Indiya za ta ƙaddamar da wata doka mai nuna 'wariya' ga Musulmai

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin ƙasar Indiya ta sanar da shirin ƙaddamar da wata doka mai cike da cece-ku-ce, wadda kuma ake suka kan cewa tana nuna wariya ga Musulmai.
Dokar ta ɗanƙasa(CAA) za ta bai wa mutanen da ba Musulmai ba da ke bin wasu addinai da suka kasance marasa rinjaye a Pakistan, Bangladesh da kuma Afghanistan damar zama ƴanƙasa.
Hukumomi sun ce hakan zai taimaka wa waɗanda ake gallaza wa.
An sanya hannu a dokar a shekarar 2019 - abin da ya janyo gagarumar zanga-zanga, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane, aka kuma tsare wasu da dama.
Ba a tsara dokokin ba ne saboda tashin hankali da ya taso, amma kuma a yanzu saboda hakan ne za a aiwatar da su, a cewar ministan cikin gida na ƙasar, Amit Shah.
A ranar Litinin ya yi sanarwar, inda ya rubuta a shafukan sada zumunta cewa Firaiminista Narendra Modi "ya cika wani alƙawarin da ya ɗauka ta yin la'akari da alƙawarin da waɗanda suka tsara kundin tsarin mulkin suka ɗauka ga mabiya addinan Hindu, Sikh, Buddha, Jain, Parsi da kuma kiristanci da ke zaune a waɗannan ƙasashe."
Ma'aikatar cikin gidan ƙasar ta fitar da wata sanarwa wadda ta ce mutanen da suka cancanta, a yanzu za su iya neman zama ƴan ƙasar ta Indiya ta hanyar intanet.
Tuni aka buɗe wani shafin intanet domin yin hakan.
Ma'aikatar ta ce akwai "rashin fahimta sosai" game da dokar, kuma annobar Korona ce ta kawo jinkiri wajen aiwatar da ita.
Ya ƙara da cewa "Wannan dokar ta shafi waɗanda suka kwashe shekaru suna fuskantar muzgunawa ce, kuma ba su da wani matsuguni a duniya sai Indiya,"
Aiwatar da dokar na daga cikin muhimman alƙawuran da jam'iyyar mabiya addinin Hindu ta mista Modi mai mulkin ƙasar(BJP) ta ɗauka gabannin babban zaɓen da za a yi a wannan shekarar.
An yi wa dokar ɗanƙasar mai shekara 64 ne gyaran fuska, ta samar da wannan dokar wadda a yanzu ta haramta wa baƙin-haure zama ƴan ƙasar ta Indiya.
A ƙarƙashin dokar, masu neman zama ƴan ƙasar dole su ba da hujjar cewa sun shiga Indiya daga ƙasashen Pakistan, Bangladesh da kuma Afghanistan kafin 31 ga watan Disambar 2014.
Sanarwar ta ranar Litinin ba ta zo da mamaki ba ga shugabannin jam'iyyar ta BJP ba, waɗanda suka riƙa yin hannunka mai sanda a watannin da suka wuce kan aiwatar da dokar suna masu cewa za a iya yin hakan gabannin zaɓukan ƙasar.
A ɗaya ɓangaren kuma an fara zanga-zanga a wasu sassan ƙasar kan aiwatar da dokar, inda wata ƙungiyar ɗalibai ta (AASU) - wadda ta jagoranci boren da aka yi a 2019 a jihar arewa-maso-gabashi - ta yi kira da a dakatar da komai a ranar Talata.
A jihar Kudanci ta Kerala, jam'iyya mai mulki mai ra'ayin kwaminisanci ta yi kira da ayi zanga-zanga a baki ɗaya jihar.
"Wannan dokar za ta raba kan mutane ne, ta janyo son kai tsakanin al'umma, tare da gurgunta muhimman dokokin kundin tsarin mulki," In ji babban minista, Pinarayi Vijayan, ya na mai bayyana cewa ba zai aiwatar da dokar a jiharsa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu sukar dokar sun ce tana nuna wariya kuma hakan ya saɓa wa dokokin da suka sanya ƙasar ta zama wadda ba ruwanta da addini kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, wanda kuma ya haramta nuna wariya saboda bambancin addini.
Misali, sabuwar dokar ba ta haɗa da mutanen da ke guje wa muzgunawa a ƙasashen da mafiya yawan al'ummarsu ba Musulmi ba ne, kamar ƴan ƙabilar Tamil masu gudun hijira da suka tsere daga Sri Lanka.
Haka zalika ba ta haɗa da Musulmai ƴan ƙabilar Rohingya ba daga makwabciyar ƙasar Myanmar.
Ana nuna damuwa cewa idan tayin rajistar ƴan ƙasa, za a iya amfani da dokar wajen muzguna wa kimanin Musulmai miliyan 200 da ke ƙasar.
Wasu Indiyawa, ciki har da waɗanda ke zaune a bakin iyakar ƙasar suna nuna damuwa cewa aiwatar da dokar zai janyo musu kwararan masu ƙaura.
Ƴan'adawa da ke zargin gwamnati da yin amfani da dokar wajen samun nasarar zaɓe mai zuwa, ba su ji daɗin sanarwar ta ranar Litinin ba.
Ana sa ran yin zaɓen a watan Mayu kuma Fiaraiminista Narendra Modi na neman zarcewa a karo na uku a kan mulki.
"Bayan an sha ɗage aiwatar da dokar a cikin shekara 4, aiwatar da ita kwana biyu ko uku kafin sanar da zaɓe na nuna cewa an yi hakan ne bisa dalilai na siyasa." A cewar shugaban jam'iyyar Trinamool Congress party, Mamata Banerjee a yayin wata zantawa da manema labarai.
Jairam Ramesh, shugaban sadarwa na jam'iyyar Indian National Congress, ya rubuta a dandanlin sada zumunta cewa: "lokacin da aka ɗauka kafin sanar da dokokin (CAA) wata manuniya ce ta ƙaryar da Fiariminsta ke shararawa".
Asaduddin Owaisi, shugaban jam'iyyar All India Majlis-e-Ittehadul Muslimeen, ya ɗora ayar tambaya ce a kan lokacin da aka zaba na ɗaukar matakin.
"CAA an yi ta ne kawai domin cuzguna wa Musulmai, babu wata manufa da ta wuce hakan," ya rubuta a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter).







