Yadda aka ceto mutum 26 bayan kifewar kwale-kwale a Neja

Asalin hoton, Twitter
An yi nasarar ceto mutum 26 bayan kifewar wani kwale-kwale a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Najeriya.
Kwale-kwalen na dauke ne da yankasuwa da ke kan hanyar zuwa cin kasuwar Zumba a yankin Kwata a ranar Asabar.
Hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja ta ce mutum 13 suka mutu a hatsarin kwale-kwalen da ke dauke da mutum 39.
"Ma'aikatan agaji sun yi nasarar ceto fasinja 26, yayin da aka samu gawar mutum 13 cikin fasinjan da ke cikin kwale-kwalen," in ji Alhaji Abdullahi Baba-Ara, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja.
Ya ƙara da cewa kwale-kwalen ya yi hatsari ne bayan ya ci karo da wani kututturi a cikin kogin Neja yankin Shiroro, kuma yana shaƙe da mutane da hatsi kusan buhu 50 har da dabbobi.
Hukumar agajin gaggawa ta Neja NSEMA ta ce ana ci gaba da aikin ceto domin neman waɗanda ke da sauran numfashi.
Hatsarin kwale-kwale ba sabon abu ne ba ne a Najeriya musamman a al'umomin da ke kusa da babban kogin Neja, duk da wayar da kan al'umma da hukumomi suke yi musamman amfani da rigar ruwa da kuma hana ɗaukar fasinja fiye da ƙima.
Sai dai wasu na zargin gwamnati da sakaci wajen rashin tilasta matakan kariya da samar da isassun kayan shiga ruwa ga al'ummar yankin da ke dogaro da kwale-kwale wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Akwai kuma matsalar rashin ingancin kwale-kwalen da mutane ke amfani da shi da babu inganci wajen ƙerawa, kuma babu wadatattu na zamani da gwamnati ta samar a matsayin hanyar sufuri.











