Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta sayi Zinchenko daga Man City
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta kammala cinikin ɗan wasan tsakiya na ƙasar Ukraine, Oleksandr Zinchenko, daga Manchester City.
Zinchenko wanda ya buga wasanni da dama a ɓangaren hagu na bayan Man City, wasa 15 kawai ya buga a kakar wasan da ta gabata a yunƙurin ƙungiyar na kare kambin Premier League da ta ɗauka.
Ɗan ƙwallon mai shekara 25 ya je Arsenal ne daga zagayen da City ke yi a Amurka don kammala komawarsa tasa bayan Arsenal ta amince da yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 30.
Zinchenko ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo kuma shi ne ɗan wasa na biyar da Arsenal ta saya kafin fara sabuwar kakar wasa.
"Wannan mafarkina ne da nake yi tun ina yaro ya zama gaskiya, saboda babban masoyin Arsenal ne ni lokacin da ina yaro," in ji Zinchenko.
Shi ne ɗan wasa na biyu da yake komawa Arsenal daga City a bazarar nan.
Tuni Gabriel Jesus ya koma Emirates kan fan miliyan 45, inda har ma ya ci mata ƙwallo wasan sada zumunta.