Ba na jin tsoron Tinubu – Atiku

Asalin hoton, TWITTER
Ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP Atiku Abubukar ya ce bai kwana da shakkar babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
A lokacin tattaunawarsa da BBC Hausa, Atiku Abubakar ya ce bai taɓa jin tsoron fafatawa da wani ɗan siyasa a ƙasar ba.
Atiku Abubakar ya kuma ce sauran manyan 'yan takarar shugabancin ƙasar biyu na jam'iyyun NNPP da LP ba sa tayar masa da hankali domin a halin yanzu ma suna kan tattaunawa da su domin yiyuwar haɗa kai a zaɓen da ke tafen.
'Abu biyar da zan mayar da hankali a kai'
Ɗan takarar shugabancin ƙasar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya kuma ce akwai abubuwa biyar da zai maya da hankali a kai da zarar ya samu damar ɗarewa kujerar shugabancin ƙasar.
Wadanda suka haɗa da batun rashin tsaro, da rashin haɗin kai tsakanin 'yan ƙasar, da batun tattalin arziki, da ilimi da lafiya.
Inganta tsaro
Da aka tambayi ɗan takarar yadda zai magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta musamman ɓullowar matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a yankin arewa maso yamma,
sai ya ce zai ƙara yawan jami'an tsaron da ake da su, tare da ba su horo a kai-a kai, tare da samar musu da na'urorin tsaro na zamani.
Sannan kuma ya ce zai amince da samar da jami'an tsaro na jihohi, amma bisa sharaɗin cewar gwamnoni ba za su yi amfani da su ba wajen muzguna wa abokan adawa.
Tattalin arziki
Atiku Abubakar ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ta hanyar gayyato 'yan kasuwa daga ƙasashen waje domin su zo su zuba jari don haɓaka tattalin arziƙin ƙasar.
''Sannan za mu tattauna da waɗanda ke bin Najeriya bashi domin sake duba hanyoyin da za a bi wajen biyan basussukan da ake bin Najeriyar'', in ji Atiku.
Inganta Ilimi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangane da batun inganta ilimi a ƙasar tsohon shugaban Najeriyar ya ce a yanzu kimanin yara miliyan 12 ne ba sa zuwa makaranta a arewacin Najeriya.
A cewarsa ''waɗannan alƙaluma sun nuna cewa jihohi da ƙananan hukumomi ba sa amfani da kuɗaɗen da suke samu daga gwamnatin tarayya yadda ya kamata wajen haɓaka harkar ilimi a matakin farko''.
Kan batun ASUU Atiku ya ce zai zauna da ƙungiyar Malaman Jami'o'in ƙasar kamar yadda yake tattaunawa da malaman da ke koyarwa a jami'arsa.
''A matsayina na mamallakin jami'a fiye da shekara 20 nakan zauna da malaman jami'ar domin tattaunawa a duk lokacin da wani abu ya taso, haka zan zauna da malaman jami'o'in ƙasar domin magance matsalarsu'' in ji shi.
Sannan kuma ya ce zai farfaɗo da ma'aikatar bayar da rance ta gawamnati domin tallafa wa ɗaliban da ba su da ƙarfin biyan kuɗin makaranta da bashin kuɗi.
''Idan sun gama jami'ar su biya gwamnati bashin da ta ba su kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya''.
Lafiya
Kan batun matsalar likitocin Najeriya da ke barin ƙasar zuwa ƙasashen ƙetare domin neman aiki, ɗan takarar shugabancin ƙasar ya ce ''kamar yadda muka zo a shekarar 1999 mun fuskanci irin wannan matsala inda mafi yawan likitocin Najeriya suka riƙa tafiya ƙasar Saudiyya domin neman aiki, amma muka zauna da su muka gyara musu albashi muka ainganta musu ayyukansu domin su dawo''.
Dan haka a cewarsa zai gyara asibitocin ƙasar, tare da inganta albashin likitocin domin su dawo aiki a cikin ƙasar.
Gwamnonin G-5
Kan batun ƙungiyar gwamnonin PDP ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da ke takun-saƙa da ɗan takarar shugaban ƙasar, Atiku ya ce suna tattaunawa da su.
''Kuma da yawa daga cikinsu ba sa nan, ba sa can, dan haka mun tabbata ba za su kawo mana wata matsala ba''.
ya ƙara da cewa ''Mun yadda da tsarin gudanar da zaɓen bana da Hukumar Zaɓen Kasa ta INEC ta shirya gudanarwa a bana, domin kuwa zaɓen bana ba kamar sauran da suka gabata ba ne, inda gwamna zai ce sai wane za a zaɓa''.
''A bana za a yi amfani da na'urorin fasaha na zamani domin gunadar da zaɓen bana'' in ji Atiku.
Rufe kan iyakokin ƙasa
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce batun rufe kan iyaka da Najeriya ta yi baya kan tsarin doka, domin kuwa a cewarsa Najeriya tana cikin ƙungiyar ECOWAS, kuma a cikin dokokin ƙungiyar, akwai batun cewa tafiye-tafiyen jama'a da kuma harkokin kasuwanci babu wani shinge, amma wannan gwamnatin da ta zo sai ta rufe.
Abu na biyu shi ne doka ta amince da mutanen da ke garuruwan da ke kusa da kan iyaka su je cin kasuwannin da ke kusa da kan iyaka (misali ƙaukan Sokoto da ke kusa da kan iyaka da Nijar za su iya zuwa cin kasuwannin Nijar da ke kusa da garuruwansu ba tare da shinge ba).
''Wannan matsala ta shafi kusan duka jihohin arewacin Najeriya da ke kusa da kan iyaka da sauran ƙasashe''
A cewarsa wannan shi ya sa mutanen ƙasar da dama suka shiga ayyukan ta'addanci.











