Dangantakar 'yan Tutsin Congo da Rwanda ta ja musu ƙyama da wariya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
'Yan tawayen M23, suna ta'annati a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inda suka mamaye manyan birane 2 a yankin bayan mummunar gwabzawar da suka yi abin da ya tursasawa dubban mutane barin muhallansu.
Daya daga cikin gangamin da suke ko yakin da suke shi ne kan batun gallazawa 'yan kabilar Tutsi da ke Congo.
Bin diddigin asalin 'yan Tutsi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kuma yadda hakan ya taso da rikicin da 'yan tawayen na M23 ke yi, abu ne mai wuya da kuma sarkakkiya sannan kuma dole sai an yi taka tsan-tsan wajen bin diddigin.
Ga wadanda ba su sani ba, hukumomi da yawa na duniya na cewa a yakin da suke na cewa ana nuna musu wariya, su kansu 'yan tawaye M23 din sun tafka ta'asa.
Kamar misali Amurka da Majalisar Dinkin Duniya, sun zargi shugabannin kungiyar 'yan tawayen na M23, da aikata laifukan yaki kamar cin zarafi ta hanyar lalata da kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba.
Abu na biyu kuma, wasu masu sharhi su ce a maimakon 'yan tawayen su kare 'yan Tutsi, sai Rwanda da ke goyon bayan 'yan tawayen da su kansu 'yan tawayen ke neman daidaita gabashin Congo wanda ke da arzikin albarkatun kasa.
Ya kamata mutane su sani akwai dubban 'yan tutsi a Congo wanda kuma yawancinsu basa goyon bayan abin da ake aikatawa da sunansu.
Kwararru da kuma kungiyoyi da dama kamar Majalisar Dinkin Duniya sun tattara bayanan da dama da ke nuna irin yadda ake nuna wa 'yan titsin wariya su da 'yan kabilar Banyamulenge wanda suka fi zama a kudancin larfin Kivu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana nuna musu wariya kama a wajen aiki da maganganun batancin da ake a kansu da kuma kashe su da ake yi.
Tun daga tushe wariyar, shi ne kungiyar'yan tsutsin da ke makwabtaka da Rwanda wadda suka kafata tun a 1994.A lokacin shekarun 1990 da farkon karni na 2000s, yawancin 'yan tutsin Congo sun taimakawa 'yan tawayen Congo da Rwanda ke marawa baya wajen yakar gwamnatin Congo a ta wancan lokacin.
Bukuru Muhizi, wani mai bincike kuma masanin tattalin arziki daga kudancin yankin Mwenga da ke Kivu, ya shaida wa BBC cewa, an kashe mutane da dama daga cikin iyalansa saboda kawai su 'yan kabilar Banyamulenge da Tutsi ne.
Ya ce, a shekaru shida da suka wuce, sojojin Congo sun kashe kakan kakansa da jikansa.To amma kuma sojojin Congon ba su ce komai ba a kan wannan zargi.
Mr Muhizi, ya ce a yanzu iyalansa na zaune a cikin Jamhuriyar Dimkradiyyar Congo, sannan kuma yana fatan duniya zata sani cewa al'ummominsu na fama da abin da ya kira kisan kiyashi a asirce.

Asalin hoton, Bukuru Muhizi
Kafin lokacin mulkin mallaka, wasu daga cikin yankunan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo suna karkashin sarautar gargajiya ne ta Rwanda wadda ke karkashin 'yan Tsutsi.
Sun jima suna yaki da masu mamaya inda suke yaki domin ganin sun mallaki karin yankuna a yankin Gabashin Afirka.
'Yan kabilar Tutsi da Hutu da sauran kabilu sun jima a cikin masarautar Rwanda,to amma bayan mulkin turawan mulkin mallaka an rana iyakoki sai aka raba masarautar tsakanin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kuma Rwanda.
Daga bisani sai wasu 'yan Tutsin suka yi kaura zuwa Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
A tsakiyar karni na 20 turawan mulkin mallaka na Belgium suka kawo ma'aikata daga Rwanda a yanzu domin su yi musu shuka, yayin da wasu kuma suka zo yankin don kashin kansu.
A bangare guda kuma, 'yan gudun hijira 'yan kabilar Tutsi sun isa Congo, inda suka gujewa rikicin kabilancin da ake a Rwanda da kuma Burundi.
Dukkan kasashen 'yan kabilar Tustis ne suka mamaye su abin da ya janyi rikici na 'yan Hutu.
Ana tunanin cewa da yawa daga cikinsu sun isa Congo ne a 1994 lokacin da aka yi kisan kiyashin a Rwanda inda a lokacin aka kashe 'yan tustin dubu 800.
A yayin da 'yan kabilar Tutsi da Banyamulenge na Congo ke kara girma, sai mahukunta a Congon suka mayar da su kasa inda aka mayar da su ba komai ba a kasar.
A farkon shekarun 1970, a lokacin mulkin shugaba Mobutu Sese Seko,sai ya bawa duk wanda ya zo daga Rwanda da Burundi damar kasancewa 'yan kasa.
To amma a 1981, sai majalisar dokokin kasar ta soke wanann dama inda yawancin 'yan tutsin da Banyamulenge suka kasnace ba su da tsuntsu basu da tarko wato ba su da cikakkiyar kasar da za su bugi kirji su ce tasu ce.
A yanzu dai kundin tsarin mulkin kasar ya dauki 'yan kabilar Tutsi da Banyamulenge a matsayin 'yan Congo inda kuma kawai manyan sojojin kasar daga suka fito daga wadannan kabilu.

Asalin hoton, AFP
To amma duk da haka akwai alamun da ke nuna har yanzu ana nuna musu wariyar launin fata.
A 2024, kwararrun da ke aiki a Majalisar Dinkin Duniya, sun ce a kudancin Kivu, ana daukar 'yan kabilar Banyamulenge a matsayin mugaye wadanda za su iya cutar da makwabtansu.
Akwai kuma wasu rahotanni a baya bayannan da aka fitar da suka ce an kashe sojojin Congo da suka fito daga kabilar Tutsi da Banyamulenge.
Kodayake akwai wasu 'yan tutsi 'yan Congo da ke goyon bayan 'yan tawayen M23 a kan fadan da suke a yanzu, yawancin a cewar Mr Strearns, ba sa jin dadi sannan kuma suna hangen abin da zai iya biyo baya.











