Mutumin da ya shafe shekaru 50 bai yi wanka ba ya rasu

Asalin hoton, AFP
Mutumin da ake gani a matsayin 'wanda ya fi kowa kazanta a duniya' ya rasu yana da shekaru 94, watanni kaɗan bayan ya yi wanka a karon farko cikin tsawon shekaru.
Amou Haji ya shafe kusan shekaru hamsin bai yi wanka da soso da sabulu ba, saboda tsoron cewa zai yi rashin lafiya.
Ɗan ƙasar Iran ɗin wanda ke zaune a kudancin lardin Fars, ya ƙi yarda a tsawon lokaci makwabtansa su yi masa wanka.
Sai dai kafafen yaɗa labaru sun ce a watannin da suka wuce ne ya bayar da kai bori ya hau inda ya amince ya yi wanka da sabulu.
A cewar kamfanin dillancin labaru na IRNA a Iran, Haji ya yi gajeruwar rashin lafiya kafin rasuwarsa a ranar Lahadi.
A wata hira da jaridar Tehran Times a shekarar 2014, ya bayyana cewa yana kwana a cikin wani ɗan karamin gida da mutane suka gina masa a kauyensu da ke Dejgah.
Ya faɗa wa jaridar cewa ya fuskanci koma-baya sosai a lokacin da yake yaro.
Yana rayuwa ne ta hanyar cin ruɓaɓɓen nama da abincin da aka zubar a bola.
Amou Haji ya kasance mutum mai yawan shan sigari.










