Waɗanda ke zargin 'an kashe ƴaƴansu' lokacin zanga-zanga sun nemi ɗaukin hukumomi

.
Lokacin karatu: Minti 4

Iyayen yaran da suka yi zargin an halaka a yayin zanga zangar tsadar rayuwa a Najeriya, musamman a yankin arewacin ƙasar - a watan Agustan 2024 - sun buƙaci gwamnati da ta yi musu adalci, tare da biyan su diyyar yaran da suka rasa.

Iyayen na zargin cewa an kashe ƴaƴansu ne a wasu daga cikin jihohin arewacin kasar, amma har kawo yanzu, babu wani abu da gwamnatin Najeriyar ta yi kan haka, illa jiyo jami'an tsaron ƙasar na musanta cewa suna da hannu a kashe-kashen da suka faru a jihohi da dama.

A tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024 ne al'umma, musamman matasa suka fantsama a kan titunan Najeriya domin nuna fushi kan halin tsadar rayuwa a ƙasar.

Sai dai jim kaɗan bayan fara zanga-zangar ne lamarin ya rikiɗe zuwa tarzoma a wasu jihohin ƙasar.

Rahotanni, da kuma bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun yi sanadin mutuwar masu zanga-zanga lokacin da suka yi amfani da ƙarfi fiye da kima wajen murƙushe tarzomar.

Sai dai hukumomi sun musanta zarge-zargen.

Iyayen yaran da suka 'rasa rayukans musamman waɗanda suka fito daga jihohi irin su Kano, da Jigawa, da Borno sun bayyana cewa har yanzu - watanni biyar - bayan ikirarin da suka yi wa jami'an na kisan 'ya'yansu, babu wani mataki da hukumomi suka dauka.

Ɗaya daga cikin iyayen da ke kokawa daga jihar Kano, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta shiga lamarin don ganin an yi musu adalci.

"Ai gwamantin ba ta yarda mutanenta sun yi laifi ba, ai wanda ya yarda ya yi laifi, da shi kake magana, amma wanda bai yarda ya yi laifi ba, babu wani abu da za a iya yi.

"Jami'na ƴansanda muke zargi, akwai wanda a kan layi ga su nan suna haurowa suna harbe-harbe kan mai tsautsayi, babu kokwanto a ciki, akwai bidiyon wani ɗansanda da yi harbe-harben ma a unguwarmu" in ji shi.

Shi ma wani mahaifin a jihar Jigawa, wanda ya zargi jami'an tsaro ne da harbe ɗan yayansa, ya tabbatar da cewa yana da shaida, kan zargin nasa.

"Lokacin da abun ya faru babu wani a gwamnatance, da ya zo ya jajanta ko ya yi mana gaisuwa, kan abun da ya same mu, ya tsaya mana a rai; sannan abin takaicin shi ne mun ji ana musatan cewar babu wanda aka haraba, kamar ma ƙage ake yi musu ko wani abu, mu kuma muna da shida a hannunmu, ga takardar da likita ta rubuta mana, ta shaidar yaron ya mutu, amma duk da haka wai ake musanta halaka wani," in ji shi.

Haka ma dai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, wani mahaifi ne ya nemi gwamnatin ta Najeriya da ta bi kadin abin da ya faru "don a yi adalci" kan zargin da suke yi wa jami'an tsaro da harba wa ƴaƴansa biyu gurneti, "abin da ya yi ajalinsu".

"Gaskiya abin ya ɗaga min hankali, yarona shekarunsa 24, ga ɗan yayata mai shekaru 29, da abokinsu wanda shekarunsa ba su fi 26 ba, idan na tuno yadda suka rasa ransu hakan, na matukar tayar min da hankali, sannan ya dugunzuma ya tashi.

"Babban abin baƙin ciki shi ne yadda na ji ƴansanda na musanta cewar wai ba su ne suka aikata ba, ina shiga cikin matsaananciyar damuwa", a cewar sa.

Haka kuma ya ce a 'duk lokacin da suka shiga matsi, sai su tuno da yaran, don su ne ke taimaka musu, "hankalinmu sai ya tashi". Don haka gwamnati ta taimaka mana, sannan ta biya mu diyya' in ji shi.

'Ba su so su saurare mu'

Masu koken sun bayyana cewa duk wani ƙoƙarin da suka yi domin tattaunawa da rundunar ƴansanda a Najeriyar abin ya ci tura.

A baya-bayan nan ma rundunar ƴansandar ta Najeriya ta buƙaci ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty Intertional da ta fito ta janye zargin da ta yi kan cewa "jami'an tsaro sun kashe sama da mutum 20", tare da ikirarin cewa za su je kotu idan hakan ba ta faru ba.

A gefe guda dai jim kadan bayan lafawar zanga-zangar a wani jawabi da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi, ya yi alkawarin cewar gwamnatisa za ta bincika kuma duk wanda ta samu da hannu za a hukunta shi.

Sai dai babu tabbas ko an gudanar da wannan bincike.