Jerin ƙasashen Afirka da za su gudanar da zaɓe a 2023

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da duniya ta yi maraba da sabuwar shekara ta 2023, a Afirka batun daban yake duba da cewa a wannan shekarar ce za a samu zuwan sabbin gwamnatoci da za su mulki ƙasashe ashirin da huɗu a nahiyar.
A cewar cibiyar zaɓe da tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyya a Afirka, ƙasashen da za su gudanar da zaɓen shugaban kasa sun haɗa da Najeriya da Gabon da Liberiya da Libya.
Akwai kuma Madagascar da Saliyo da Sudan ta Kudu da Yankin Somaliland da Sudan da kuma Zimbabwe.
Sauran ƙasashen da za su gudanar da zaɓukan gundumomi sun hadar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Comoros da Ivory Coast da Djibouti da Masar da Ghana da Guinea-Bissau da Mali da Togo da kuma Swaziland.
Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta a Najeriya INEC, ta ƙara nanata zimmar ta na tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na ran 23 ga watan Febrairu cikin gaskiya da adalci duba da cewa idon duniya duka ya karkata kan zaɓen ƙasar.
Yayin magana a wani taro na musamman da cibiyar zaman lafiya ta Amurka da wasu cibiyoyin tabbatar da ingancin zaɓe suka shirya, shugaba Muhammadu Buhari shi ma ya jaddada bukatar ganin an gudanar da zaɓe mai gaskiya.
Ya ce "INEC a shirye take saboda na tabbatar da cewa an basu dukkan abubuwan da suke buƙata, don bana son wani uzuri na cewa gwamnati bata sake musu kuɗaɗe ba.’’
Gabanin zaɓukan da za a gudanar, jam’iyyu 18 ne suka fitar da ‘yan takara, inda na gaba-gaba sune Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour da kuma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.
Sauran sun haɗa da Imumolen Christopher na Accord da Majour Hamza Al-Mustapha da Sowore Omoyele na African Action Congress da Kachikwu Dumebi na ADC da Sani Yabagi Yusuf na ADP da Umeadi Peter na APGA da Ojei Princess Chichi na APM.
Akwai kuma Nnamdi Charles Osita na APP da Adenuga Sunday Oluwafemi Boot Party da Osakwe Felix Johnson na NRM da Abiola Latifu Kolawole na PRP da Adebayo Adewole Ebenezer na SDP.
Sai kuma Ado-Ibrahim Abdumalik na YPP da kuma Nwanyanwu Daniel Daberechukwu na Zenith Labour Party.
Ga jerin ƙasashen Afirka da irin zaɓukan da za su gudanar da kuma ranakunsu a 2023
1. Benin
Zaɓen ‘yan Majalisar Tarayya
24 ga Yunin 2023
2. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Zaɓen gundumomi
Janairun 2023
3. Comoros
Gwamnonin Tsibirai
2023
4. Côte d’Ivoire
Zaɓen gundumomi
2023
5. Djibouti
Zaɓen ‘yan Majalisar Tarayya
2023
6. Masar
Zaɓen gundumomi
2023
7. Gabon
Zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisa da kuma na gundumomi
2023
8. Ghana
Zaɓen gundumomi da na shiyyoyi
2023
9. Guinea
Zaɓen gundumomi
2023
10. Guinea-Bissau
Zaɓen ‘yan Majalisar Wakilai da ta Dattijai
2023
11. Liberiya
Zaɓen Shugaban ƙasa
10 Oktoba 2023
12. Libya
Zaɓen Shugaban ƙasa
Zaɓen ‘yan Majalisa
2023
13. Madagascar
Zaɓen Shugaban ƙasa
2023
14. Mali
Zaɓen ‘yan Majalisar Wakilai da ta Dattaɓai
Yunin 2023
Zaɓen gundumomi
Watannin Oktoba da Nuwamban 2023
15. Mauritania
Zaɓen ‘yan Majalisa Tarayya da na gundumomi
2023
16. Mozambique
Zaɓen gundumomi
11 Oktoba 2023
17. Najeriya
Zaɓen Shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Wakilai da kuma na Dattaɓai
25 ga watan Febrairun 2023
Zaɓen ‘yan Majalisar Dokokin Jihohi da kuma na Gwamnoni
11 ga watan Maris 2023
18. Saliyo
Zaɓen Shugaban ƙasa da ‘yan Majalisar Tarayya da kuma na Ƙananan Hukumomi
24 ga watan Yunin 2023
19. Yankin Somaliland (mai cin gashin-kansa)
Zaɓen Shugaban ƙasa
2023
20. Kudancin Sudan
Zaɓen Shugaban ƙasa da ‘yan Majalisar Tarayya da kuma na gundumomi
2023
21. Sudan
Zaɓen Shugaban ƙasa da na Kwamitin Zartaswa da ‘yan Majalisar Tarayya da na Jihohi da Gwamnoni da kuma na gundumomi
Yulin 2023
22. Swaziland
Zaɓen ‘yan Majalisar Dattaɓai da na Wakilai da Birane da kuma na gundumar Tinkhundla
2023
23. Togo
Zaɓen Larduna
2023
24. Zimbabwe
Zaɓen Shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Dattaɓai da na Wakilai da kuma na Gundumomi
2023











