Man Utd za ta zabtare albashin Ten Hag, Chelsea da PSG sun raba wa Osimhen hankali

Asalin hoton, Getty Images
Za a rage wa Erik ten Hag yawan albashinsa da kashi 25 cikin dari idan har zai ci gaba da zama a matsayin kociyan Manchester United, yayin da kungiyar ke neman rasa gurbin gasar Zakarun Turai. (ESPN)
Manchester United na son dan wasan Brentford mai kai hari Ivan Toney na Ingila, kuma kungiyar na ganin dan wasan mai shekara 28 zai taimaka mata sosai da kwarewarsa da kuma ta fannin shugabanci a tsakanin 'yan wasa. (90min)
Sai dai, Tottenham ka iya neman Toneyn idan har ba gogayya a zawarcinsa kuma kungiyar za ta gabatar da tayin fam miliyan 45 a kanshi. (GiveMeSport)
Watakila Manchester United ta rabu da 'yan wasanta har 12 a bazaran nan, wadanda suka hada da Marcus Rashford, da kuma Casemiro. (Mirror)
Makomar Mauricio Pochettino a Chelsea na zaman kila-wa-kala, kuma za ta dogara ne a kan ko zai sama wa kungiyar gurbin gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa. (Times)
Newcastle United ce kan gaba wajen damar sayen dan bayan Sporting Lisbon, Ousmane Diomande na Ivory Coast mai shekara 20, wanda yarjejeniyarsa ta tanadi sayar da shi a kan yuro miliyan 80. (A Bola)
Tottenham na da dama sosai ta sayen dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, daga Chelsea a bazaran nan, duk da sha'awarsa da Newcastle ke yi. (Football Insider)
Dan gaban Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25, na dab da kammala tattaunawar tafiya Paris Saint-Germain, amma kuma dan wasan na Najeriya na daukar hankalin Chelsea ma. (Il Mattino )
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana alakanta Arsenal da dan bayan Real Madrid Ferland Mendy, amma kuma Liverpool, da Manchester United, da Newcastle ma na son dan wasan dan Faransa. (L'Equipe )
Kociyan Aston Villa Unai Emery na matsa lamba kan kungiyar ta sayi matashin dan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, na Sifaniya mai shekara 21. (GiveMeSport)
Haka kuma Villa din na sa ido sosai a kan matashin dan wasan gaba na gefe na Leeds United Crysencio Summerville, dan Holland mai shekara 22. (Football Insider)
Tottenham ka iya bai wa Genoa damar sayen dan bayanta Djed Spence, da ta karba aro domin musaya da dan gabann kungiyar ta Italiya Albert Gudmundsson, dan Iceland mai shekara 26. (Calcio Mercato )
A shirye Arsenal take ta karbi fam miliyan 20 zuwa 25 a kan dan wasanta na tsakiya Thomas Partey, na Ghana mai shekara 30, kuma duk har yanzu tana sha'awar dan wasan tsakiya na Aston Villa Douglas Luiz, dan Brazil a matsayin wanda zai maye gurbin Partey. (Football Insider)
Feyenoord na son kociyan FC Twente, Joseph Oosting idan har Liverpool ta yi galaba a kanta ta dauke Arne Slot. (Mirror)
West Ham na tattaunawa da tsohon kociyan Sifaniya Julen Lopetegui tsawan watanni, kasancewar kociyanta na yanzu David Moyes zai kammala kwantiraginsa a watan Yuni. (Mundo Deportivo )
Newcastle na shirin sayen matashin dan bayan Chelsea Lewis Hall na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21, mai shekara 19, dindindin a bazara. (Football Insider)










