India: Ana murnar kisan masu fyade a Indiya

Masu zanga-zanga a India
Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a wajen ofishin 'yan sanda da ke Hyderabad a lokacin da aka yi wa matar fyade

'Yan sanda a India sun harbe mutum hudu da ake zargi da yi wa matashiya fyade tare da kashe ta a makon da ya wuce a birnin Hyderabad.

Tun da fari ana tsare da mazan hudu a ofishin 'yan sanda. Daga nan ne kuma aka wuce da su kotu, sannan a safiyar Juma'a aka sake mayar da su ofishin.

An harbi wadanda ake zargi da aikata fyaden a lokacin da suka kwace bindigogin jami'an tsaron, kamar yadda 'yan sandan yankin Telugu suka shaida wa BBC.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam ciki har da Amnesty International, sun yi kiran a gudanar da bincike kan abin da suka kira kisa ba bisa ka'ida ba da aka yi wa mazan.

Babban daraktan Amnesty a Indiya Avinash Kumar ya ce wannan kisan da aka yi masu ba shi zai kawo karshe ko kare afkuwar fyade a kasar ba.

Jim kadan bayan yaduwar labaran mutuwar mutanen, mahaifiyar matashiyar ta ce ''an yi wa 'yar ta adalci,'' yayin da makobtansu suka fara murna ta hanyar harba tartsatsin wuta sama, dubban mutane kuma suka cika tituna tare da jinjinawa 'yan sanda.

Wanne dalili 'yan sanda suka bayar kan harbin mutanen?

'Yan sanda 10 dauke da bindigogi ne suka fita da mazan hudu, wadanda ba a sanya masu ankwa a hannu ba.

Sun kai su wurin da aka aikata laifin a Cyberabad domin sake duba wurin kamar yadda mataimakin kwamishinan 'yan sanda VC Sajjanar ya shaida wa BBC.

Wurin da aka aikata fyaden, akwai manyan kamfanonin fasaha kamar Microsoft da Google.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce: '''Yan sandan suna neman wayar salula, da abin cajin waya da agogon wadda aka yi wa fyaden, wadanda kuma aka nema aka rasa.''

An tambayi kwamishinan dalilin da ya sa aka kashe mutanen. Ya kada baki ya ce: ''Mazan hudu sun fara jifan 'yan sandan da duwatsu da sanduna, tare da kwace bindigar biyu daga cikin 'yan sandan tare da harbe-harbe.

''Duk da cewa 'yan sandan sun bukaci masu laifin su ajiye bindigogin, sai suka ki yadda kuma suka ci gaba da harbi.

"Sun dauki minti 15 ana abu daya, babu yadda za mu yi dole muka mayar da martani, a nan aka kashe mutane hudun,'' inji kwamishina Avinash.

Biyu daga cikin jami'an tsaron sun ji rauni a kai, amma ba harbin bindiga ba ne, kuma tuni aka garzaya da su asibiti.