Ronaldo zai maye gurbin Griezmann a Atletico, Bayern ta tuntubi Harry Kane

Atletico Madrid ta kara kaimin raba Cristiano Ronaldo - dan wasan gaba mai shekara 37 da Manchester United - ta hanyar sanya Antoine Griezmann a kasuwa. (Times - subscription required)

United za ta kyale Ronaldo ya bar kungiyar amma a matsayin dan wasa na aro na shekara guda idan ya bukaci haka, amma dole ya koma Old Trafford bayan kakar wasan guda ta wuce. (Mirror)

Barcelona na fatan riga Chelsea sayo Jules Kounde, bayan da kungiyar ta Stamford Bridge din ta yi tayin sayo shi kan yuro miliyan 65, wanda za ta biya sannu a hankali, inda Barca ke son biyan kudin lokaci guda. (Sport - in Spanish)

Chelsea za ta koma ga neman Presnel Kimpembe mai shekara 26 idan Barcelona ta riga ta saye Kounde. (Express)

Bayern Munich ta tuntubi wakilan Harry Kane, dan wasan gaba na Tottenham da Ingila mai shekara 28, wanda bai cire ran komawa Jamus a sabuwar kakar wasa mai zuwa ba. (Bild - in German)

Dan wasan Brazil Neymar ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai bar Paris St. Germain a wannan kakar wasan mai shigowa, inda ake cewa wai Chelsea da Manchester City sun bayyana sha'awar raba dan wasan mai shekara 30 da Faransa. (Mail)

Manchester United na da karfin gwuiwar sayo Denzel Dumfries, dan wasan baya na Inter Milan da Netherlands mai shekara 26. (Calciomercato - in Italian)

Chelsea ta kulla yarjejeniya da za ta ba ta damar rike Romelu Lukaku, dan wasan gaba mai shgekara 29 na karin shekara guda bayan ya kammala buga wasa na kaka guda a matsayin dan aro a gasar Serie A ta Italiya. (Mail)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce babu sauran wani dan wasa da zai sayo a bana sai idan wani dan wasa ya sami rauni ko idan kungiyar ta sayar da wani dan wasanta. (Sky Sports)

Brighton ta ki amincewa ta rage farashin da ta sanya wa Marc Cucurella, dan wasan baya dan Sfaniya, kan fam miliyan 50. Ta kira tayin fam miliyan 30 da Manchester City ta yi "abin dariya". (Athletic - subscription required)

Kungiyar Brighton, wadda masoyanta ke kira Seagulls za su nemi sayo Brandon Williams, dan wasan baya mai shekara 21 idan Cucurella ya koma wata kungiyar a bana. (Mirror)