Iyayen da suka kai ƴaƴansu yawon ganin duniya kafin su makance

Iyayen da suka kai ƴaƴansu yawon ganin duniya kafin su makance

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A lokacin da aka gano cewa uku daga cikin ƴaƴan Edith da Sébastian huɗu suna fama da wata cuta da za ta iya makantar da su, sai iyayen suka kai su yawo a ƙasashen duniya daban-daban don su samu abin da za su dinga tunawa a idon zuci idan suka makance ɗin.

Cutar idanun mai suna retinitis pigmentosa, cuta ce da ake kamuwa da ita tun daga lokacin haihuwa.

Yawanci cutar ba ta nuna alamu.

A yanzu haka iyalan suna cikin wata na shida da fara zagaye ƙasashen duniyar inda tuni suka je Namibia da Zambia da Tanzania da Turkiyya da Mongolia da Indonesiya.