Yadda za a gwada ƙwanji a zaɓukan cike gurbi a Kano da Kaduna

Jagororin ƴan siyasar Kaduna da Kano
Lokacin karatu: Minti 4

A yau Asabar ne za a gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu mazaɓu guda 16 a sassa daban-daban a faɗin Najeriya, inda aka samu wasu kujeru da ko dai suka ajiye suka koma wata kujerar, ko kuma waɗanda suka rasu.

Sai dai zaɓen a jihohin Kano da Kaduna suna matuƙar ɗaukar hankali, musamman a arewacin Najeriya, inda ake ganin tamkar wani sabon gwagwarmayar siyasa ce za a sake yi domin nuna ƙwanji tsakanin wasu jigajigan ƴansiyasa masu ƙarfin faɗa a jihohin biyu.

A Kano, akwai siyasa da tsama mai zafi a tsakanin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yanzu za a iya cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gada. Haka kuma yanzu akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda shi ma yake da ƙarfin faɗa a siyasar jihar.

A jihar Kaduna kuma, gwagwarmayar nuna ƙarfin iko ne tsakanin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da gwamnan jihar mai ci, Uba Sani wanda ya gaje El-Rufai, inda tun bayan ɗarewa karagar mulkinsa aka fara ganin ɓaraka a tsakaninsu, duk da cewa a baya akobai ne na kusa.

Waɗannan manyan ƴansiyasar da adawar da ke tsakaninsu ne ya sa ake ganin zaɓukan cike gurbin jihohinsu za su fi ɗaukar hankali, musamman ganin yadda tuni lamura suka fara ɗaukar zafi a wuraren yaƙin neman zaɓe.

Jihar Kano

A Kano dai za a fafata zaɓen a kujerun mazaɓar Bagwai da Shanono da Ghari da Tsanyawa duka a majalisar jihar.

A jihar, asali dai da Ganduje da Gwamna Abba duk sun kasance a tsarin siyasa ɗaya ta Kwankwasiyya, lokacin da Ganduje yake mataimakin gwamna, shi kuma Abba yake kwamishinan ayyuka.

Shi ma Sanata Barau ya taɓa zama a tsarin na Kwankwasiyya, inda dukansu suka kasance a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan Ganduje ya maye gurbin Kwankwaso ne a matsayin gwamna, sai rikici da saɓani ya ɓarke a tsakanin su, inda Ganduje ya ja wasu jigajigan tafiyar, wasu kuma suka tsaya tare da Kwankwaso.

A zaɓen shekarar 2019, wanda shi ne karo na farko bayan rabuwar Ganduje da Kwankwaso, inda Kwankwason ya fice daga APC ya koma PDP, ya tsayar da Abba a matsayin ɗantakara, shi kuma Ganduje ya tsaya domin neman sake komawa wa'adi na biyu.

Zaɓen ya yi zafi sosai, inda a zagaye na farko aka gama ba tare da sanin cikakken wanda ya samu nasarar zaɓen ba, sai aka yi 'inconclusive' kafin Ganduje ya samu nasara.

Amma a zaɓen shekarar 2023, bayan Kwankwaso ya fice daga PDP, ya koma jam'iyyar NNPP, sai ya sake tsayar da Abba, shi kuma Ganduje ya tsayar da mataimakinsa, Yusuf Ganuwa, inda suka fafata, amma Abba ya doke shi.

Wannan ya sa tsamar da ƙara faɗaɗa, inda magoya bayan APC da NNPP suka sa zare, suna tafka muhawara a siyasar jihar.

Shi ma Sanata Barau ya ƙara samun tagomashi ne bayan ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, inda har ake tunanin akwai ɗan takun-saƙa tsakanin zaginsa na APC da tsagin Ganduje, duk da cewa suna nanata cewa babu wata matsala a tsakaninsu.

Sai dai ana ganin yanzu fafatawa ce tsakanin APC, da jagororinsu wato Ganduje da Sanata Barau, da NNPP da jagororinsu Kwankwaso da Abba a gefe guda, inda kowane ɓangare ke son nuna ƙarfin iko.

Jihar Kaduna

A Kaduna kuma za a yi zaɓen majalisar jihar a mazaɓar Basawa, bayan tsohon ɗanmajalisar Jamil Albani ya zama shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari, sai kuma na cike gurbin majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Chikun da Kajuru bayan Ekene Abubakar ya rasu.

Uba Sani da El-Rufai dai abokai ne da suka daɗe a tare suna siyasa, inda El-Rufai ya tsayar da Uba a matsayin ɗantakarar gwamnan da yake so ya gaje shi bayan ya kammala wa'adinsa biyu.

Sai dai jim kaɗan bayan Uba Sani ya fara mulki, sai magoya bayansu suka fara takalar juna, lamarin da su biyun suka fara nuna cewa raɗe-raɗi ne kawai, ba tare da makama ba.

Daga baya tsamar ta fito fili, inda har ta kai tsohon gwamnan ya fito ya bayyana cewa ana masa bita da ƙullin siyasa daga jihar.

Daga baya El-Rufai ya fice daga APC, inda ya koma SDP, amma ake ganin yanzu yana alaƙa da ADC domin haɗakar fuskantar APC, inda ya kasance kan gaba wajen tallata haɗakar.

Wannan ya sa ake ganin El-Rufai yana so ya nuna cewa har yanzu yana da masoya a jihar, kuma zai iya ci gaba da juya alakar siyaar jihar.

A gefe ɗaya kuma, gwamnan jihar da masoyansa suna so su kasa su tsare, domin nuna wa duniya cewa yanzu lokacinsu ne, kuma su ne ke riƙa da akalar siyasar jihar a yanzu.

Shirye-shiryen zaɓen

Kwamishinan hukumar INEC reshen jihar Kano, Zango Abdu ya ce hukumar ta shirya gudanar da zaɓen cike gurbi na ƴan majalisa a jihar, amma ya ƙara da cewa babbar damuwar ita ce yanayin siyasar jihar.

Abdu ya kuma ce an raba muhimman kayayyakin zaɓe da sauran abubuwan da ake ɓukata ga ƙananan hukumomin huɗu gabanin zaɓen.

Kazalika baturen zaɓen ya ce an kammala yi wa mutanen da za su yi aikin zaɓen horo, kuma an samar da cikakken tsaro.

Ita kuma jam'iyyar ADC a Kaduna ta zargi jam'iyyar APC ne da ɗaukar ƴandaba da kuma ciro maƙudan kuɗi daga lalitar jihar domin gudanar da maguɗin zaɓen.

Sai dai Kwamishinan ƴaɗa labarai na jihar, Ahmed Maiyaki ya mayar da martani, inda ya ce zarge-zargen na ADC "ba su da tushe, kuma abin dariya ne."