Ci gaba da tsare Mohamed Bazoum na jawo ƙarin barazana

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Yusuf Akinpelu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, West Africa Journalist
Ci gaba da tsare tsohon shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum, wanda shugabannin juyin mulkin suka zarga da cin amanar kasa, ya ja hankalin shugabannin duniya daga Abuja zuwa Washington.
Kungiyar kasashen yammacin Afirka Ecowas ta tsayar da ranar da har yanzu ba ta bayyana ba na ɗaukar matakin soji a Nijar domin mayar da shugaba Bazoum kan karagar mulki, amma da farko suna ƙoƙarin tabbatar da an sake shi lafiya.
Mista Bazoum ana tsare da shi ne a fadar shugaban kasa a Yamai babban birnin Nijar tare da dansa da matarsa.
Sau biyu kawai aka samu ganawa da shi tun hamɓarar da shi a watan jiya lokacin da tawagar Ecowas ƙarƙashin jagorancin Janar Abdussalami Abubakar ta ziyarci ƙasar.
Kodayake, Mista Bazoum ya na rayuwa ne ba lantarki a inda ake tsare da shi, kuma sojojin sun ce hakan zai tabbata daga cikin tasirin takunkuman Ecowas, kamar yadda Janar Abdussalami ya shaida wa BBC.
Duk da takunkuman Ecowas, sojojin da suka yi juyin mulki sun yi watsi da dukkanin tayin da ake masu inda suka ce shekaru uku za su yi kan mulki, matakin da Ecowas ta yi watsi da shi.
Tuni sojojin suka naɗa firaminista na farar hula, Ali Mahaman Lamine Zeine, kuma sun ce gwamnatin ta 'riƙon ƙwarya' na tattaunawa ne kawai ga "aminanta da suka yi imani da ƴancin Nijar."
Tattaunawa za ta kuma ƙunshi makomar Mista Bazoum, wanda masana suka ce shi ne babban makamin sojojin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Idan har Ecowas ta taka ƙafa a ƙasar a yau, Bazoum ya zama babban abin dogaro," in ji Jaafar Abubakar, wani mai sharhi. "Idan suka kashe shi, sun zama wasu ƴan tawaye."
Bazoum zuwa yanzu ya ƙi miƙa wuya, inda ya ƙi yin murabus.
"Har yanzu yana kan bakarsa na tabbatar da an dawo masa da mulkinsa, in ji Janar Abdussalami.
Mista Bazoum ya shaida wa jaridar Financial Times a wata hira a farkon shekarar nan cewa "babu wata dama ta juyin mulkin sojoji a Nijar."
Amma bayan wata biyu hakan ta faru inda babban hafsan sojin tsaron fadar shugaban ƙasa Abdourahmane Tchiani ya kifar da gwamnatin Bazoum.
Babu dai wani tabbaci kan yadda Ecowas da aminanta za su karɓi Bazoum domin duk wani shiga tsakani za a iya zubar da jini.
A baya, lokacin da tsohon shugaban Saliyo Ahmad Tejah Kabba aka yi masa juyin mulki, sojojin da ke masa biyayya sun taimaka masa ya tsere zuwa Guinea da ke maƙwabtaka, kuma sojojin Ecowas suka abka ƙasar kuma suka dawo da shi bayan wata tara.
Shugabannin da aka haɓarar a ƙasashe maƙwabta ana tsare da su tsawon watanni. Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Faso an tsare shi tsawon wata biyu. Shugaban Guinea president Alpha Condé an tsare shi kusan wata takwas . Marigayi shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta an tsare shi ne kwana tara.
Hassan Stan-Labo, kanal din soja mai ritaya wanda ya yi yaƙi a Liberiya da Saliyo lokacin da sojojin Ecowas suka shiga ƙasashen, ya ce kamata ya yi Ecowas su bi hanyoyi na siyasa domin ganin an saki Bazoum an fice da shi daga Nijar.
Ya ce akwai manyan jami'an Nijar da suka samu hoto a Najeriya da Ecowas za ta iya dogaro da su.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai an fahimci cewa akwai tankiya tsakanin Bazoum da wani ɓangare na sojin Nijar kafin juyin mulkin, kamar yadda wata ƙungiyar da ke bincike kan rikici a duniya ta bayyana.
Mista Tchiani, wanda ya shafe shekaru 12 yana tsaron shugabannin Nijar tare da jagorantar wata rundunar manyan sojoji 700 da ke da motocin sulke ya daƙile tunƙurin juyin mulki a 2021, kwana biyu bayan rantsar da Bazoum.
Amma an rage masa ƙarfi da matsayi bayan da Mista Bazoum ya kafa wata runduna mai yaƙi da ta'addanci.
Tsawon watanni, ana tunanin shugaban na shirin korar Mista Tchiani a wani daftari. Wannan ya jefa shakku a fadar shugaban ƙasa inda wasu manyan jami'ai suka shiga fargabar za su iya rasa aikinsu.
A watan Maris, Mista Bazoum ya tuɓe babban hafsan soji da kuma shugaban hukumar tsaro ta jandarmeri Janar Salifou Modi tare da tura shi a matsayin jakada zuwa Daular Larabawa, wani mataki da masharhanta suka bayyana na dasa sojoji masu biyayya ga shugaban.
Lokacin da sojoji suka sanar da kafa gwamnati, Mista Modi ne suka bayyana mataimakin Tchiani.
Haka kuma, saboda Bazoum ya fito ne daga ƙabilar larabawa tsiraru a Nijar, sojojin da galibinsu Hausawa ne, na masa kallon wani baƙo, kamar yadda wani mai sharhi ya shaida wa BBC.

Asalin hoton, Getty Images
Juyin mulkin ya haifar da cikas ga wani ci gaban dimokuraɗiyya a Nijar, ƙasar da ta yi fama da juyin mulki sau huɗu tun samun ƴancin kai daga Faransa a 1960, da kuma rantsar da shugaba balarabe na farko a ƙasar.
Shugaban adawa Mahaman Ousmane, na jam'iyyar RDR-Tchanji wanda ya zo na biyu a zaben 2021 ya yi tir da juyin mulkin da kuma jerin takunkuman Ecowas yana mai kira maimakon yin amfani da ƙarfi a bayar da lokaci domin mayar da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya.
Mista Ousmane, zaɓaɓɓen shugababan Nijar na farko, shi ma sojoji suka hamɓarar da shi a 1996.
Mista Bazoum, tsohon malamin makarantar sakandare, yana da kyakkywar dangantaka da ƙasashen yammaci.

Asalin hoton, Getty Image
Mai haƙoron tabbatar da canji, ɗan shekara 63 tsohon ɗan gwagwarmaya, ya sha alwashin inganta ilimin ƴaƴa mata a ƙasar.
Bayan shekaru na taɓarɓarewar tattalin arziki, tsohon ministan harakokin cikin gida da na waje, ya samu damar farfaɗo da tattalin arzikin da aka yi hasashen zai samu ci gaba da kashi 7% a bana.
A zamaninsa, yawan hare-hare sun ragu daga 2021 da 2022. A farkon wata shida na 2023, hare-haren sun ragu da kashi 40 idan aka kwatanta da watanni shida baya, kamar yadda cibiyar binciken rikice-rikice a duniya ta Acled ta bayyana.
Wannan nasarorin da ake alaƙantawa da Bazoum sun shafi hulɗarsa da dakarun ƙasashen waje da kuma ƙoƙarinsa na sulhu da ƴan ta'adda domin tsagaita buɗa wuta.
Wannan ci gaban ya taɓarɓare. Tun juyin mulkin ranar 26 ga Yuli, an ci gaba da kai hare-hare kan sojojin ƙasar, musamman yankin Tillaberi da ke kan iyaka da Burkina Faso.
Yanzu akwai fargabar matsalar za ta ƙazance kamar yadda ta faru a ƙasashen Mali da Burkina Faso masu makwabtaka da Nijar











