Wadanne 'yan wasa ne za su yi fice a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023?

Asalin hoton, BBC Sport
- Marubuci, Rob Stevens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
Za a fara gasar Cin Kofin Afirka karo na 34, wadda za a take 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu a Ivory Coast.
Kungiyoyin Premier League da dama za su rasa 'yan wasan da za su je buga gasar, ciki har da Mohamed Salah da ke fatan kawo karshen shekara 14 rabonda Masar ta dauki kofin.
Sashen BBC Sports Afirka ya yi bitar 'yan wasa shida, wadanda suke ganin suna da dalilin ya kamata kasarsu ta lashe kofin nahiyar Afirka a 2024.
Mohamed Salah (Masar)
Masar ta yi rashin nasarar lashe kofin a hannun Senegal a 2022 a Kamaru, sannan Teranga Lions ta hana ta zuwa gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Dukkan wasannin a bugun fenariti Senegal ta yi nasara - kuma Salah bai buga fenaritin ba a Afcon, wanda shi ne na karshen bugawa, kuma kafin nan Senegal ta lashe kofin.
Kofin Afcon na bakwai da Masar ta dauka shi ne a 2010, kuma Salah na fatan taka rawar gani fiye da wadda ya yi a Gabon a 2017 da kuma a Kamru a 2022.
Salah ya dauki kofuna da yawa a Liverpool, sai dai mai shekara 31 zai so ya kara cin kwallo bayan shidan da ya zura a raga daga Afcon ukun da ya halarta.
Kamar yadda yake taka rawar gani a Anfield a bana, Salah ne zai ja ragamar kasar a fafatawa da Ghana da Cape Verde da Mozambique a rukuni na biyu.
Victor Osimhen (Nigeria)

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan da bai je gasar da aka yi a 2021 sakamakon bullar cutar korona da raunin da ya ji ba, ko wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na bana zai ja ragamar Super Eagles ta lashe kofin na 2024?
Mai shekara 24 ya zama daya daga fitattun masu cin kwallaye a Turai, wanda ya zama kan gaba a cin kwallaye a SerieA, kuma hakan ya sa Napoli ta lashe kofin a karon farko tun bayan 1990.
Jinya da Osimhen ya yi ya sa Super Eagles ta yi canjaras da Lesotho da kuma Zimbabwe a wasan shiga gasar Kofin Duniya da za a yi a 2026.
Tsohon dan wasan Lille din yana cikin tawagar Super Eagles a Afcon 2019, amma daga baya aka saka shi a wasan da kasar ta zama ta uku a wasannin.
Najeriya tana ruknin da ya hada da mai masaukin baki Ivory Coast da Equatorial Guinea da Guinea-Bissau a rukunin farko.
Ana ta rade-radin cewar Osimhen zai koma taka leda a gasar Premier League, amma wannan gasar dama ce a gare shi ya kara nuna kwazon da yake da shi a fannin zura kwallaye a raga.
Serhou Guirassy (Guinea)
Dan wasan na taka rawar gani a Stuttgard, wanda ya ci kwallo 15 a wasa 10 a gasar Bundesliga.
Mai shekara 27, tsohon matashin tawagar Faransa zai buga Afcon a karon farko, bayan da ya fara yi wa Guine wasa a Maris din 2022.
Rukuni na uku za a yi wasannin hamayya da ya kunshi mai rike da kofin Senegal da Kamaru, inda Syli National ke ciki da The Gambia, wadda karo na biyu ke nan da za ta kara a wasannin.
Raunin da ya ji a watan Nuwamba ya kawo masa tsaiko, amma dai Guinea na fatan Guirassy zai sa kwazon da zai kai kasar zagaye na biyu, inda daga nan komai zai iya faruwa.
Mohammed Kudus (Ghana)

Asalin hoton, Reuters
Ghana za ta ziyarci makwabciyarta Ivory Coast da fatan ba za ta maimaita abin kunya da ta yi a Kamaru ba, inda aka fitar da ita a wasannin rukuni - har da wanda Comoros ta doke ta 3-2.
Ghana tana tangal-tangal a wasa biyu da ta buga a neman shiga gasar Kofin Duniya da za a yi a 2026, wadda ta kara rashin nasara a hannun Comoros.
Kudus ne kan gaba a cin kwallaye da kasar ta samu gurbin zuwa Ivory Coast mai uku a raga, kuma yana taimaka wa West Ham United a wasan da take bugawa tun bayan da ya koma kungiyar da ke buga Premier League a cikin watan Agusta.
Bayan da ya ci kwallo biyu a Kofin Duniya a Qatar a 2022, ko dan wasan mai shekara 23 zai ja ragamar kasar ta taka rawar gani a Ivory Coast?
Issa Kabore (Burkina Faso)
Mai tsaron baya daga gefe, shi ne aka zaba a matashin dan wasa a 2021, bayan da Burkina Faso ta kai ta daf da karshe, wadda daga baya ta yi rashin nasara a hannun Senegal.
Kabore yana cikin 'yan wasan Manchester City tun bayan da ya koma kungiyar daga Mechelen ta Belgium a 2020, amma har yanzu bai fara yi wa mai rike da kofin Premier da FA Cup da Champions League a bara ba.
Bayan da ya je wasannin aro a Troyes da Marseille, mai shekara 22 na taka leda a Luton Town, wadda ba ta yin abin kirki a wasannin bana.
Yayin da Burkina Faso za ta fuskanci Algeria da Mauritania da kuma Angola a rukuni na hudu, Kabore - wanda tuni ya buga wa tawagar wasa sama da 30 - ya samu damar da zai nuna kansa - hakan zai sa Pep Guardiola ya kira shi cikin 'yan wasan Manchester City 11 daga kakar badi da zarar ya nuna kansa.
Azzedine Ounahi (Morocco)
Rawar da dan wasan ya taka a gasar Kofin Duniya a Qatar a 2022 a tawagar Morocco da ta kafa tarihin kaiwa daf da karshe ta farko a Afirka - hakan ya sa Marseille ta dauki Ounahi.
Sai dai ya sha jinya tun raunin da ya ji a lokacin da yake buga wa tawagar Morocco wasa a watan Maris, bayan wasa bakwai da ya buga wa sabuwar kungiyarsa.
Mai shekara 23 na aiki tukuru don ya taka rawar gani a Afcon, koma ya yi fiye da kwazon da ya saka a gasar Kofin Duniya - sai dai dan wasan bai yi wa Morocco karawa biyu a neman shiga Kofin Duniya ba da ta yi a cikin Nuwamba.
Koci,Walid Regragui zai so yin amfani da dan wasan da ya bayar da gudunmuwar da suka kai daf da karshe a kofin duniya, yayin da Morocco ke rukuni na shida da ya hada da Jamhurirae Congo da Zambia da kuma Tanzania.











