Al’umma sun fusata bayan kotu ta wanke wanda ake zargi da yi wa matarsa fyaɗe har ta mutu

A volunteer from a non-governmental organisation (NGO) holds a placard during a protest in New Delhi on October 11, 2020 to condemn the alleged gang-rape and murder of a teenaged woman in Bool Garhi village at Hathras in Uttar Pradesh state

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Indiya na cikin wasu kasashen da ba su yadda cewa fyaɗe tsakanin ma'autrata laifi ba ne
    • Marubuci, Geeta Pandey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, London
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gargadi: Wannan rahoto ya ƙunshi wasu bayanai masu tayar da hankali.

Hukuncin da wata kotu a Indiya ta yanke na cewa wani mutum ya tilasta wa matarsa ​ "saduwa da shi karfi da yaji" ba laifi ba ne, ya haifar da gagarumin ɓacin rai tare da kiraye-kirayen samar da kyakkyawar kariya ga matan aure.

Wannan doka mai cike da cece-ku-ce ta kuma mayar da hankali kan batun fyaɗe tsakanin ma'aurata a ƙasar da ta ki amincewa da aikata hakan a matsayin laifi.

A farkon makon nan ne wani alƙalin wata kotu a jihar Chhattisgarh da ke tsakiyar ƙasar Indiya ya saki wani mutum ɗan shekara 40 da wata kotu ta ɗaure a shekarar 2019 kan laifin yin fyaɗe da kuma lalata da matarsa, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.

Kotun ta kuma samu mutumin da laifin "kisan kai". An yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 da horo mai tsanani a kan kowace tuhuma, yayin da hukuncin za su gudana ne a lokaci guda.

Sai dai a ranar Litinin mai shari'a Narendra Kumar Vyas na babbar kotun ƙasar ya wanke mutumin daga dukkan tuhumar da ake yi masa, yana mai cewa tun da Indiya ba ta amince da cewa ana fyade tsakanin ma'aurata ba, ba za a iya samun mutumin da laifin yin jima'i da matarsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Hukuncin ya fusatar da al'umma, yayin da masu fafutuka da lauyoyi suka sabunta kiraye-kirayen da suke yi na a fara hukunta fyaɗe tsakanin ma'aurata a Indiya.

"Gani yadda mutumin nan zai tafi ba tare da hukunci ba, wani babban tashin hankali ne. Wannan hukunci na iya zama daidai bisa doka, amma abin kyama ne a ɗabi'ance," in ji lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙn jinsi Sukriti Chauhan.

Ta shaida wa BBC cewa "Hukuncin da ya wanke mutum daga irin wannan laifin, a ce ba laifi ba ne, ba ƙaramin koma baya ba ne a tsarin shari'armu."

"Ya girgiza mu sosai. Wannan yana buƙatar sauyi kuma ya kamata a sauya cikin hanzari."

A doctor is painting a mural with slogans inside Kolkata Medical College and Hospital campus condemning the rape and murder of a trainee medic at a government-run hospital, in Kolkata, India, on August 19, 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cin zarafin mata ya zama ruwan dare a Indiya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Priyanka Shukla, wata lauya a Chhattisgarh, ta ce hukunci irin wannan "na nuna cewa saboda kai ne mijin, kana da haƙƙoƙi. Kuma za ka iya yin duk abin da ka ga dama, har ma za ka iya tsira da kisan kai".

Ta ƙara da cewa ba wannan ne karon farko da kotu za ta yanke irin wannan hukuncin ba, kuma a ko da yaushe hakan na janyo matuƙar ɓacin rai.

"A wannan karon, abin ya fi zafi saboda matar ta mutu."

A cewar masu gabatar da ƙara, lamarin ya faru ne a daren ranar 11 ga watan Disamban 2017, lokacin da mijin wanda direban mota ne, "ya yi jima'i da wata ba bisa ƙa'ida ba, kuma ba tare da son ranta ba... inda ya jefa ta cikin mawuyacin hali".

Bayan ya tafi aiki sai ta nemi taimako daga wajen yayarsa da wani ɗan‘uwansa, inda suka kai ta asibiti amma ta rasu bayan wasu ƴan sa'o'i.

A bayanin da ta yi wa ƴansanda da bayanin da ta yi wa wani alƙali yayin da take gab da mutuwa, matar ta ce ta kamu da rashin lafiya "saboda saduwa ƙarfi da yaji da mijinta ya yi da ita".

Kotu na daukar duk wani bayani da mutum ya yi a lokacin da zai mutu da matukar muhimmanci, kuma masana shari'a sun ce za a iya dogara da shi a yanke hukunci, sai dai idan wasu shaidu sun ƙaryata hakan.

Yayin da take yanke wa mutumin hukunci a shekarar 2019, kotun da ke sauraron ƙarar ta dogara kacokan kan bayanan matar da kuma rahoton binciken da aka gudanar a kan gawar, wanda ya bayyana cewa "abin da ya yi sanadin mutuwarta shi ne peritonitis" - abin da hakan ke nufi a sawwaƙe shi ne, munanan raunuka da ta samu a cikinta da al’aurarta.

Mai shari'a Vyas, duk da haka, ya dubi al'amuran ta wata fuska ta daban - ya ƙalubalanci bayanin da matar ta yi gabannin mutuwarta, ya yi la'akari da cewa wasu shaidun sun janye shaidar da suka bayar kuma, mafi mahimmanci, ya ce fyaɗe tsakanin ma'aurata ba laifi ba ne a Indiya.

A doctor is painting a mural with his hand with slogans inside Kolkata Medical College and Hospital campus condemning the rape and murder of a trainee medic at a government-run hospital, in Kolkata, India, on August 19, 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gabatar da ƙorafe-ƙorafe da dama a shekarun baya-bayan nan da ke neman a hukunta aikata laifin fyaɗe tsakanin ma'aurata

Hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke ya kasance "abin da ba a saba gani a fagen shari'a ba," in ji Ms Shukla, "wataƙila saboda matar ta mutu".

"Amma wani abin mamaki game da hukuncin da babbar kotun ta yanke shi ne babu ko da wani tsokaci na tausayawa daga bakin alƙalin."

Idan aka yi la'akari da yanayin harin, umurnin da babbar kotun ta bayar ya zo wa mutane da yawa da mamaki, inda suke ganin bai kamata alƙali ya yi watsi da hukuncin ba.

Indiya na cikin ƙasashe fiye da 30 - tare da Pakistan da Afganistan da Saudiyya - inda fyade tsakanin ma'aurata ba laifi ba ne.

An gabatar da ƙararraki da dama a cikin ƴan shekarun nan na neman soke sashe na 375 na kundin hukunta manyan laifuka na Indiya, wanda ya kasance tun shekara ta 1860.

Dokar Burtaniya ta zamanin mulkin mallaka ta ambaci wasu lokuta da jima'i bai kasance fyaɗe ba - kuma ɗaya daga cikin lokutan shi ne "tsakanin namiji da matarsa" muddin ba ta yi ƙasa da shekaru 15 ba.

Burtaniya ta haramta fyaɗe tsakanin ma'aurata a shekarar 1991 amma Indiya, wadda kwanan nan ta sake sabunta kundin laifukanta, ta ci gaba da amfani da daɗaɗɗiyar dokar.

Students, citizens, and medical professionals are holding placards and shouting slogans in a protest march named 'The Night is also ours' on the 78th Independence Day against the rape and murder of a trainee woman doctor at Government-run R G Kar Medical College & Hospital, in Kolkata, India, on August 15, 2024

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ra'ayin ya samo asali ne daga imani cewa muddin mace ta yarda ta yi aure hakan na nufin ta amince da jima'i ke nan a kodayaushe da wannan mutumin da ta ke kira mijinta.

Masu fafutuka sun ce bai ma kamata irin wannan cece-ku-ce ya taso a zamanin yanzu ba, kuma tilasta jima'i fyaɗe ne, ba tare da la'akari da wanda ke aikata hakan ba.

Amma a ƙasar da ake mutunta auratayya da iyali, al'amarin ya janyo bambance-bambancen ra'ayoyi kuma ana fuskantar turjiya sosai kan batun haramta fyaɗe tsakanin ma'aurata.

Gwamnatin Indiya da shugabannin addinai da masu rajin kare haƙƙin maza sun nuna adawa da matakin.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata, gwamnati ta shaida wa kotun ƙolin ƙasar cewa haramta fyade tsakanin ma'autrata zai kasance mataki "mai tsanani sosai". Ma'aikatar cikin gida ta tarayya ta ce "yana iya haifar da babbar matsala a harkar aure".

Hukumomin sun kuma dage kan cewa akwai isassun dokokin da za su kare matan aure daga cin zarafi mai alaƙa da jima'i. Sai dai masu fafutuka sun ce Indiya ba za ta iya fakewa da tsoffin dokoki ba wurin tauye wa mata haƙƙnsu.