Nwaneri: Matashi ɗan Najeriya da ya ci wa Arsenal ƙwallo biyu a gasar Carabao

Asalin hoton, Getty Images
Matashin ɗan ƙwallon ƙafa mai shekara 17, Ethan Nwaneri ya zira ƙwallo biyu a wasan da Arsenal ta lallasa Bolton Wanderers da ci 5-1, nasarar da ta ba ta damar tsallakawa zagaye na huɗu a gasar Carabao Cup.
Wannan ne karo na farko da aka fara wasa da matashin a matakin babbar ƙungiyar ta Arsenal.
Ɗan ƙabilar Ibo ne daga yankin kudancin Najeriya, wanda iyayensa suka haifa a Ingila, wanda yanzu haka yake taka wa tawagar Ingila 'yan ƙasa da shekara 19 leda.
Ya taɓa kafa tarihin zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya taka wa Arsenal leda a gasar Premier League, lokacin da aka sako shi a wasan Arsenal da Brentford a kakar 2022/2023 - lokacin yana ɗan shekara 15 da wata 5 da kwana 38.
Da yake jawabi a kan Nwaneri, kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce, "Yana taka leda cikin natsuwa da yarda da kai, sannan ya san me ya kamata ya yi a cikin filin wasa.
"Duk lokacin da aka sako shi ya taka leda a babbar ƙungiyar, yana zarce abin da mutane suka yi tsammani. Don haka za mu ci gaba da ba shi dama," in ji Arteta.
Sauran waɗanda suka ci wa Arsenal ƙwallaye a wasan su ne Rice da Sterling, wanda shi ma wannan ce ƙwallonsa ta farko a Arsenal, sai kuma Kai Havertz.







