Masarautu 10 mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya

Asalin hoton, forbes
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
Babu shakka duniya ta tara hamshakan masu arziki, sai dai kuma akwai wasu rukunin mutane ko zuri'a da arzikinsu abin jinjinawa ne, hakazalika karfin ikonsu da faɗa aji a duniya.
Daga tsarin mulki irin na soja zuwa tsari na dimokraɗiya har zuwa masarautu.
Amma fa akwai wani abu guda da kusan za a iya cewa na da kamanceceniya ga duk mutumin da ke burin iko, wato karfin mulki da tattalin arziki.
Daukar hankalin duniya da Qatar ta yi a karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na 2022 na irin dumbin arzikinta, ya sa mutane a fadin duniya na mararin son jin labarin arzikin sauran kasashe masu tsarin masarauta kamar ta.
A wannan maƙala za mu duba wasu hamshakan mutane ko masarautu 10 da ke da ƙarfin faɗa a ji kuma mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya.
Waɗannan mutane iyalai ne na gidan sarautun da ke da ƙarfin faɗa a ji a duniya.
BBC ta duba karfin tattalin arzikinsu da kuma daga inda suke samun kuɗaɗensu, bisa bincike da bayanai da muka tattaro daga mujallar Forbes da Economic Times da kuma ƙididdigar tattalin arziki ta duniya.
1. Masarautar Saudiyya - mai karfin tattalin arzikin dala tiriliyan 1.4

Asalin hoton, Getty Images
Masarautar Saudiyya ita ce ta ɗaya mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Iyalan gidan sarautar sanannu ne a kowace kusurwa ta duniya, kuma arzikinsu ba ɓoyayyun abu ba ne.
Masarautar zuri'ar 'Saud' kamar yada ake kiranta, ta ba da tazara sosai in dai aka zo batun tattalin arzikinta a duniya.
Zuri'ar ke mulkar ƙasar ta Musulunci, kuma hoton sarkinsu na farko ne tambarin kuɗin da ake kashewa a ƙasar wato 'Riyal' tun 1744.
Masarautar a yanzu na hannun Sarki Salman Bin Abdul'aziz, wanda ake cewa ya fi kowa a zuri'arsu arziki.
Mujallar Forbes ta kiyasta cewa karfin tattalin arzikin masarautarsa ya kai dala tiriliyan ɗaya da miliyan hudu ($1.4 tiriliyan).
Tattalin arzikin Saudiyya ya dogara kacokan kan ɗanyen man fetur da suke fitarwa.
Ita ce ƙasa ta biyu mafi arzikin fitar da mai a ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.
Saudiyya ke fitar da kashi 18 cikin 100 na ɗanyen mai a duniya, hakan ya sa ake daraja ƙasar sosai a kasuwannin duniya.
2. Masarautar Kuwait - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 360

Asalin hoton, Getty Images
Zuri'ar Al Sabah ce ke mulkar ƙasar Kuwait. Karkashin mulkin Sarki na yanzu Sabah IV Ahmad Al-Jaber Al-Sabah.
Zuri'ar Al Sabah ke mulkin Kuwait tun 1752, kuma ta kasance ta biyu a duniya cikin masarautu mafiya karfin tattalin arziki.
Karfin tallalin arzikin iyalan ya kai dala biliyan 360 ($360 biliyan) inda kusan suke da tarin hanayen jari a kowanne kamfanin na faɗa a ji a Amurka.
Ƙasar mai yawan al'umma miliyan uku da rabi ita ce kuma ta biyu mafi karfin tattalin arziki a ƙasashen Musulunci a duniya.
Kuwait na da ɗanyen mai ganga miliyan 104 jibge a kasa, wanda kusan ta mallaki kashi 10 cikin 100 na man duniya.
Ana hasashen cewa a wannan shekara ta 2022 man da take haƙowa zai karu da ganga miliyan hudu.
Sauran kadarorin da masarautar ta mallaka sun haɗa da manyan jiragen ruwan alfarma da na dakon kaya, akwai gine-gine da harkokin kuɗaɗe.
3. Masarautar Qatar - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 335

Asalin hoton, Getty Images
Qatar ce daula ta uku mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Suna kiran masarautar ƙasar da Gidan Thani, wanda Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ke mulka a yanzu bayan hawa mulki a 2013.
Zuri'arsu ke mulkar Qatar tun tsakiyar karni na 19.
Tattalin arzikin masarautar ya kai dala biliyan 335 a 2022, sun kuma gina kansu ne daga ayyuka daban-daban kamar zuba hannu jari a fanin gine-gine.
A ciki akwi irin su dogon ginin alfarma na London Shard, da katafaren yankin da aka taɓa yin wasannin Olympics da ake kira 'UK capital Olympic village', da yankin rukunin shagunan alfarma na Harrods.
Iyalan na kuma da hannun jari mai karfi a kasaitaccen dogon ginin nan na 'New York Empire' da bankin Barclays da kamfanin jirgin Burtaniya na 'British Airways' da kuma kamfanin ƙera motoci na Volkswagen.

Asalin hoton, Getty Images
Shekaru aru-aru baya, a 1922 Qatar 'yar karamar kasa ce a yankin Gulf da girman ƙasar bai zarta kilomita dubu 12 ba.
Tana da yawan al'umma miliyan uku wanda akasarinsu makiyaya ne da suka yada zango a ƙasar bayan fitowa daga wasu yankunan Larabawa.
Sai dai a yau, Qatar na ɗaya daga cikin kasa mafi karfin tattalin arziki na duniya, godiya ga amfani da damarsu ta arzikin mai da iskar gas.
A 1970, yawan al'ummar ƙasar ya ƙaru daga kasa da dubu 25 zuwa mutum dubu 100, inda ma'aunin tattalin arzikinsu ya zarta dala miliyan 300.
A wannan lokacin ne ƙasar ta samu cikakken ƴanci, bayan kasancewa karkashin mulkin Burtaniya tun 1916.
Yanzu haka Qatar na da ɗanyen mai jibge a ƙasar da ya haura gangan miliyan 25, kuma ita ce ta 13 da ke wannan mataki a duniya.
Wannan na daga cikin dalilan da suka sa ƙasar ba ta ji ko ƙyashin kashe kuɗi, kamar yadda aka gani wajen shirya gasar cin kofin duniya na 2022.
4. Masarautar Abu Dhabi - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 150

Asalin hoton, @mohamedbinzayed/Instagram
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk inda aka jiyo Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, abin da ke zuwa zuƙatan mutane ko tunani shi ne rayuwar jin daɗi ta alfarma da ƙasaita.
Sai dai ƙasar ta wuce batun yawon buɗe ido da shakatawa da tsarin rayuwar alfarma.
Kasa ce da ke fitar da mai da gas da ke taka gagarumar rawa wajen tattalin arzikinta, musamman a Abu Dhabi.
Hada-hada ta manyan gine-gine da faɗaɗa ayyukan kamfanoni na taimakaw a ƙasar wajen buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga.
Zuri'ar Al Nahyan ita ke mulkin Abu Dhabi.
Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ke mulkin masarautar Abu Dhabi kuma shi ne shugaban ƙasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa tun 2004.
Sarkin ke kuma jagorantar majalisar nazarin zuba jari da ke kula da kadarorin da suka zarta dala biliyan 696 ($696 billion).
Masarautar da ke ta haɗu a karfin tattalin arziki a duniya an kiyasta cewa ta mallaki kuɗaɗen da yawansu ya kai dala biliyan 150.
Kaso mafi yawa na wannan kuɗaɗe an same su ne daga fannin mai, sannan sarkin na ɗaya daga cikin waɗanda suka fi yawan gidajen haya a Landan da yawan gine-gine da kuɗaɗensu suka zarta dala biliyan bakwai da miliyan 100 ($7.1 biliyan).
Abin mamaki ko!..
5. Masarautar Burtaniya - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 88

Asalin hoton, AFP
Masarautar Burtaniya da Sarki Charles III ke mulka a yanzu, ba su ba ne mafi karfin tattalin arziki a cikin masarautun duniya ba, sai dai suna da karfin faɗa a ji da tasiri sosai a duniya.
A cewar mujallar Forbes, tattalin arzikin masarautar ya kai dala biliyan 88, wannan ya sa suke mataki na biyar a duniya a jerin masarautu masu arziki.
Galibin dukiyar wannan masarauta ya fito ne daga rukunin gine-gine na crown estate da zuba jari a harkokin gine-gine da dama.
Sai dai marigayiya Queen Elizabeth ita ce mafi tarin arziki a zuri'ar masarautar inda kadarorin da ta mallaka ita kaɗai suka kai dala biliyan 428 da miliyan uku ($428.3 biliyan).
6. Masarautar Thailand - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 30-60

Asalin hoton, Getty Images
Zuri'ar Chakri ita ce masarauta da ke mulki a Thailand, kuma ta shida mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Wannan zuri'a ke tafiyar da harkokin wannan masarauta tun kafata a 1782.
Sarki na yanzu sunansa Maha Vajiralongkorn wanda ya hau mulki a 2016 bayan mutuwar mahaifinsa, Sarki Bhumibol Adulyadej.
Duk da cewa akwai kokonta kan yawan arzikin wannan zuri'a, mujallar Forbes ta kiyasta cewa arzikin masarautar ya kai dala biliyan 30 zuwa dala biliyan 60 a shekara ta 2022.
7. Masarautar Brunei - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 28

Asalin hoton, Getty Images
Burnei ƙasar Musulunci ta uku mafi karfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Musulmi, kuma ta bakwai a jeren masarautu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.
Burnei ta samu haɓɓaka sosai saboda karfin arzikinta na fetur da iskar gas.
Kusan fetur da gas ne suka mamaye komai na tattalin arzikin ƙasar sama da shekaru 80 yanzu, sannan wannan hanya ko fitar da ɗanyen mai ke sama mata kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta ko ma'auninta na tattalin arziki.
Sarki Hassanal Bolkiah ke mulkin ƙasar da ke bin tsarin mulki na masarauta.
Sarkin na rayuwa a fadar da ta kasance irinta mafi girma da alfarma a duniya, fadar da har a kundin bajinta na Guinness an yi maganarta.
Zuri'ar Masarautar Burnei sun tara akasarin dukiyarsu, ko mu ce baki ɗaya dala biliyan 28 na tattalin arzikinsu na ɗanyen mai.
Sarkin ya mallaki jiragen alfarma da dama da dubban motocin ƙasaita irinsu Rolls Royce 600 da Ferarri 300.
Abin tu'ajjubi ko?..
8. Masarautar Dubai – mai karfin tattalin arzikin - dala biliyan 18

Asalin hoton, Getty Images
Masarauta ta takwas mafi karfin tattalin arziki a duniya, ita ce masarautar Sarkin Dubai da Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum ke mulka.
Shi ne babba a zuri'ar iyalan da ke mulkin Dubai, kuma mutum mafi arziki a masarautar Al Maktoum.
Kuma a yanzu sarkin shi ne mataimakin shugaban kasa kuma firaministan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Zuri'ar da ya fito sun shafe tsawon shekaru wajen gina masarautar da miliyoyin daloli.
Wannan zuri'a ta samu kuɗaɗenta ne ta hanyoyin zuba jari, ciki har da rukunin kamfani na Dubai Holdings, da gidan gonar Darley Stud mafi girma a duniya wajen harkokin dawakai.
Baya ga waɗannan kasuwanci, iyalan masarautar sun mallaki kadarorin alfarma a ko ina a faɗin duniya.
9. Masarautar Moroko – mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 8.2

Asalin hoton, Getty Images
Masarautar Alaouite ita ce ta zuri'ar da ke mulkin Moroko. Sarki Mohammed VI, ke mulkar masarautar tun 1999.
Zuri'ar Alaouite ta kasance ta tara mafiya karfin tattalin arziki cikin masarautun duniya.
Sun mallaki dukiyoyi sakamakon zuba jarin biliyoyin daloli a fanni daban-daban na rayuwa.
Mujallar Forbes ta ce a 2022 karfin tattalin arzikin iyalan masarautar ya kai dala biliyan takwas da miliyan biyu, ($8.2 billion0.
Wannan arziki shi ma ya kai ya kawo...
10. Masarautar Liechtenstein - mai karfin tattalin arzikin dala biliyan 4.4

Asalin hoton, Liechtenstein Royal Family
Masarauta ta goma mafi karfin tattalin arziki a duniya ita ce ta Liechtenstein da Yarima Hans-Adam II ke mulka.
Iyalan masarautar ke mulkar Liechtenstein ta tsarin mulki na masarautu, kuma idan ana maganar karfin arzikinsu, dukiyar da wannan masarauta suka tara ya wuce tunani, don haka ba abin mamaki ba ne kasancewarsu ta 10 a duniya.
A wannan lokaci da muke cikin shekara ta 2022, arzikin iyalan wannan masarauta ya kai dala biliyan huɗu da miliyan 400, ($4.4 biliyan).
Iyalan dai sun tara dukiyarsu ce ta hanyoyi daban-daban kama daga zuba jari a fannonin gine-gine da kuma zane.











