MDD ta ce miliyoyin 'yan Sudan na fuskantar yunwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, By Jeremy Howell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Miliyoyin 'yan Sudan na fuskantar barazanar yunwa saboda yaƙin da aka shafe sama da shekara ɗaya ana yi, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Rikicin tsakanin dakarun sojan Sudan da na gamayyar ƙungiyar tawaye ta RSF ya tilasta wa mutuum miliyan tara guduwa daga gidajensu, abin da hakan ke nufin akwai masu yawa da ke fama da yunwa "mai tsanani".
Ana siffanta faɗan na Sudan a matsayin "yaƙin da aka manta da shi", saboda yadda yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza da kuma na Rasha da Ukraine suka fi jan hankalin duniya.
Sai dai kuma, ƙungiyoyin ba da agaji na gargaɗin zai iya haifar da mummunan bala'in yunwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ahmed mazaunin Omdurman ne - wani gari da ke gefen Khartoum babban birnin ƙasar - kuma ya siffanta wa BBC irin wahala da ƙarancin abinci da ake fama da shi a Sudan.
Ya ce farashin kayan abinci da aka fi ci sun ninka sau huɗu a Omdurman da Khartoum, inda 'yan tawayen ske iko da su.
"Duka abincin da ake shigo da shi daga ɓangaren sojojin Sudan na da matuƙar tsada," in ji shi.
"Akasarin mutanen da ba su gudu daga gidajensu ba na ci abinci sau ɗaya a rana.
"Ɗaruruwan mutane kan hau layi tun daga farar safiya a kusa da inda nake muku magana yanzu, inda suke jira a ba su lantils a matsayin abincin safe. Wasu kan ƙara ruwa a kan lentils ɗin saboda su ajiye wanda za su iya ci da dare.
"Mutane na ƙara dogara da abincin da ake girkawa a kullum a duka ɓangarorin da RSF ko gwamnati ko iko da su. Layukan na ƙara tsayi a kowace rana. Ana ƙara buɗe wuraren raba abincin amma kuma ingancin abincin na raguwa."

Asalin hoton, Getty Images
Yaya ƙamarin ƙarancin abincin yake?
Kusan mutum miliyan 18 cikin 49 na al'ummar Sudan ne ke fuskantar "barazana mai girma ta ƙarancin abinci", a cewar (OCHA).
'Dubun dubata na mutuwa'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar Justin Brady, wanda shi ne shugaban ofishin OCHA a Sudan, akwai mutum miliyan 4.9 da ke cikin matsanancin ƙarancin abinci, kuma shi ne mataki na ƙarshe kafin shiga annobar yunwa.
"Babu tantama akwai yiwuwar dubbai ko dubun dubatar 'yan Sudan za su mutu a watanni masu zuwa," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
"Rashin ɗaukar cikakkun matakai zai iya haddasa matsalar ta zama mafi muni a tsawon shekaru a duniya baki ɗaya, kuma ya ta'azzara yawan mutanen da aka kora daga gidajensu," in ji Anette Hoffmann na Clingendael, wata cibiya da ke ƙasar Netherlands.
A wasu yankunan na Khartoum, mutane kan tsinki ganyayyaki daga jikin bishiya su ci.
Sarrafa abincin gwangwani ya ragu da kashi 40 cikin 100 a Sudan daga 2022 zuwa 2023, a cewar hukumar abinci ta MDD.
Akwai fargabar yunwa za ta ƙaru a watanni masu zuwa kafin saukar damina.
Hatta a lokacin ba lallai ne a samu abinci da yawa ba, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Manoma masu ko dai sun gudu sun bar gonakinsu, ko 'yan tawaye sun ƙwace su, ko kuma sun cinye shukokin saboda yunwa.

Asalin hoton, Getty Images
Ba wai ƙaranci kawai abinci ya yi ba, miliyoyin mutane ba za su iya saya ba ko da akwai shi.
Rabin al'ummar ƙasar ba su da aikin yi, a cewar hukumar ba da lamuni ta duniya IMF. Tsarin ajiyar kuɗi a banki ya lalace a Sudan ta yadda ba a iya cire kuɗi daga bankunan. Abu ne mawuyaci a iya tura wa mutum kuɗi ta intanet.
Kamfanin Humanitarian Outcomes ya ce kashi ɗaya cikin biyar na 'yan Sudan ne ke samun tallafin abincin da suke buƙata.
Me ƙungiyoyin agaji za su iya yi?
Ƙungiyoyin agaji sun ce za a iya ɗaukar makwanni kafin su samu izinin da za su iya shiga da dukkan tallafin da suke so su bayar a yankin Darfur - daga 'yan tawayen RSF da sauran mayaƙa.
Sojojin Sudan sun ce RSF ne ke tarewa da sace kayan agajin, amma ƙungiyar ta musanta zargin.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnati ta ce ta mayar da hankali wajen ba da damar kai kayan agajin. Amma ƙungiyoyin agaji sun ce an saka wasu dokokin da ke kawo tarnaƙi.
'Yara na cin ƙasa'
Wuraren da lamarin ya fi shafa a Sudan su ne sansanonin 'yan gudun hijira kamar ZamZam da ke arewacin Darfur, inda mutum kusan 500,000 ke fakewa.
Ƙungiyar agajin likitoci ta Doctors Without Borders ta ce kusan kashi ɗaya cikin uku na yaran da ke sansanin masu shekara ƙasa da biyar na fama da yunwa sosai.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa akwai yaran da ke cin ƙasa saboda yunwa.







