Kasar da ake harbe mutum guda a kowacce awa daya

Rahoto daga Pumza FihlaniBBC News, Johannesburg
Kwararru a Afirka ta Kudu sun ce ana harbe mutum guda cikin kowacce awa a kasar.
Hakan ya sa mutane suke fama da tashin hankalin da ke biyo bayan harbe-harben bindigar.
"Kwana ake ana jin harbin bindiga. Harbe-harbe a kowanne dare," in ji wani mazaunin Soweto da bai son a ambaci sunansa.
A wannan garin da ke wajen birnin Johannesburg, aka harbe mutane 15 a wata mashaya a farkon watan nan inda suka mutu nan take.
Kwanaki kadan karin wasu suka mutu a gadon asibiti.
Rahotanni sun ce gungun mahara dauke da bingigogi ne suka afka wa mashayar da daddare tare da bude wa mashaya wuta sannan suka tsere.
Wannan harin da wadanda aka ci gaba da kai wa mashaya daban-daban, sun kara fitowa da hadarin da ake ciki a kasar Afirka ta Kudu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Na kai ziyara yankin Soweto, bayan kashe-kashen, inda na fahimci cewa har yanzu mutane na cikin firgici.
Sai dai suna da kyakkyawan fatan hukumomi za su dauki matakin da ya dace.
"Tun da na fara zama a wannan yankin shekara da shekaru, ‘yan sanda ba sa zuwa ko da mun kai rahoton bukatar haka.
Abin da suke fada mana shi ne, yankin ya fi karfinsu, yana cike da hatsari.
"Ban san dalilin da ya sa suke fadar haka ba, alhalin akwai mutanen da ke zaune a nan," in ji mutumin.
An dauki makwanni da kai harin, amma har yanzu ba a kama ko da mutum guda ba.
Sai dai laifukan harbin bindiga ba sabon abu ba ne a Afirka ta Kudu, ko a yankin Soweto.
A nan na hadu da wata uwa a Cape Town, mai suna Lesley Wyngaard, da ke cikin alhini, a yankin da ‘yan bindiga da tashin hankali suka yi wa jama’a kawanya.
"Sun dauke min sanyin idanuna, ba zan sake farin ciki ba har abada," in ji ta lokacin da ta fashe da kuka, tana yi min bayani kan halin da ta samu kanta a ciki tun bayan mutuwar danta shekaru bakwai da suka gabata.
‘Yan bindiga ne suka kashe Rory, mai shekara 25, ta hanyar harbinsa da bindiga a kai, a wani dare da ya ke hira da abokanshi a Mitchells Plain, a wani lamari na tsautsayi a lokacin da bai dace ba.
Ana yi wa yankin Mitchells Plain kallon unguwar bata-gari, yankin da gungun masu aikata muggan laifuka - kama daga safarar kwaya da sayar da ta, zuwa matattarar ‘yan daba - suke yawan samun hatsaniya, da ke rutsawa da wadanda ba su san hawa, ko sauka ba.

Shekaru bakwai da suka gabata aka kashe Rory, amma har yanzu ba a daina tashin hankali a yankin ba, in ji Ms Wyngaard.
Mun hadu da ita a wani karamin lambu da ke kusa da wani coci, inda ana aka yi jana’izar dan nata.
"Na san yanzu ya kubuta, yah uta da radadin da yak e ciki. Babu wanda ya isa ya cutar da shi," ta fada a lokacin da take sanya sabbin furanni a kusa da tokar gawar danta.
"Rory ya na shaida wa mahaifinsa, ba ya son wannan unguwar, saboda duk lokacin da hatsaniya ta tashi da gudu suke dawowa gida.
"Idan ana harbe-harben bindiga su yi ta kokarin kaucewa harsashi, saboda yadda gungun ‘yan daba ke yawan ta da zaune-tsaye. Babu wani abu da aka yi, kuma babu wani sauyi da aka samu unguwar nan," in ji ta.
Kamar yadda kwararu a fannin muggan laifuka suka bayyana, lamarin harbe-harben bindiga ya kara munana.
Sun ce ana kashe akalla mutane 23 da harbin bindiga a Afirka ta Kudu a kowacce rana, yayin da shekaru shida da suka gaba ake kashe mutane 18 a kowacce rana.
Me ya sa ake samun karuwar hare-haren bindiga?
Wata kwararriya Farfesa Lufuno Sadiki, na ganin cewa akwai alaka mai karfi tsakanin kasar da tashe-tashen hankula.
"Ba za mu taba kawar da ido kan abubuwan da suka faru a kasarmu ba," in ji ta, tana magana ne a kan yadda aka amince da wariyar launin fata, kafin daga bisali ala tilas aka kawo karshen hakan shekaru kusan 30 da suka gabata.
"Tsarin wariyar launin fata kan shi tashin hankali ne, da kaskanci, wanda hakan ke nufin da jami’an tsaro da al’uma su na dauke da makamai," ta yi karin bayani.
"A baya, ‘yan Afirka ta Kudu ba su da kwarin gwiwa kan jami’an tsaro, saboda hakan babu aminci tsakaninsu, don hakan yawancin farar-hula sun dauki matakin mallakar makamai."
Kwararru da dama sun amince saída makamai ba bisa ka’ida ba shi ne gagarumar matsalar.
Bincike na baya-bayan nan da cibiyar bincike kan manyan laifuka ta gano, yawancin manyan makaman da ake amfani da su an yi fasa-kwaurinsu daga wasu kasashe makwafta zuwa Afirka ta Kudu, kamar Zimbabwe, da Mozambique ta hanyar kungiyoyin ‘yan ta’adda daban-daban.
Sannan ana samun bacewar makamai daga wajen jami’an tsaro. A bara kadai an samu rahotannin fashi da makami da aka kai ofisoshin ‘yan sanda a kasar, an kuma sace daruruwan makamai.
Masu suka na cewa hukumomi sun gagara shawo kan matsalar safarar makamai.
Kuma irin wadannan makaman ne sukai ajalin Rory Wyngaarg.
"Lokacin zaman kotun mun gano an harbe shi da bindigar ‘yan sanda. Ko dai ta bata ne ko kuma an sace ta, amma tabbas da bindigar ‘yan sanda aka kasha shi," in ji Ms Wyngaard.
Hatta kotu sai da ta yi watsi da shari’ar, saboda rashin cikakken bayani daga jami’an tsaro, wanda babban tashin hankali ne da bakin ciki ga iyalan Rory.
‘Yan sanda sun kafe cewa su na kokari domin magance hare-haren ‘yan bindiga.
Sun ce sama da shekaru 10 da suka gabata, sun gano kashi 70 na bindigogin da aka sace, kuma da sun shigo hannu ake lalatasu.
Adele Kirsten wanda ta dade ta na fafutukar ganin haramta mallakar bindiga a Afirka ta Kudu, ta ce idan kasar na da wani fata na magance ko takaita amfani da bindigar, ana bukatar daukar matakai kwarara, domin rage yawan bindigar da ke yawo tsakanin al’umma.
"Muna bukatar kawar da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, dole sai an rufe ido wajen kakkabe dukkanin hanyoyin da ake samun makamai musamman bindigogin da ke kwarara kamar ruwan sama," in ji ta.
Ms Wyngaard da iyalan ta iyalanta babu wani fata da suke da shi, face ayi wad ansu adalci da ma sauran wadandasuka taba rasa wani na su.
A yanzu tana kokarin kwantarwa iyaye irin ta hankali, sakamakon ita mata samu kanta cikin halin da suke ciki.
"Ba lamari ne mai sauki ba, abubuwan na kara munana.
"Ko da yaushe ina bai wa mutane shawarar, su tausayawa halin da ka samu kan ka aciki, su dan ji abin da ka ke ji, Allah ya yi maka kyauta amma wani ya kwace, ya raba ka da farin cikin ka. An kwace maka damar da ka samu ta mallakar Da, wannna abu akia bakin ciki, da radadi a zuciya."
Ya yin da ake ci gaba da kiraye-kirayen hukumomi su auki mataki kan yawan tashe-tashen hankula da ake samu a kasar, da batun takaita mallakar bindiga.
Iyalai kamar na Rory ba za su taba mantawa da abin da ya faru da ‘yan uwansu ko ‘ya’yan da aka kasha sanadin harbin bindiga.











