Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na son maye gurbin Slot da Alonso, Arsenal za ta saye Hincapie
Aikin Arne Slot na kociyan Liverpool na cikin yanayi na rashin tabbas zuwa karshen kakarnan, inda masu kungiyar suka ce ba wanda suke so ya maye gurbin dan Holland din illa tsohon kociyan Real Madrid, Xabi Alonso. (Teamtalk).
Arsenal za ta sayi dan bayan Ecuador Piero Hincapie, mai shekara 24, dindindin daga Bayer Leverkusen a karshen kakar nan. (Sun).
Sai dai kuma Gunners na bukatar sayar da wani daga cikin manyan 'yan wasanta a bazaran nan, inda ake ganin dan wasanta na tsakiya Martin Odegaard, dan Norway mai shekara 27, da kuma Gabriel Martinelli, dan Brazil mai shekara 24, ke cikin wadanda za ta iya rabuwa da su. (Telegraph).
Manchester City na dab da kammala yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiya na Ingila Elliot Anderson daga Nottingham Forest. (Teamtalk).
Nottingham ta yi wa Anderson mai shekara 23, wanda ya fi son tafiya City a kan abokan hamayya Manchester United, farashin sama da fam miliyan 70. (Talksport)
Arsenal, da Manchester United da kuma Chelsea, na shirin gogayya wajen sayen matashin dan wasan baya na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 19, Samuel Amissah, mai shekara 18, daga Fulham. (Telegraph).
Liverpool na son sayen Yan Diomande, mai shekara 19, domin maye gurbin Mohamed Salah, to amma kuma kungiyarsa ta RB Leipzig ta sanya masa farashin fam miliyan 87. (Teamtalk).
Tsohon kociyan Tottenham Mauricio Pochettino da Roberto de Zerbi na daga cikin wadanda kungiyar ke harin dauka a bazaran nan, amma kuma, idan kungiyar ta fadi daga gasar Firmiya kila ta karkata ga tsohon dan wasanta Robbie Keane, wanda yanzu yake horad da Ferencvaros ta kasar Hungary. (GiveMeSport).
Manchester United na shirin tattaunawa da dan wasan tsakiya na Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 31, bayan gasar Kofin Duniya da za a yi a bazaran nan. (Football Insider).
Chelsea da Manchester City na daga cikin kungiyoyin da suke sha'awar dan wasan tsakiya na Bayern Munich, Aleksandar Pavlovic na Jamus mai shekara 21, wanda ake ganin zai iya kaiwa yuro miliyan 65. (Caught Offside).