Mutumin da ke 'latsa' kwamfuta da tunaninsa ya gode wa Elon Musk

- Marubuci, Lara Lewington, Liv McMahon da Tom Gerken
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Saka wa mutum maganaɗisu a cikin ƙwaƙwalwa zai iya bayar da damar mayar da tunaninsa cikin kwamfuta - abu kamar tatsuniya - amma kuma haka rayuwar Noland Arbaugh.
A watan Janairun 2024 - shekara takwas bayan ɓarin jikinsa ya shanye - matashin mai shekara 30 ya zama mutum na farko da kamfanin Neuralink ya saka wa irin wannan maganaɗisun.
Ba wannan ne karon farko da aka saka wa mutum na'ura a ƙwaƙwalwa ba, amma na Noland ya ja hankali ne saboda wanda ya mallaki kamfa Neuralink shi ne Elon Musk, attajirin duniya.
Amma Noland ya ce abu mafi muhimmanci shi ne kimiyyar da ake amfani da ita ba wai shi ko kuma Musk ba.
Ya faɗa wa BBC cewa ya san irin kasadar da ya ɗauka - amma dai "ko ma me zai faru zan bayar da taimakona ne".
"Idan komai ya tafi yadda ya kamata, to zan taimaka wa Neuralink," in ji shi.
"Idan kuma lamarin bai yi kyau ba, na san za su koyi darasi kan hakana."
'Babu iko, babu sirri'
Noland wanda mazaunin Arizona ne, ya gamu da shanyewar jikinsa daga ƙasan kafaɗa ne a wani hatsarin ninƙaya a 2016.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Raunukan da ya ji sun yi munin da har ma ya yi fargabar ba zai iya ci gaba da karatu ba, ko aiki ko kuma ma ci gaba da wasa.
"Kawai dai mutum ba shi da wani iko, babu sirri, lamari ne mai wuya," in ji shi.
"Dole ne mutum ya saba da tunanin cewa rayuwarsa ta koma dogara da wasu a kan komai."
An saka maganaɗinsun na Neuralink ne domin dawo masa da wani ɓangare na ikon da yake da shi kan rayuwarsa, inda zai iya sarrafa kwafuta da zuciyarsa.
Wannan ake kira brain computer interface (BCI) a Turance - wanda ke aiki ta hanyar gane alamun aiki idan mutum ya yi tunanin aikata wani aiki kamar motsi, sai kuma ya sarrafa alamun zuwa umarni ga na'ura, kamar matsar da kibiyar kwamfuta a kan fuskarta.
Fage mai sarƙaƙiya da ƙwararrun masana kimiyya ke aiki a kai tsawon shekara.
Shigar mai kuɗin duniya Elon Musk harkar ta jawo shaharar kimiyyar - har ma da Noland - a kafofin yada labarai.
Hakan ya sa Neuralink ya samu masu zuba jari da yawa da kuma saka ido kan lafiyar aikin.
Lokacin da aka sanar da saka wa Noland na'urar, masana sun yabi aikin a matsayin "babban cigaba".
Musk bai fiya magana kan lamarin ba a lokacin, sai wani saƙo kawai da ya wallafa a shafinsa yana cewa: "Sakamakon farko-farko ya nuna alamun nasara wajen gano motsin tunani a ƙwaƙwalwa."
A fili kuma, Noland ya ce attajirin ya zaƙu sosai. Sai dai ya jaddada cewa batun Neuralink ya zarta mamallakinsa, kuma ba shi kallonsa a matsayin "na'urar Elon Musk".
Tasirin wannan na'urar a rayuwar Noland yana da yawa sosai.
'Bai kamata wannan ya yiwuwu ba'

Lokacin da Noland ya farka bayan yi masa tiyatar saka maganaɗisu, ya ce ya fara iya sarrafa hannun kwamfuta (cursor) a kan fuskarta ta hanyar tunanin motsa yatsunsa.
"Magana ta gaskiya ban san ma me zan yi tunani ba - abin ya fi kamata fim," a cewarsa.
Amma bayan ya ga ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwarsa sun yunƙura a na'ura - ya ce sai abin ya zamar masa wani iri cewa wai zai iya sarrafa kwamfuta da tunaninsa kawai.
Daga baya yakan iya amfani da na'urar wajen yin wasan dara (chess) da buga wasan game na bidiyo.
"Na taso ina yin wasan game," in ji shi yana mai cewa dole ta sa ya haƙura da shi saboda larurarsa.
"Yanzu nakan iya doke abokaina a wasan, abin da bai kamata ya faru ba, amma kuma dai yana faruwar."
"Ɗaya daga cikin matsalolin shi ne muutum ba shi da sirri," a cewar Anil Seth, farfesa a ɓangaren kimiyyar ƙwaƙwalwa a jami'ar University of Sussex.
"Saboda haka idan muna fitar da ayyukan da ƙwaƙwalwarmu ke yi [...] kamar muna bai wa sauran mutane damar sanin abin da muke tunani ba wai kawai abin da muke aikatawa ba, da abin da muka ƙudirce, da abin da muke ji a ranmu," in ji shi.
"Indai aka samu damar sanin abubuwan da ke cikin ƙwaƙwalwar mutum, to ai babu wani abu na sirri da ya rage kuma."
Noland ya ce yana fatan na'urar za ta ba shi damar sarrafa kujerar da yake zaune, ko kuma ma wani mutum-mutumi a nan gaba.
Wani zubin akan samu matsalar katsewar layi tsakanin maganaɗisun da kuma ƙwaƙwalwarsa, abin da ke sa ya rasa ikon sarrafa kwamfutar.
"Abin ɓacin rai ne sosai idan haka ta faru," a cewarsa.
"Ban sani ba ko zan iya ci gaba da aiki da Neuralink nan gaba."
An gyara matsalar network ɗin kuma ya ci gaba da aiki lafiya kalau, amma hakan na ƙara fito da matsalar da masana ke yawan nuna fargaba a kai kan dogara da fasahar.
Babban kasuwanci
Neuralink ɗaya ne cikin manyan kamfunnan da ke bincike kan yadda za a iya shiga cikin ƙwaƙwalwar ɗan'adam.
Synchron na cikinsu, wanda ya ce maganaɗinsa Stentrode zai taimaka wa mutane guje wa yi musu tiyata kan ƙananan larurori.
Maimakon a buɗe kan mutum, ana saka shi ne a wuyan mutum, sai kuma a tura shi zuwa ƙwaƙwalwa ta cikin jijiya.
"Takan fara aiki ne duk lokacin da mutum ya fara tunanin ɗora hannu ko ƙin ɗora kan madannan kwamfuta," in ji shugaban sashen kimiyya na kamfanin, Riki Bannerjee..











