Janar din Uganda mai nuna ci da zuci a Twitter

Asalin hoton, AFP
Bayan horo da ya samu daga makarantun horas da sojoji masu daraja na duniya, dan gidan shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya zama janar din soja wanda yayi kaurin suna wajen aike sakonnin Twitter da ke janyo ce-ce-ku-ce daga ciki da kasar da kuma sauran sassan yankinsu.
Janar Muhoozi Kainerugaba ya cika baki kan cewa sojojinsa za su iya kama Nairobi babban birnin kasar Kenya, cikin kasa da mako biyu, ya kuma ja wa Masar da ke hamayya kunne kan cewa Uganda za ta iya shiga duk wani yaki na yankin arewacin Afirka, daya bangare da ya nuna sha'awa a kai shi ne gadar mahaifinsa mai shekara 78.
Ya ki bin umarnin da aka ba shi na ya daina janyo hayaniya a Twitter yana cewa: "Na mallaki hankalin kaina babu wanda zai hanani komai!".
Wani dan jaridar Uganda Solomon Serwanjja ya ce sakonnin Twitter da Janar Kainerugaba ke aike wa - na nufin "madaukin fansa" - da yake aikin soji da burin siyasa.
"Yana so ya tabbatarwa magoya bayansa cewa yana da 'yancin yanke hukuncin da ya ga dama. Kazalika zai zama dan da ke ci gaba da mayar da hankali ga umarnin mahaifinsa," in ji shi.
Mahafinsa Mista Museveni da ke kan mulki tun 1986, ana zargin ya dade yana horas da dan nasa mai shekara 48, domin ci gaba da mulkin da ake zargin sun mayar na mulukiya a Uganda.
"Iyalin da ke juya Uganda. Mahaifiyarsa na kan gaba, shi kuma shi ne yarima, da ke jiran gadar mahaifinsa," in ji Peter Kagwanja da ke cibiyar siyasa ta Afrika da ke Kenya. Kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya taba yi, shi ma Janar din yana amfani da Twitter ne domin daga likafarsa.
Farfesa Kagwanja na yi masa kallon "wakilin da zai iya tayar da hayaniya" wanda sakonninsa na Twitter ke kai wa ga shugabannin Afrika, su kuma kara habbaya abubuwan da siyasar Uganda ta sa a gaba, "Muhoozi ya fusata, sannan mahaifinsa ya nemi ya je ya nemi afuwa, ta haka ne aka gabatar da shi cikin zagayen wadanda za su iya zama shugabannin."
Manufarsa ta bayyana a fili ne lokacin da Janar Kainerugaba ya fusata da gwamnatin Habasha, lokacin da ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Masar a lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin da Habasha kan kan madatsar ruwa ta kogin Nilu.
Nesa da mayar da shi saniyar ware a Habasha, daga Twitter da ya aike ya ba shi damar ziyartar Firaiminista Abiy Ahmed da kuma wasu manyan jami'ai a farkon wannan shekarar.
Hakan ya sanya Janar ya sauya salonsa, ya yabi Mista Abiy mai shekara 46 a matsayin dan uwa, yana cewa:
"Mun yi imanin cewa matsalolin Afirka za a warware su ne kawai daga Afrika", yana bayyana ra'ayinsa da yayi daidai da na shugaban Habasha kan cewa masu kishin ci gaban Afirka ne.
'Mahaifin da dansa na aiki tare'
Janar Kainerugaba da ke amfani da sunan ahalinsu, yana bayyana yadda yake ganin shugabannin Afrika a matsayi daban daban da kuma yadda alakarsu take.
Ya bayyana shugaban Rwanda Paul Kagame a matsayi "Kawuna" kuma ya ziyarce shi a gonarsa.
Lokacin da wani rikici ya sanya aka rufe iyakar Rwanda da Uganda, ya yi kokarin dawo da alakar kasashen biyu ta hanyar hada zama tsakanin mahaifin nasa da "kawun nasa".

Asalin hoton, AFP
Yayin da abubuwa suka zo kan Kenya, Janar Kainerugaba ya wallafa cewa ya tattauna da tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta bayan ya sauka a karshen wa'adin mulkinsa biyu da ya yi a watan Agusta.
"Matsala daya dai ita ce Kawuna bai nemi wa'adin mulki na uku ba. Da mun ci mulki cikin ruwan sanyi!"
Wannan ya janyo koke-koke a tsakanin mutanen Kenya a Twitter, wadanda suka rika zargin Janar din da neman dakile musu dimokradiyyarsu.
Mista Museveni ya fi son Willian Ruto, wanda ya lashe zaben kasar a wani yanayi mai cike da bacin rai.
"Sakon Twitter na nuna gamsuwa da Kenyatta, da ba su so rasa shi ba saboda muhimmancin da yake da shi a siyasar Kenya," in ji Farfesa Kagwanja.
"Mahaifin da dan sun rika aiki tare a baya. Muhoozi ya gabatar da kansa a matsayin mai hamayya da mahaifinsa, ta yadda ya zama mai yawan janyo ce-ce-ku-ce, domin nuna mahaifinsa mutumin kirki ne."
'Dogon buri'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan kammala makarantar sojoji da ya yi ta Sandhurst a Birtaniya, Janar Kainerugaba ya fara darewa mukaman soji a Uganda, wanda ya shiga rundunar a 1999.
Yana da matar aure tare da 'ya'ya uku, kuma ya bayyana biyayyarsa ga addinin Kirista da kuma kimar iyalansa a Twitter.
Ya taka muhimmiyar rawa a wajen ilmantar da dakaru na musamman da ake kira SFC da ke ba da tsaro ga mahaifinsa, wadanda ake yawan zarga da take hakkin dan adam - ciki har da tsarewa tare da azabtar da 'yan adawa.
"A 2008 Muhoozi ya tashi ne cikin dakarun da suke bai wa mahaifinsa tsaro, wani matsayi da ya rike har 2017. Ya koma cikin tawagar a 2020 lokacin rikicin zabe," kamar yadda wani dan jarida Musinguzi Blanshe ke cewa.
Mista Serwanjja ya ce bayan korarsa da aka yi a matsayin kwamandan sojin kasa, babu wanda zai iya fada maka irin tasirin da yake da shi a rundunar sojin kasar.
Abin da ya bayyana shi ne Mista Museveni ya nuna fatan da yake da ita, cewa shi ne dan nasa ya gaje shi a zaben 2026 bayan duka abokansa - ciki har da mataimakin shugaban kasa da ministan cikin gida sun nuna goyon bayansu na ya dare bisa mukamin.

Asalin hoton, AFP
Wannan wani lokaci ne a baya da ya yi murnar cikarsa shekara 48 a duniya a watan Afrilu, kuma goyon bayan da ya samu daga wurare daban-daban ya kara daukaka likafarsa tsakanin matasa.











