Yadda maza da mata ke amfani da harshe daban-daban a gari guda

Hausawa kan ce ''Allah daya, gari bambam'', domin kuwa, yayin da wasu al'ummomi na duniya ke amfani da harshe daya tsakanin mata da maza, wajen zantuttuka da mu'amalar yau da kullum, a garin Ubang na yankin karamar hukumar Obudu ta jihar Kuros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya ba haka abin yake ba.

Mutanen garin Ubang na amfani da harsuna biyu ne, wato harshen maza daban, na mata daban.

Al'ummar ta Ubang dai kamar sauran al'ummomi, ita ma tana da nata al'adu da dabi'u da suka bambanta da sauran wasu al'ummomi.

Sai dai mafi ban al'ajabi shi ne batun harasa biyun da mata da maza ke amfani da su.

Chief Osang Isaiah, mai unguwa ne a garin Ukwerisen a yankin na Ubang, ya shaida wa wakilin BBC Abdussalam Ibrahim Ahmed, da ya kai ziyara garin cewa, harsuna biyun da ake amfani da su a garin nasu su ne Jiye-Ban-Chiye, wanda shi ne wanda maza ke amfani da shi, sai kuma Jiye-Ban Yiye, na mata.

Basaraken, ya ce harsunan biyu da suke da su wata baiwa ce daga Ubangiji domin a bambanta maza da mata.

Chief Osang Isaiah, ya ce “A tarihance, mutanen Ubang sun samu asali ne tun halittar bil-Adam, kuma tushen mutanen na Ubang ya samu ne daga wani waje da ake kira Agbutan.

Basaraken ya ce idan kana da yara maza da mata tun suna kanana ake banbance musu harshen da zasu yi amfani da shi, idan sun girma wato na maza da mata.