Kalli sabon wurin bautar Hindu da aka gina kan filin masallaci
Kalli sabon wurin bautar Hindu da aka gina kan filin masallaci
Firaministan Indiya, Narendra Modi ya ƙaddamar da wurin bauta na ubangijin mabiya addinin Hindu, Ram a birnin Ayodhya.
Wurin bautar ya maye gurbin wani masallaci da aka gina a ƙarni na 16, wanda mabiya addinin Hindu suka ƙona a 1992.
Yawancin masu adawa da gwamnatin Modi ba su halarci bikin buɗewar ba, suna zargin cewa firaministan na amfani da addini domin cin gajiyar siyasa.
Kalli bidiyon domin samun bayani kan abin da ya sa ake ce-ce-ku-ce kan wurin bautar.



