‘Lokacin da za mu mutu babu wanda zai sani': Labarai daga Gaza

fg

Asalin hoton, .

Mutum hudu a Gaza sun naɗarwa BBC yadda rayuwa take kasancewa a lokacin da ake ruwan bama-bamai, suka yi bayanin yadda suke kwashe yini wajen neman abinci da ruwan sha da daddare kuma su yi ta fama da wajen fakewa daga harin sama, suna addu'ar ganin safiya ta gaba.

Tun ranar 7 ga watan Oktoba dakarun Isra'ila ke yi wa Zirin Gaza luguden bama-bamai, sun kashe Falasɗinawa sama da 10,000, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana.

Sun ce hare-haren dai na ramuwa ne kan wanda Hamas ta kai wa Isra'ila, wanda ya kashe sama da mutum 1,400 kuma aka kwashi 242 a matsayin garkuwa.

Rashin intanet da network ɗin wayar salula mai kyau yasa ba a jinhalin da ake ciki akai-akai, amma mutanen da muke da su a Gaza suna aiko mana sakonni da bidiyoyi lokacin da dama ta samu.

Gargaɗi: Akwai hotuna marasa daɗin kallo a wannan maƙala

Juma'a 13 ga watan Oktoba

Jiragen saman Isra'ila sun riƙa sako fastoci da suke bayani kan cewa mazauna yankin Arewacin Gaza su fice su koma kudanci gabanin ta fara kai mamaya, saboda "Tsaronsu da Lafiyarsu."

fg

Asalin hoton, .

FARIDA: Farida Wata malama ce 'yar shekara 26 da ke koyar da Turanci a Gaza. " Yanzu haka an lalata gidaje uku na makobtana. Dole mu bar wurin kuma ba mu da wurin zuwa," abin da ta rubuta kenan a sakonta na farko da ta aiko. " Muna nan muna jira. An nemi ƙawayena da yawa an rasa, wataƙila sun mutu. Ban san inda iyayena suke ba yanzu."

Haka ta nufi kudancin Gaza da ƙannenta da kuma yaranta ƙanana su shida.

Sun yi tafiyar ƙasa ta kimanin mako guda, sun riƙa barci a kan titi. Burinsu shi ne su isa wani wuri da ake kira Wadi Gaza, yankin da Isra'ila tace babu fargaba ga wanda yake can.

ADAM: A dai wannan rana a kudancin garin Khan Younis, Adam, wani matashi ne da ke aiki, yana ta shirin barin inda yake karo na biyar cikin kwana biyar.

"Sama da mutum miliyan guda da ke zaune a arewacin Gaza aka umarta su koma kudanci, zuwa Khan Younis," a cewarsa. " To amma shi ma Khan Younis ɗin an ci gaba da kai masa hare-hare ta sama. An kai wani kusa da gidanmu.ounis is being subjected to air strikes. There was one very close to my home."

fg

Asalin hoton, .

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An fuskanci rashin magani da abinci da man fetur bayan da Isra'ila ta sanar da yin ƙawanya da Zirin Gaza baki ɗaya hakan ya sa Amad ya gaza samun kulawar da ta dace ga dattijon mahaifinsa, wanda yake da cutar karkarwa.

Sun kasa samar masa gado ko a asibiti. A daren jiya ma a ƙasa suka yi barci a cikin asibitin.

KHALID: Mai kai magani ne da ke zaune a Jabalia a arewacin Gaza, Khalid ya ƙi barin inda aka nema tare da iyayensa, duk kuwa da sanarwar da aka ba su.

"Ina za mu je? Babu wurin tsira, babu. Mutuwa za muyi a ko wanne lokaci," cikin wani bidiyo da ya yi da aka riƙa jin tashin bam ciki, an ga Khalid yana neman ɗan uwansa da yaransa ƙanana biyu waɗanda suka tsira daga wani hari da aka kai kasuwa da ke makwabtaka da su.

Ya ƙara da cewa "An riƙa fuskantar ƙarancin magani saboda yawan waɗanda suka jikkata,". Wasu magungunan da ke so a ajiye su cikin sanyi haka duk suka lalace saboda rashin wuta. waɗanda kuma ana buƙatarsu cikin gaggawa."

Ya ce tun da aka fara yaƙin baya iya kai magunguna.

Litinin 16 ga watan Oktoba

An kai wa wata tawagar ababan hawa da ke ɗauke da fararen hula da ta nufi kudancin Salah al-Din ɗaya daga cikin inda Isra'ila ta ce a koma. Mutum 70 sun mutu mafi yawansu mata da yara, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta bayyana. Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta musanta hannu cikin harin. Ya zuwa yanzu an kashe Falasdinawa 2,785.

fg

Asalin hoton, .

Yayin da ake fuskantar hare-hare ta sama a yankin kudanci, mafi yawan Falasdinawa sun gwammace zama a gidajensu da ke arewaci. waɗanda ma suka samu mafaka a kudancin sun koma.

FARIDA: Bayan kwana a kan titi na kwanaki masu yawa, yanzu duk ta sama inda za ta sa kanta. "Ban san yadda zan bayyana abin da nake ji ba ko abin da yake faruwa yanzu," in ji ta. "An ta samun tashin bama-bamai a yankinmu duka yaran yankin sun riƙa kuka. Ba musan inda za mu ba.

"Idan ka ga dare a Gaza ba ka da tabbas ɗin za ka wayi gari. Ina zaune da iyana, sanye da hijabi. A shirye nake da duk wani hari da za a iya kowa mana."

Talata 17 ga watan Oktoba

Wani bam da ya fashe a asbitin Al-Ahli a Gaza ya kashe mutum 471. Mata da ƙananan yara da suka samu mafaka a farfajiyar asibitin suna cikin waɗanda aka kashe. Isra'ila ta ce ba ta da hannu cikin wannan hari, inda ta ce Hamas ce ta harba makamin kan asibitin bisa kusakure.

ABDELHAKIM: Watanni kaɗan gabanin fara yakin, Abdelhakim ya kammala makaranta a matsayin injinyan kwamfuta. Yana zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira na Al Bureji da ke tsakiyar Gaza. Yace bam ɗin da ya tashi ya rutsa da abokansa. Daya ya jikkata ɗayan kuma duk 'yan gidansu sun mutu.

fg

Asalin hoton, .

"Shekarata 23 kuma ya zuwa yanzu dai gani a raye," kamar yadda ya faɗa a wani bidiyon da ya yi. "ban sani ba ko za a bayyana labarina lokacin da nake raye. Harin jirgin sama zai iya kashe ni."

"Ba mu da ruwa, ba magani, ba wutar lantarki babu duk wani abin buƙatar rayuwa. A kwana uku ban ci komai ba sai wani biredi sala ɗaya da muka ci da ƙannena. Ni da iyayena cikin kwana 12 ba mu yi barcin awa 10 ba. Mun gaji. Ba za mu iya zama muhuta ba saboda fargaba."

Abdelhakim da wasu masu aikin sakai sun rika raba abinci daga gidansu. "Muna shirin raba kayan agaji da kuma barguna. Har da yara cikin masu taimakawa. Mun yanke shawarar fara hakan ne maimakon jiran motoci su shigo daga Masar," in ji shi.

Juma'a 20 ga watan Oktoba

An ruguza gidan su Abdelhakim a wani harin sama da Isra'ila ta kai kuma ya tura yadda ginin ya rushe. Akwai tashin hankali lokacin da iyalan gidansu ke neman tserewa.

ABDELHAKIM: "Muna zaune kawai sai muka ji fadowar makamin roka. Mu ka fice a guje daga gidan. Makwabtanmu har yanzu suna cikin ɓaraguzai," in ji shi. "Mun je nemansu amma ba mu samu kowa ba. Muna rayuwa ne amma a kowacce sa'a zagaye muke da mutuwa."

"Ni da 'yan gidanmu muna raye ne dai kawai a yau a matsayin wata bai wa. Sai da muka gyara wani ɓangare na gidanmu, akalla muna nan dai kafin mutuwa ta zo."

Laraba 25 ga watan Oktoba

Wani hari ya ƙara dira makwabtan su Abdelhakim, ranar da aka kashe Falasdinawa 6,972.

ABDELHAKIM: A wannan karon saƙon murya da na rubutu kawai ya iya aiko mana yana cewa: " Na gaza taimakawa, Na yi mutuwar tsaye saboda ganin gawa a koina. Babu wanda ya tsira a nan, dukkanmu shahidai ne da ke jiran lokaci.

Motar kai kayan agaji ta shiga Gaza ta maƙtarar Rafah da ke iyaka da Masar, amma kayan da aka kawo ba su isa ba, saboda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin mutum miliyan 1.4 ne ke rayuwa a yankin da suka bar gidajensu.

ADAM:Fafutukar yadda zai samawa iyayensa abinci ne kullum a ransa: "Ina farkawa da sassafe ne domin kaucewa dogon layin karɓar agaji."

KHALID: "Suna ta harba mana makamai, ba mu san yadda za mu iya fita mu karɓo biredin ba. Babu firjin ajiye abinci. Wani lokacin abincin da ya lalace muke ci, Ba mu da wani zaɓi muna ci ne domin ba mu da komai.

fg

Asalin hoton, .

FARIDA: Iyalai da dama sun yanke shawarar komawa gidanjensu da ke yankin arewaci. "Ba mu da wurin zama a kudancin. kuma ana ci gaba da kai hare-hare a inda muke. Shi ne muka yanke shawarar mu koma inda muka fito mu tsira da mutuncinmu." in ji ta

"Muna cikin farin ciki na samun matsuguni da kuma mu'amala da abokai da yan uwa, ko da ta minti biyar ne zuwa hudu a rana."

Jim kaɗan bayan komawarsu aka kai wa unguwarsu hari, kuma harin ya taba wani ɓangare na gidansu.

Juma'a 27 ga watan Oktoba

An yanke netwok ɗin waya da intanet ba ki ɗaya a Gaza, wanda hakan ya yanke sadarwa na kwana biyu, yayin da ita kuma Isra'ila ke ƙara faɗaɗa hare-harenta. Hakan ya sa mun gaza samun Khalid da Abdelhakim da Farida da Adam. Yayin da aka dawo da intanet sun ce an yi zaman duhu.

ABDELHAKIM: "An fuskanci tashin bam da yawa a daren jiya. Babu hanyoyin sadarwa babu yadda za a iya kiran motar asibiti ta ɗauki mutane, don haka dun wanda harin ya rutsa da shi sai dai ya mutu nan take.

ADAM: "Ina nan lafiya na godewa Allah. Amma lokacin da ba sadarwa mahaifina ya mutu. Allah ya jiƙansa."

FARIDA: "An kashen ƙawa an kuma rusa gidanmu," ta fada tana kuka. "An raunata ɗan uwana. tashin hankali ya taba ni."

KHALID: "Da babu intanet sai muka yi kamar mun saba, amma bayan ta dawo sai muka riƙa jin labarai. An rusa gidaje. An kashe iyalai. Yanayin ya ƙazanta. Sun yanke mu daga duniya sannan suka fara kisan kiyashi."

Litinin 30 ga watan Oktoba

Tankokin Isra'ila sun nufi Gaza, an riƙa ganinsu a titin Salah al-Din, hanyar da ake tafiya inda Isra'ila ta ce daga arewaci zuwa kudancin Gaza.

fg

Asalin hoton, .

KHALID: "Ba zan je ko ina ba yanzu. Yanzu tunanin da muke yaushe ne bam na gaba zai sauka ya kashe mu mu huta?"

FARIDA: "Ina da burin samun iyalai da abokan arziki. Ina son na yi rayuwa mai kyau. ina yawan tunani: 'Idan muka mutu babu wanda zai san mai ya faru da mu.' Dan Allah ku rubuta duka abin da na fada. Ina son gayawa duniya labarina.

ADAM: "Ina son ku faɗi duka labarin, a jiye wannan, duniya ta ji kunya na barin da ta yi wannan ya faru gare mu."

Kwararrun MDD sun yi gargaɗin lokaci na ƙurewa na hana kisan ƙare dangi a Gaza.

Cikin makonni huɗun farko na yaƙin sama da Falasɗinawa 10,000 aka kashe, kuma mafi yawansu fararen hula ne. kuma sama da 4,000 ƙananan yara ne.