Ƙalubalen da ke gaban sababbin gwamnonin Kano da Kaduna

Asalin hoton, TWITTER
Jihar Kano
Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar adawa za ta karɓi mulki daga jam'iyyar APC, bayan hukumar zaɓe ta ayyana Abba Kabir Yusuf, na NNPP, a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris.
Kamar kowace jiha a Najeriya, Kano na da nata matsalolin kuma hankalin al’ummar jihar ya karkata kan zaɓaɓɓen gwamnan Abba Kabir Yusuf, wanda za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu domin ganin salon mulkinsa da kuma ƙoƙarin da zai yi wajen magance matsalolin.
Ko waɗanne ƙalubale ke gaban Abba Gida-Gida?
Kabiru Sa’id Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan al’umma a kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci, CAJA, ya ce Abba Kabir, ya zama gwamna ne a "doro na tafiyar Kwankwasiyya" wadda matasa suka san ta kan bayar da ilimi kyauta ba wai iya matakin firamare da sakandare ba har ma jami'a a ciki da wajen Najeriya.
Masanin ya bayyana wasu daga cikin manyan ƙalubalen da Abba Kabir Yusuf, zai fuskanta.
Ƙalubalen kuɗi
Kabiru Dakata, ya ce zaɓaɓɓen gwamnan zai shiga gwamnati ne a lokacin da lalitar gwamnatin ke fama da rashin kuɗi, abin da ya ce babban ƙalubale ne domin "su matasa da za su amfana da wannan abu, burinsu shi ne daga fara aikin gwamnati, za a fara aiwatar da tsarin na ilimi kyauta."
Ya ce rashin kuɗi na iya kawo tarnaƙi wajen cika tsammanin matasa na ganin sabon gwamnan ya yi koyi da tsarin bayar da ilimi kyauta tun daga firamare har zuwa jami'a.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Biyan Basuka
Kabiru Dakata, ya ce ƙalubalen tulin bashin da ya yi wa gwamnatin Kano katutu wani lamari ne babba kasancewar basuka ne da ake bin jiha.
"Basussuka ne da aka yi wanda yarjejeniyarsu ta tanadi lokaci da za a biya". in ji Dakata.
Ya bayar da misali da wasu basukan da aka ƙayyade a biya cikin kowanne wata sannan lokacin biyan basukan bai ƙare ba.
A cewarsa, gwamnan zai zo ne ya fara tunkarar yadda zai biya ma'aikata albashi da kuɗaɗen da zai aiwatar da ayyukan more rayuwa da kuɗaɗen da zai biya basussukan.
Karɓo filayen da aka sayar
Ƙarin ƙalubalen da Kabiru Dakata ya ce gwamnan na Kano zai fuskanta shi ne batun sayar da filaye da wurare masu muhimmanci da gwamnati bai barin Kano ta yi ba bisa ƙa'ida ba.
Ya ce akasarin kadarorin na wuraren ci gaban al'umma ne kamar makarantu da asibitoci.
Kabiru Dakata ya bayar da misali da yadda aka sayar da ɓangaren asibitin Nasarawa da aka sayar wa makusantan gwamnan.
A cewarsa, gwamnan zai zo ne a yayin da yake neman yi wa jama'a ayyukan da za su mora a gefe guda kuma, yana ƙoƙarin yin duk yadda za a yi domin ganin kadarorin da aka sayar an maida wa gwamnati - wani batu da wataƙila sai an kai ga zuwa kotu.
Ya ƙara da cewa ba wai iya filaye bane aka yi gwanjonsu, har ma da fitulun kan titi da aka sayar.
Jihar Kaduna
A jihar Kaduna wacce Mallam Nasir El-Rufai zai mika mulki ga sabon zababben gwamna Sanata Uba Sani, akwai kalubale da dama wadanda sabon gwamnan zai tarar.
Dr. Tukur Abdulkadir, masanin siyasa ne a jami'ar jihar Kaduna KASU kuma ya ce duk da kokarin da gwamna mai barin gado Nasir El Rufai ya yi wajen saita al'amura a jihar Kaduna, akwai aiki a gaban sabon gwamna Uba Sani kuma zai gaji matsaloli da suka hada da;
Rashin tsaro
Dr. Tukur ya ce rashin tsaro matsala ce da ke ciwa al'ummar jihar Kaduna tuwo a kwarya musamman kudancin jihar.
"Garkuwa da jama'a ya na ci gaba da ta'azzara musamman a kauyuka da kuma sauran garuruwa da ke nesa da fadar jihar, dole ne sabon gwamna ya fito dqa tsare-tsare wadanda za su kawo karshen sace mutane domin su samu damar walwala a yankunansu" acewar Dr. Tukur.
Ya kuma kara da cewa jihar na fama da matsalar bangaranci da rikicin addini da kuma na kabilanci wadanda ke kara kawo rashin tsaro.
"Dole a takawa wannan abun birki saboda hada kan mutane sannan a samu zaman lafiya, duk da yake gwamnati mai barin gado tayi iyta kokarinta wajen magance hana tashe-tashen hankula to amma akwai bukatar sabuwa ta kara kaimi" in ji masanin siyasar.
Magance talauci da samar da aiki.
Fatara na daya daga cikin matsalolin da Uba Sani ya kamata ya magance a matsayinsa na sabon gwamna sannan ya samar da aiki ga dumbin matsa da ke jihar.
Dr. Tukur ya ce dole ne a farfado da masana'antu da Allah ya baiwa jihar Kaduna saboda za su samar da dubban ayyuka ga mutane da kuma hanyar samun abinci da kudaden shiga.
Har'ilayau, ya kara da cewa "inganta harkar noma tilas ne domin a mayarda manoma gonakinsu,a basu takin zamani sannan a magance matsalar manoma da makiyaya".
Malamin na harkokin siyasa ya kuma fadi muhimmancin da hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kano wajen samarda aiki ga mutanen Kaduna.
"Akwai kauyuka da dama da ke kan wannan titin kuma akasarinsu noma da kiwo al'ummarsu ke yi, lalacewar hanyar ya shafi yadda suke fitar da abinci da kuma dabbobinsu domin sayarwa, mutane basu son bin hanyar saboda lalacewarta.
Idan aka kammala aikin hanyar manona za su yi farin ciki domin za su rika fitar da abinci da su ke nomawa zuwa wurare da dama cikin sauki" inji Dr. Tukur.
Inganta ilimi
Wani kalubale da ke gaban Sanata Uba Sani shi ne yiwa harkar ilimi garambawul a Kaduna.
Dr. Tukur ya ce a halin da ake ciki sakamakon jarrabawa na makarantun sakandare a Kaduna babu yabo babu fallasa ne kuma ya kamata a ce dalibai da ke karatu a makarantun jihar su ciri tuta.
Baya ga wannan ya ce akwai matsala a jami'o'i
"Jami'o'i na fuskantar kalubale, ya kamata a samar da litattafai da kayan aiki da inganta albashin ma'aikata da kuma saukakewa dalibai kudin makaranta" a cewar Dr. Tukur.
Masanin siyasar ya kuma yi kira ga sabuwar gwamnati ta farfado da kwalejojin koyar da aikin yi da ke jihar.











