Napoli da Atletico na zawarcin Greenwood, Tuchel ya gindaya wa Bayern sharuɗɗa

Mason Greenword

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mason Greenword

Napoli na zawarcin dan wasa mai kai hari na Ingila Mason Greenwood, wanda aka ba da shi aro ga Getafe daga Manchester United, sai dai watakila ta fuskanci gogaya daga Juventus idan suna son su dauko dan wasan dan shekara 22 . (Corriere dello Sport - in Italian)

Ita ma Atletico Madrid ta na son ta dauko Greenwood din. (Star)

Kociyan Bayern Munich Thomas Tuchel na son kungiyar ta ba shi tabbacin cewa za ta dauko ‘dan wasan tsakiya kuma mai kwazo a bazara kafin ya sake shawara a kan ko zai ci gaba da aiki da kungiyar ta Bundesliga har bayan kakar wasanni kuma ana ganin hankalin kungiyar na kan dan wasan Manchester United Bruno Fernandes mai shekara 29. (Independent)

Real Madrid ta sauya shawara wajan sayan dan wasan baya ta gefen hagu na kasar Kanada Alphonso Davies dan shekara 23 wanda kwantaraginsa da Bayern Munich zai zo karshe a bazarar 2025. (COPE - in Spanish)

Napoli na nazari kan dan wasa mai kai hari na Atletico Madrid Samu Omorodion, dan shekara 20 wanda aka ba da shi aro ga Alaves a wannan kaka a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasa mai kai hari na Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 25. (Sky Sports Italy)

Kociyan Chelsea Mauricio Pochettino ya samu goyon bayan wasu jiga-jigan kungiyar gabanin nazarin karshen kakar wasani da zai tantance makomarsa a Stamford Bridge. (Guardian)

Dan wasan tsakiya Chelsea da Ingila Conor Gallagher mai shekara 24 ba ya son ya koma Newcastle United, wadanda suka dade suna zawarcinsa a wannan bazara. (Football Insider)

Real Madrid na shirin baiwa Espanyol Yuro miliyan 1.5 domin dan wasai mai kai hari na Sfaniya Joselu mai shekara 34 da aka ba ta shi aro ya ci gaba da taka mata leda kafin ta yanke shawara a kan ko za ta sayi shi a bazara (Sport - in Spanish)

Dan wasan tsakiya na Aston Villa da Brazil Philippe Coutinho mai shekara 31 , wanda a halin yanzu an bada shi aro ga Al-Duhail SC ta Qatar, watakila ya sake komawa tsohuwar kungiyarsa ta Vasco da Gama(TNT Sports Brazil, via Mail)

Juventus na nazari akan ko ta kori kociyanta Massimiliano Allegri, duk da cewa a karon farko a cikin shekaru uku sun ci kofin Coppa Italia a ranar Laraba (Sky Italia - in Italian)

Juve ta yi wa kociyan Bologna Thiago Motta tayin yarjejeniyar shekara uku domin maye gurbin Allegri a matsayin sabon kociyanta. (Fabrizio Romano)