Yadda harajin Trump ke neman durkusar da kasuwancin China

    • Marubuci, Laura Bicker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, China correspondent
    • Aiko rahoto daga, Guangzhou
  • Lokacin karatu: Minti 6

"Trump yana da matsala," in ji Lionel Xu, wanda yake kewaye da kayayyakin kamfaninsa na maganin sauro – da dama daga cikin kayayyakin a baya suna daga cikin wadanda aka fi saye a kantunan Walmart na Amurka.

To yanzu dai wadannan kayayyaki suna nan jibge, katan-katan a manyan dakunan ajiyar kayayyaki a China, kuma za su ci gaba da kasancewa jibge a nan har sai Shugaba Trump ya janye harajin kashi 145 cikin dari da ya dora wa dukkanin kayan China da za a kai Amurka.

"Wannan abu ya jefa mu cikin mawuyacin hali," in ji shi.

Kusan rabin dukkanin kayan da kamfaninsa, Sorbo Technology, ke yi a Amurka ake sayar da su.

Karamin kamfani ne idan aka yi la'akari da sauran kamfanoni na China, kuma yana da ma'aikata kusan 400 a lardin Zhejiang.

To amma ba su kadai ba ne ke shan wahalar wannan dambarwa ta kasuwanci tsakanin Amurka da China ba.

"Mun damu sosai. Idan TRump bai sauya matsalarsa ba fa? Wannan zai zama babbar matsala ga ma'aikatarmu," in ji Mr Xu.

Haka ita ma, Amy da ke kusa wadda take taimakawa wajen sayar da na'urorin yin askirim na kamfanin Guangdong Sailing Trade Company, a kantinta, lamarin ya shafe ta. Manyan masu sayen kayayyakin nata, ciki har da Walmart, su ma suna Amurka ne.

"Tuni muka dakatar da kera na'urorin da muke yi," ta ce. "Dukkanin kayanmu suna ajiye a manyan dakunan ajiye kayayyakinmu."

Wannan shi ne labarin kusan dukkanin tarin kantunan da ke cibiyar masana'antu ta Guangzhou.

Lokacin da BBC ta yi magana da Mr Xu, ya fara shirye-shiryen kai wasu kayan ga masu saye a Australiya. Sun zo China inda suka tattauna a kan farashin kayayyakin da zummar cimma matsaya kan farashi mai sauki.

"Za mu zuba ido mu ga abin da zai faru," kan maganar harajin. Ya yi amanna Trump zai sauya shawara.

Mr Xu ya kara da cewa : "Watakila abubuwa za su sauya nan da wata daya ko biyu." A yanayi na addu'a ya ce watakila, watakila..."

Kasuwar China

Asalin hoton, Rachel Yu/ BBC

Bayanan hoto, Amurka da China dukkaninsu sun ƙaƙaba wa juna haraji
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A makon da ya gabata Shugaba Trump, ya dan dakatar da yawancin harajin da ya sanya, bayan da kasuwannin hannun haraji na duniya suka fadi, kuma aka yi ta karyar da takardun lamuni a kasuwar Amurka.

To amma duk da haka ya bar harajin da ya sanya a kan kayan China da ake shigarwa Amurka.

Ita ma gwamnatin China ta mayar da martani inda ta lafta harajin kashi 125 cikin dari a kan kayan Amurka da ake shigarwa China.

Wannan ya bai wa 'yankasuwa daga sama da kamfanoni 30,000 da suka zo kasuwar baje kolin ta shekara-shekara domin nuna kayansu a zaurukan holin kayan da ya kai girman filin wasan kwallon kafa 200.

A bangaren kayayyakin amfanin gida, kamfanoni sun baje na'urori iri daban-daban, inda masu saye ke zuwa dubawa daga kasashen duniya daban-daban, su ga kayan kuma su kulla kasuwancinsu.

To amma farashin kayayyakin hadi da harajin da aka sanya a yanzu sun sa kayan sun yi tsada ta yadda kamfanonin Amurka ba za su iya dora wannan nauyi na sayen kayan a wannan farashi mai tsada ba a kan kwastomominsu ba.

Manyan kasashen biyu da suka fi karfin tattalin arziki a duniya sun gamu da cikas, kuma kayayyakin China da za a kai Amurka a sayar suna ta kara taruwa jibge a kamfanoni.

Bisa ga dukkan alamu za a ga illar wannan dambarwar kasuwanci ta kasashen biyu ne a gidajen jama'a a Amurka saboda, yanzu dole ne Amurkawa da ke son wadannan kayayyaki su saye su da tsada.

China ta yi tsayuwar gwamen jaki kan matsayarta a wannan dambarwa ta kasuwanci da Amurka, kuma ta lashi takobin ci gaba da fafatawa har sai ta kai karshen lamarin.

Hy Vian, wanda ke son sayen wasu rusho-rusho ga kamfaninsa, ya yi watsi da batun sanya harajin na Amurka.

Ya ce, '' Idan ba sa so mu fitar da kayan waje - sai su jira. Tuni mu muna da masu saye a cikin gida, China, za mu rika sayar wa da al'ummar China kayayyakin da suka fi kyau, kafin mu fitar da sauran zuwa waje. Sai mutanenmu sun fara zaba sun darje."

Hoton Lionel Xu

Asalin hoton, Rachel Yu/ BBC

Bayanan hoto, Lionel Xu ya ce ya damu kan abin da zai faru idan Trump ya ki janye harajin kan China

China tana da yawan al'umma biliyan 1.4 saboda haka idan aka duba wannan ba karamar kasuwa ba ce ta cikin gida.

Shugabannin China su ma sun yi kokarin bunakasa kasuwar ta cikin gida ta hanyar sa 'yan kasar su rika sayen kayan a cikin gida.

To amma hakan bai samu ba, saboda yawancin masu matsakaicin hali na kasar sun zuba kudadensu wajen sayen gidajensu, kuam bayan su zuba kudin a wannan bangare sai kasuwar gidajen ta yi kasa a shekara hudu da ta gabata. To yanzu kuma suna son tsimin kudinsu ne - ba kashe kudinsu ba.

Duk da cewa China ce kasar da ake ganin za ta iya jure wannan dambarwa ta haraji fiye da sauran kasashe, maganar gaskiya ita ce ita China kasa ce da tattalin arzikinta ya ta'allaka ga fitar da kaya waje, amma ba cinikin cikin gida ba.

Haka kuma China ita ce har yanzu kamar masana'antar duniya domin kiyasin kamfanin zuba jari na Goldman Sachs ya nun acewa akwai kimanin mutum miliyan 10 zuwa 20 a China da suke aiki a masana'antun da ke yin kayan da ake kaiwa Amurka.

Tuni wasau daga cikin wadannan ma'aikatan ke cikin radadin wannan dambarwa ta haraji.

Wani ma'aikaci a China

Asalin hoton, Xiqing Wang/ BBC

Bayanan hoto, BBC ta ziyarci wata masana'anta a kauyen Guangzhou wadda ta fara mayar da hankalinta daga mai fitar da kaya waje zuwa mai sayarwa a cikin gida

Wasu ma'aikata a gefen titikusa da wasu ma'aikatun yin takalma, suna zaune suna hira suna shan taba.

" Abubuwa sun baci," in ji wani daga cikinsu da ba ya son ya fadi sunansa. Abokinsa ya ce ya daina magana ya kame bakinsa. Yin magana a kan abin da ya shafi matsalar tattalin arziki abu ne da hukumomin China ke sa ido a kai.

"Muna da matsaloli tun lokacin annobar Korona, kuma yanzu ga wanna dambarwa ta kasuwanci. A da ana biyana yuan 300-400 ($40-54) a duk rana, to amma yanzu na yi sa'a idan har na samu yuan 100 a rana."

Mutumin ya ce da wahala mutum ya samu aiki a yanzu. Sauran mutanen da suke yin takalmi a gefen titi sun gaya mana cewa sun ce suna samun abin da za su biya muhimman bakutunsu ne kawai a yanzu.

Yayin da China ke fuskantar hadarin rasa abokiyar kasuwanci da ke mata cinikin da ya zarta na dala biliyan 400 a duk shekara, to amma ita ma Amurkar ba za ta sha ba, domin masana na gargadin cewa za ta iya gamuwa da matsalar durkushewar tattalin arziki.

Mutane na kai komo a wata kasuwa

Asalin hoton, Xiqing Wang/ BBC

Bayanan hoto, Wata kasuwar bajekoli a Guangzhou ta ce ta daina shigar da kaya Amurka

Wanda ke kara haddasa rashin tabbas a kan halin da ake ciki, shi ne Trump, mutumin da aka sani da kafiya a kan lamarinsa.

Yayin da yake kara tsananta al'amura ita kuwa China ta ki bayar da kai ta kafe a kan matsayinta.

To amma duk da haka Chinar ta ce ba za ta yi kari a kan harajin ramuwar gayya na kashi 125 da ta sanya wa kayan Amurka ba.

Ko ba komai hakan ya bayar da wata kafa ta samun sauki a kan lamari - illa dai za ta iya ci gaba da ramuwar gayya ta wata hanyar.

Rahotanni na cewa babu wani yunkuri na tattaunawa tsakanin bangarorin biyu na China da Amurka a nan kusa.

A halin yanzu dai wasu kamfanonin na China da ke wannan baje koli ( Canton Fair), suna amfani da damarsu wajen neman wata sabuwar kasuwar da za su karkatar da kayansu.

Wasu sun ce suna fatan karkata ga Turai ko SaudiArabia da ma Rasha.

Wasu ma kuma suna ganin har yanzu za su iya cin kasuwarsu a cikin kasar ga China.

Masu yin takalma da dama a China a yanzu sun koma Vietnam inda kudin yin takalman bai kai yawan da suke biya ba a China.

Wasu daga cikin masu harkokin kasuwancin kamar sauran abokansu sun gano cewa wannan wata dabara ce ta Amurka ta gurgunta China.