Ko kun san amfanin gulma?

Hoton alamun gulma da baki.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, "Why Do We Do That?" program
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Radio 4
  • Lokacin karatu: Minti 5

Gulma ka iya ɓata maka suna. Za ta iya bayyana halayyarka. Aba ce mai daɗi a wajen wasu. Amma kuma a wajen wasu mutanen da dama, ɗabi'a ce maras kyau - ko ma a ce laifi ce.

Gulma wata ɗabi'a ce da masana halayyar ɗan'Adam suka lura cewa al'ummomi da dama suna yint, kama daga yankuna na karkara da birane da ma ƙauyukan ƙayau.

"Kusan kowa na yin gulma idan har damar yinta ta samu,'' in ji Dr Nicole Hagen Hess, masaniyar halayyar ɗan'Adam da ke Jami'ar Jihar Washington a Amurka.

Idan aka yi maganar gulma abin da zai zo mana a rai shi ne, maganar wani a bayansa da nufin ɓata shi. Ko kuma a ce cin naman wani kamar yadda ake kira a wata al'adar.

To amma kuma Dr Hess ta faɗaɗa ma'anarta, inda ta ce gulma musayar bayanai ne da suka danganci halayyar wani mutum.

Wannan zai iya kasancewa abin da dangi ko abokanai ko abokan aiki ko ma abokan hamayya ko gaba ke faɗa a kanmu.

Haka kuma gulma za ta iya kasancewa wani abu da aka faɗa a labarai ko ma sakamakon gasar wasanni a cewar masaniyar.

Dr Hess ta ce ba wai sai wanda ake magana a kanshi ba ya wajen ba ne za a kira zance gulma - mutumin da ake maganarsa zai ma iya kasancewa a gabanku.

''Idan har kana magana a kan mutumin, ko wata tufa ko wani abu da ya sanya a jikinsa, ko abin da ya yi, duka zan iya kiran wannan gulma,'' in ji ta.

To amma me ya sa mutane suke wannan ɗabi'a ta gulma tun asali, wannan ita ce tambayar da har a yau ɗin nan masu bincike da nazari ke neman sani.

Ga wasu daga cikin nazariyyar da masana ke ganin mutane ke yin gulma.

Shaƙuwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Robin Dunbar masani a kan halayyar ɗan'Adam shi ne ya bayyana cewa gulma na iya taka rawa mai amfani a cikin al'umma - kuma ya yi ta jaddada hakan.

A bisa nazarinsa a tsakanin halittu irin su ɗan'Adam na zamanin da mai gashi buzu-busu a jikinsa da birai da dangoginsu na zamanin da, irin susar nan da suke yi wa juna ko cire ƙwari a jiki da suke yi ɗabi'a ce ta nuna 'yan'uwantaka da zaman tare.

Bayan ƙulla alaƙa ta ƙut-da-ƙut, ɗabi'a ce da kuma ke zaman wata hanya ta sasantawa bayan an yi faɗa ko an samu saɓani, da kwantar da hankali bayan zaman tankiya.

Sannan kuma hakan na zama wata hanya ta ajiye kowa a matsayinsa a cikin al'umma.

Babba ya san matsayinsa shi ma yaro ya san matsayinsa a cikin iyali ko al'umma.

To amma saboda su mutane ba su da gashi irin na dabbobi buzu-buzu, zaman gaɗa da gulma na iya kasancewa irin waccan halayyar da aka san birai da ita.

Kuma hakan na zama da amfani kamar yadda ita waccan halayya ta birai take, wajen sasantawa bayan faɗa da kwantar da hankali da ƙulla alaƙa da abokantaka da kuma nuna wa kowa matsayinsa a cikin al'umma - babba ya san matsayinsa yaro ma ya san matsayinsa.

Bugu da ƙari gaɗa ko gulma na zama wata hanya ta musayar bayanai, misali wa ya kamata ka amincewa, waye bai kamata ka yarda da shi ba.

Ga fahimtar Farfesa Dunbar, hatta shi kansa yare ko harshe ya samu ne ta wani ɓangare domin a samu hanyar da za a iya yin gulma.

wasu maza biyu na magana a ofis yayin da wasu mata biyu ke kallon kwamfutarsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Idan aka yi maganar gulma yawanci muna tunanin yin maganar wani mutum ne a bayan idonsa da nufin ɓatanci

Wani bincike da aka yi a Jami'ar Dartmouth ta Amurka a 2021, ya nuna cewa mutanen da ke gulma tare ba wai kawai suna tasiri a ra'ayin juna ba kaɗai, alaƙa na ƙulluwa sosai a tsakaninsu a dalilin hakan.

Masu binciken sun kuma gano cewa gulma na taimakawa wajen wanzar da haɗinkai da abokantaka ta ƙut-da-ƙut a tsakanin masu yinta.

Lokacin da aka tilasta wa mutane zaman gida a lokacin annobar Korona - sai sha'awar mutane ta ƙaru a kan son jin labarai.

"Daga lokacin ne na san cewa ashe an tauye mana damar samun labarai," in ji ɗaya daga cikin masu binciken.

"Da dama daga cikin rayuwarmu da kuma yadda muke kallon duniya- muna sanin hakan ne daga labaran da muke gaya wa wasu - kuma gulma ita ce wannan labari.

Muna bai wa juna labaran kanmu, to kuma hakan na da haɗari, amma kuma akwai alfanu da dama a kan hakan," in ji ta.

Wasu matasan mata uku na kallon wani abu da ya burge su a waya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bincike ya nuna cewa mutanen da ke gulma a tsakaninsu suna zama abokan juna sosai

Dabarun ci gaba da rayuwa

Bayan tsawon lokaci na miliyoyin shekaru mutane sun koyi dabaru na hanyoyin da ya kamata su bi domin kare kansu da kuma waɗanda ke tare da su daga duk wani abu da zai cutar da su.

Ga wasu matan gulma wata muhimmiyar hanya ce da rayuwa ko kare kai daga wata hanya ta cutarwa - misali wata alaƙa da namiji wadda za ta iya cutuwa a sanadiyyarta.

"Mata sun fi cutuwa sosai idan ana maganar faɗa tsakaninsu da namiji. Saboda haka ta hanyar gulma mata za su iya yaɗa bayani ko ankarar da junansu game da wata illa da ta danganci alaƙa da maza," in ji Dr Nicole Hagen Hess.

Rayuwa da kuma matsayinmu a cikin al'umma abubuwa ne da suka dogara sosai a kan halayyarmu.

Idan mutum ya kasance mai mummunar ɗabi'a ne ko kuma wanda sunansa ya riga ya ɓaci, wannan na iya yi masa illa sosai a cikin al'umma, in ji Dr Hess.

Wannan zai iya illa ga matsayinka a cikin al'umma, da taƙaita damarka ta tattalin arziƙi, hatta ma damarka ta samun wasu abubuwa kamar abinci za ta iya taaita.

''Saboda haka idan har ya kasance mutane na yin gulmarka, hakan zai iya yi maka illa sosai,'' in ji masaniyar.

Dr Hess na ganin baya ga wasu abubuwan, gulma wata hanya ce da za ta iya shafar matsayin mutum a cikin al'umma -a ta ɗaga shi ko kuma ta sa matsayinsa ya yi baya ko mutuncinsa ya zube.

''Bisa ɗabi'a mutane na gasa ko hamayya a tsakaninsu -kowa na son ya fi wani, saboda haka rikici abu ne da ba za mu iya rabuwa da shi ba,'' in ji Hess.

Wasu matasan mata biyu na zaune a tebur suna gulma da dariya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Walau saboda jin daɗi ko tsira da rayuwa ko ƙulla alaka, gulma ta zama wata ɗabi'a a rayuwarmu ta yau da kullum

Nishaɗi

A wajen wasu mutanen da yawa gulma ba wata aba ce mai illa ba ko maras kyau ba - illa raha ce kawai

"Wannan ita ce irin gulmar da na ƙware a kai," in ji McKinney, mai yaɗa bayanai ta shafukan sada zumunta da muhawara.

Sha'awarta da gulma - da kuma sha'awarta da bayar da labari - duka sun samu ne kasancewar ta taso ne a gidan da ake addini sosai, inda aka koyar da ita cewa gulma laifi ne mai janyo zunubi.

"Gulma wata aba ce da za ka ji kana zakwaɗin yi da wani," in ji ta.

Tana dariya ta ce : Idan aka ce yau ba gulma? "Kaico! Ai ji za ka yi duniyar ma ta gundire ka."

Walau saboda nishaɗi ko tsira da rayuwa ko neman ƙulla alaƙa, gulma ta zama wani ɓangare na rayuwarmu ta yau da kullum – ta zama wata ɗabi'a ta ɗan'Adam da ba zai iya rabuwa da ita ba, in ji Dr Hess.