin na samun galaba a yaƙin.
"Lokacin da aka fara yaƙin, bai kasance kaɗan ko mai zubar da jini ba kuma hakan ya shafi yadda ƴan Rasha ke kallon kansu, kallon waje da kuma shugabansu".
Dr Schulmann ta yi imanin cewa mamayar da aka fara a ranar 24 ga watan Febrairun 2022 ba wani babban abu bane ga Rashawa, saboda ya ta'allaka ne ga waɗanda ke wajen ƙasar. "Akwai annashuwa da kuma farin ciki lokacin da mutane a Rasha suka yi ta ɗaga tutar ƙasar. Sai dai da yaƙin ya fara tsananta a watan Satumban 2022, fargaba ta ƙaru, mutane sun shiga tsoro kuma goyon bayan yaƙin ya ragu matuka," in ji ta.
Soldatov ya amince da kuma yin imanin cewa, ganin raguwar goyon bayan da yaƙin ya samu a farko, sai Putin ya sauya akala.
"A yanzu ba yaƙi ne da Ukraine ba, in ji shi, "sai dai maimakon haka yaƙi ne da ƙasashen yamma, kuma hakan ya sanya ƴan Rasha da dama na alfahari saboda sojojinsu ba wai suna faɗa da karamar ƙasa ba, amma na faɗa da manyan abokan gaba".
A jawabin da ya saɓa yi wa ƴan ƙasar na shekara-shekara a ranar 29 ga watan Febrairu, Putin ya gargaɗi ƙasashen yamma kan aika dakaru zuwa Ukraine kuma ya ce Rasha na buƙatar karfafa dakarunta ganin cewa Sweden da Finland sun shiga Nato.
"Kowaye a ƙasar, ciki har da ni, an koya mana a makaranta cewa Daular Rasha ita ce daula kaɗai a duniya wadda aka kafa da mutane masu zaman lafiya," a cewar Soldatov. "Kowaye na son kawo mana hari don haka idan ka faɗa cewa Nato na tinkarar iyakar ƙasar ka, mutane za su amince da kai."
Soldatov ya ce ƙasashen yamma ba su bayyanawa duniya kan me ya sa yaƙin Ukraine ke da muhimmanci ba. "Alal misali, Mutane a Afrika, Kudancin Amurka, ba su san me ya sa za su nuna kulawa ba, kuma wannan shi ne abin da Putin ya yi amfani wajen ci gaba da fafata yaƙi," in ji shi.
"Putin ya iya taku na yadda yake tafiyar da tarihin da tarayyar Soviet ke da shi kuma hakan ne ya sa nahiyar Afrika ke ƙara zama muhimmanci a gareta kuma wasu daga cikin ƙasashen na bayar da taimakon kayayyaki da kuma na soji."
Girman tattalin arzikin Rasha

Asalin hoton, Getty Images / BBC
Duk da irin tarin takunkumi da aka kakaba wa Rasha bayan mamayar da ta yi a Ukraine, ƙasar ta bai wa masana tattalin arziki da dama mamaki ta hanyar zama ƙasar da tattalin arzikinta ke haɓaka cikin sauri a Turai.
"Tattalin arzikin na cikin yanayi mai kyau, dukkan abubuwa na tafiya yadda ya kamata, kuma hakan ya saka Putin zama sananne saboda ya sake nuna kansa a matsayin mutumin da ya bijire wa Yamma kan takunkumi da suka saka wa tattalin arzikin Rasha," in ji wakilin BBC a ɓangaren kasuwanci, Alexey Kalmykov.
Maimakon faɗuwa ƙasa kamar yadda mutane da dama suka yi tsammani, tattalin arzikin Rasha ya ƙaru da kashi 2.6, a cewar kiyasin Hukumar Ba Da Lamuni ta Duniya (IMF), duk da takunkuman Yamma, da suka haɗa da hana Rashar taɓa kuɗinta da ya kai $300b.
Sai dai waɗannan takunkumai ba su yi aiki a faɗin duniya ba. Wannan ya bai wa Rasha damar hulɗar kasuwanci da ƙasashen China, Indiya da kuma Brazil yayin da makwabta, ciki har da Kazakhstan da Armenia, na taimaka wa Rasha kauce wa takunkuman Yamma.
"Tattalin arzikin Rasha na da grima," in ji Kalmykov, ya ƙara da cewa: "Za a ɗauki tsawon gomman shekaru kafin takunkumai ko ɓarnar kuɗi su kai tattalin arzikin Rasha ƙasa amm dai ba yanzu ba."
"Rasha na samun kuɗi ta hanyar fitar da kayyaki waje kuma tana da damar sayar da duk abin da take so," a cewar Kalmykov. "takunkumi kan man fetur na je ka nayi ka one, sai dai babu takunkumi kan iskar gas da kuma nukiliya daga Tarayyar Turai saboda suna cikin waɗanda ke sayen abubuwan daga Rasha."
Dr Schulmann ya ce duk da cewa farashin kayyaki ya ninka har sau huɗu ba kamar a baya ba, a shirye suke, wanda ta ce yana da muhimmancin gaske.
"An san Rasha da ƙara farashin kayayyaki. Fargabar da muke da ita ba wai ta hauhawar farashi ba ne, sai dai illa giɓi.
Kalmykov ya amince cewa: "Abu ɗaya shi ne farfagandar Putin na iya yin tasiri matuka."
Karfin ikon Putin ba zai kasance har abada ba...
Duk da cewa ta nuna Putin a matsayin mai karfin ikon da ba a taɓa gani ba a baya, Dr Schulmann ta yi gargaɗin cewa akwai lokacin da hakan zai kawo karshe.
Putin na da damar kasancewa a kan mulki na akalla wa'adi biyu, abin da ke nufin cewa za yi mulki har zuwa shekara ta 2036 - lokacin da zai cika shekara 83. Hakan ya faru ne sakamakon garanbawul ɗin kundin tsarin mulkin ƙasar da aka yi a 2020 byan kuri'ar jin ra'ayin jama'a na faɗin ƙasa.
"Yin ritaya ba abu ne mai yiwuwa ba," a cewar Dr Schulmann , inda ta ƙara da cewa: "Magana ta gaskiya ita ce zai mutu a kan mulki kuma mutanen da ke da irin ra'ayinsa ne za su gaje shi."
Sai dai Dr Schulmann ta ce hakan ba zai faru ba. Ta ce shekaru na ƙara cimma tsarin ƙasar Rasha wanda wani da ba matashi ba ke jagoranta, inda ta karkare da cewa "an mayar da hankali kan mutumin da ba zai kasance har abada ba".











