Yariman Saudiyya da ya shafe shekara 20 cikin dogon suma ya rasu

Asalin hoton, Social Media
Masarautar Saudiyya ta sanar da rasuwar Yarima Alwaleed bin Khalid bin Talal, wanda aka fi sani da “Yarima mai bacci”.
Yariman ya rasu ne ranar Asabar yana da shekara 35 a duniya, bayan ya kwashe shekara 20 cikin dogon suma.
Mahaifin yariman, Khalid bin Walid ya wallafa wani bayani a shafinsa na X, inda ya yi addu’ar Allah ya ji kan dan nasa.
”Kasancewar zuciyoyinmu sun yi imani da duk abin da Allah ya hukunta, amma a cikin a cikin alhini, muna jimamin danmu, abin kaunar mu Yarima Alwaleed bin Khalid bin Talal bin Abdulaziz Al Saud, Allah ji kan shi, ya koma ga Allah madaukaki a yau,” kamar yadda bayanin ya nuna.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Social Media
An haifi Yarima Waleed bin Khalid ne a shekarar 1990, sai dai ya samu wani mummunan hatsarin mota a shekarar 2005 lokacin da yake karatu kwalejin horas da sojoji.
Lamarin ya haifar da zubar jini a cikin kokon kansa, wanda hakan ya sa ya shiga cikin dogon suma na tsawon shekara 20.
A tsawon wadannan shekaru Yariman ya kasance yana rayuwa ne tare da tallafin na’urori da kulawar likitoci.
Lalurar da yariman ya samu ta ja hankalin al’umma da dama a kasar ta Saudiyya, inda duk wani motsi da ya yi yake zama labari a fadin kasar.
A shekara ta 2019 labarin motsawar kansa da kafadarsa ta hagu sun ja hankalin al’umma, sai dai duk da haka ya ci gaba da kasancewa cikin dogon suma.
Haka nan a farkon wannan shekarar an yi ta yada jita-jitar farkawarsa, to amma masarautar Saudiyya ta musanta hakan, har zuwa yanzu da aka bayar da sanarwar rasuwarsa.
A tsawon lokacin da ya kwashe yana cikin dogon suma yariman ya samu kyakkyawar kulawa daga masarautar ta Saudiyya, inda iyalansa suka dage kan cewa sai an ci gaba da yi masa magani.
Mahaifinsa Yarima Khalid ya bukaci da kada a cire abubuwan da ke taimaka masa wurin cigaba da rayuwa, inda ya bayyana cewa rayuwa da mutuwa a hannun Allah suke.











