Kulob ko ƙasa? Tsaka mai wuya kan Gasar cin Kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da manyan ƙungiyoyin tamaula ke shirye-shiryen sakin fitattun 'yan wasansu domin fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2023, wato Afcon. Shin har yanzu ana bai wa ƙungiya ko ƙasa fifiko?
Fitattun 'yan wasa irinsu Mohamed Salah, da Victor Osimhen da Achraf Hakimi, za su je gasar da ƙasar Ivory Coast za ta karɓi bakunci da za a yaye labulen fara wasan ranar 13 ga watan Junairu a kuma kare ranar 11 ga watan Fabrairun 2024.
Duk da lokacin ana cikin yanayin sanyi a wasu ƙasashen Turai, lokacin hutu ne ga 'yan wasa kuma ƙungiyoyi, inda za su ɗauki makonni kafin ganin wasu 'yan wasa musamman a farkon kakar.
Sashen wasannin Afirka na BBC, ya yi duba kan tasirin da gasar cin kofin nahiyar Afirka zai yi wa 'yan wasa, manajoji, da ƙungiyoyin tamaula da kuma magoya bayansu.
Shin ƴan wasa za su shiga tsaka mai wuya?
Ɗan wasan tsakiya na Brentford Frank Onyeka na shirin bugawa ƙasarsa Najeriya wasa karo na biyu a gasar ta Afcon, dama dai ya halarci wasan da aka yi a jamhuriyar Kamaru a farkon shekarar 2022.
"A kodayaushe ina son wakiltar ƙasata a babban wasa irin wannan. Abin alfahari ne sanya rigar kwallo mai launin kore da fari, don haka abu ne da ya kamata na yi," inji ɗan wasan a hirarsa da BBC.
"Idan an yi waiwaye, karamin yaro ne ni da ke buga tamaula a titunan Najeriya, amma a yanzu zan wakilci ƙasata karkashin ƙungiyar Super Eagles.
"Mafarkina ne ya tabbata, saboda abin da na ke ayyanawa kenan a shekarun baya idan ina kallon zakakuran 'yan wasa, amma sai ga shi a yau na samu wannan damar. Na kosa lokacin ya zo."
Onyeka dai na buga wasa a ƙungiyar Brentford, tare da 'yan wasan Afirka irinsu Bryan Mbeumo (Kamaru) da Yoane Wissa (Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo).
Ɗan wasan gaba Mbeumo ba zai halarci Afcon ba saboda raunin da ya ji, kuma za a yi kewar dukkan 'yan wasan uku a Premier League a wata mai zuwa.
Onyeka ya ce su ukun sun tattauna kan yadda wasan zai gudana.
"Ba lamari ne mai sauki ba. Amma na san tawagarmu, suna da kwarewa," in ji matashin ɗan wasan mai shekara 25.
"Duk lokacin da wani ba ya nan, to akwai wanda zai karɓe shi domin cike wannan giɓin."

Asalin hoton, Getty Images
A baya kocin ƙungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya soki matakin sanya lokacin gasar a tsakiyar kaka, amma kocinsu Onyeka Thomas Frank yana ba su kwarin gwiwa.
"Ya taya ni farin cikin cewa zan wakilci ƙasata. Na yi matukar farin ciki ganin yadda yake ba ni kwarin gwiwa, da bai wa 'yan wasa damar halartar gasar Afcon," in ji shi.
Sai dai sake komawa wasan Premiere League bai zo wa Onyeka da daɗi ba a wancan lokacin, inda aka fitar da Najeriya a mataki na 16.
"Idan ka dawo buga wasa, tuni abokanka sun yi nisa, sake shiga cikinsu da ci gaban wasan kan ɗauki makonni kafin ka saba.''
"Ya kamata ɗan wasa ya zama jajirtacce, saboda fita daga tawagar da kuke wasa a kodayaushe, na makonni da sake dawowa na da matukar wuya."
Yaushe za a fara gasar Afcon?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 2017, masu ruwa da tsaki a tamaula sun sauya lokacin gudanar da wasan na al'ada daga watan Janairu da Fabrairu, zuwa watan Yuni da Yuli, saboda Masar ce ta karɓi bakuncin gasar a shekarar 2019, kuma a karon farko lokacin zafi a Turai.
Amma duk da hakan dole kanwar na ki a shekarar 2021, an ɗage wasannin karshe zuwa ainihin watannin da aka saba yi, domin kaucewa yanayin ƙasar Kamaru da ta karɓi bakunci, sai kuma annobar cutar Korona da aka yi fama da ita.
A shekarar 1994 Jay-Jay Okocha, ya lashe wa Najeriya kofin Afcon. Ya ce lokacin da ake sanyawa na gasar ka iya tasiri kan 'yan wasa.
"Suna sanya 'yan wasan Afirka cikin tsaka mai wuya, kan dole su rin ga wasan a watan Janairu ko farkon kakar wasanni," in ji Okocha a hira da BBC.
"Idan za su iya matsar da lokacin gasar cin kofin duniya zuwa watan Disamba saboda ƙasashen da za su halarta su samu nutsuwa, me zai hana a yi hakan ga Afcon, a kuma yi aiki tare yadda babu wanda zai cutu?
"Na san kociyoyin da suka ki rattaɓa hannu kan amince da ɗaukar 'yan wasan Afirka saboda gasar Afcon, amma za su ɗauki 'yan Brazil waɗanda za su shiga gasar Copa Amerika a lokacin bazara. Wannan bai dace ba."
Magoya baya

Asalin hoton, Issahaku Abdul-Mumen
Kamar sauran tawagogi, ita ma Ghana tana da 'yan wasan da za su shiga gasar ta Afcon 2023, kuma akwai waɗanda suke buga wasa a manyan kulob na ƙasashen Turai.
Ɗan wasan tsakiya na Arsenal Thomas Partey, da na West Ham Mohammed Kudus da ɗan wasan gaba na Crystal Palace Jordan Ayew, na cikin 'yan wasan da za su bar ƙungiyoyinsu na Premier League domin tafiya Ivory Coast.
Shugaban magoya bayan West Ham a Ghana, Issahaku Abdul-Mumen, ya ji ba daɗi, wani ɓangare yana farin ciki wani kuma bai ji daɗi ba, saboda dole Kudus ya bar Landan a tsakiyar kakar wasa domin zuwa Afcon.
"Idan babu Kudus a tawagar Ghana, ba inda za ta je. To amma Kudus na buga wasa mai kyau a West Ham," inji Abdul a hirarsa da sashen wasanni na BBC daga Ghana.
"Shigar Kudus ƙungiyar West Ham na ɗaya daga cikin abubuwan farin ciki gare ni. Yana ɗaya daga cikin kwararrun 'yan wasan Afirka.
"Ina daga cikin 'yan gani kashe-nin Afcon - kawai ka kira ni Afcon. Ni ɗan Afirka ne, wannan kuma gasarmu ce. Kuma iyaye da kakannin mu ne suka samar da ita.
"Amma a ce Kudus zai bar [West Ham] wannan lokaci ne da zan yi matukar bakin ciki, ba gare ni ba har da magoya baya. Amma haka za mu yi hakuri, za mu daure.
"Abin yana da ciwo, gare ni da sauran masoyan West Ham, amma ina matukar farin ciki a matsayina na ɗan Ghana."
Abin da ke gaban manajojin kulob-kulob

Asalin hoton, Getty Images
Ba wai masoya West Ham ne kaɗai suka shiga damuwa saboda fargabar abin da ka je ya zo idan Kudus ya tafi Afcon ba.
Kocin West Ham David Moyes, ya bayyana karara zai yi kewar ɗan wasan gaban mai shekara 23, wanda ke burge shi saboda irin salon kwallonsa.
"Wato yaro ne zakakuri da ake jin daɗin aiki da shi, kuma yadda yake zura kwallo a raga da taimakawa 'yan wasa a cikin fili abin a yaba ne," in ji Moyes.
"Abin takaici ne da kuma sanyaya gwiwa idan ya tafi, saboda irin salon yadda ya ke zura kwallo a raga daban ne. Dole mu nemi wata hanyar."
Sai dai tsohon kociyan Kudus a Black Stars, Chris Hughton, ya yi amanna cewa an daina abin nan da ake yi a baya da ɗan wasa ke shiga tsaka mai wuya kan zaɓar ƙasarsa ko ƙungiyarsa.
Ya ce kociyoyi a ƙasashen Turai sun sauya salo ta yadda suke shiryawa tsaf a duk lokacin da 'yan wasansu za su halarci wani wasa, kuma Afcon ba ita ce dalilin da yasa ake kaucewa ɗaukar fitattun 'yan kwallo daga Afirka ba.
"Yawancin ƙungiyoyi da kociyoyi sun amince duk ɗan wasan Afirka da suka ɗauka da zarar lokacin Afcon ya yi, za su koma gida domin wakiltar ƙasashensu," ji mai shekara 65 ɗin.
"Don haka yanzu an daina wannan ya yin na zaɓar ƙasa ko kulob, an bar wannan tuntuni. Ina ganin ƙungiyoyi sun waye, suna ɗaukar matakai yadda ya dace da amincewa da abin da ya zo a lokacin."
Ana sa ran gasar sauya lokacin buga gasar kofin nahiyar Africa ta 2025 da ƙasar Morocco za ta karɓi bakunci, kamar yadda aka tsara na watanYuni zuwa Yuli.
Sai dai hakan zai zo daidai lokacin da Fifa za ta ƙara faɗaɗa ƙungiyoyin da za su je gasar kofin duniya zuwa 32.
Koma yaya ta kasance, tabbas za a yi ja-in-ja tsakanin manyan ƙungiyoyin Turai da manyan 'yan wasa nan da watanni 18 masu zuwa.











