Man United na son Fernandes ya ci gaba da zama a ƙungiyar - Ten Hag

Asalin hoton, Reuters
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ungiyar na da niyyar cigaba da aiki da ɗan wasan tsakiyarta Bruno Fernandes bayan ya nuna yana son cigabada zama a kulbo ɗin.
An san cewa United ta buɗe ƙofar sayar da dukkan 'yan wasanta, ban da masu ƙananan shekaru kamar Alejandro Garnacho, da Kobbie Mainoo da Rasmus Hojlund saboda suna son sake gina ƙungiyar.
Fernandes na cikin wannan jerin kuma ma har ana alƙanta shi da komawa Inter Milan da Bayer Munich a 'yan kwanakin nan, duk da cewa ba ƙaramin tayi ne zai sa United ta rabu da shi ba.
Yayin wata hira da Sky Sports bayan kammala wasan Newcastle ranar Laraba, Fernandes ya bayyana jajircewarsa a kulob ɗin.
"Zan ci gaba da zama idan kulob ɗin yana buƙatata," in ji shi. "Idan kuma wani dalili ya sa ba su buƙatata zan tafi."
Har yanzu Fernandes na da sauran shekara biyu a kwantaraginsa da ya saka hannu a 2022. Yarjejeniyar na da tanadin ƙarin shekara ɗaya.
Da aka faɗa masa abin da kyaftin ɗin nasa ya ce, Ten Hag ya ba da amsa da cewa: "Tabbas kulob ɗin na son ya ci gaba da zama."






