Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne ƙawayen Iran da suka rage?
Yankin gabas ta tsakiya yana cikin barazanar faɗawa gagarumin yaƙi bayan harin da Isra'ila da Amurka suka kai kan Iran a ranar Asabar.
Iran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-haren kan sansanonin Amurka a yanking Gabas ta Tsakiya.
Iran ta kai harin makamai masu linzami ne a ƙasashe irinsu Jordan, Qatar, Kuwait, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Bahrain, Saudiyya da Isra'ila.
Duka waɗannan ƙasashen ƙawayen Amurka ne, kuma suna da kyakkyawar alaƙa da maƙociyarsu Iran, wadda tuni ta yakice duk wata alaƙarta da Amurka, amma kuma Isra'ila na da ƙarfin iko a yankin gabas ta tsakiya.
Ƙungiyoyi irinsu Hamas a Gaza, da Hezbollah a Lebanon, da 'yantawayen Houthi a Yemen da wasu masu tada ƙayar baya a Syria da Iraqi da ake musu kallon 'yan ta'adda sun daɗe suna farmakar Isra'ila.
Tehran na ci gaba da neman ƙawance daga wasu masu adawa da Amurka, kamar su shugaban Rasha Vladimir Putin, da tsohon shugaban Syria Bashar Al-assad da tsohon shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro.
Sai dai, ƙawancen da ke tsakanin waɗannan ƙasashe yana raguwa a 'yan kwanakin nan bayan an tsige wasu daga mulki.
Maduro yana zaman kaso a gidan yarin Amurka yayin da Bashar Al-assad ya ɓuya tun bayan hamɓarar da gwamnatinsa.
Ita kuwa Hezbollah an rage mata ƙarfi tun bayan hare-haren da Isra'ila ta kai mata, yayin da ita ma Hamas da alama ta samu naƙasu bayan yaƙin ta da Isra'ila a Gaza.
Mun yi nazari kan ƙasashen da suka daɗe suna ƙawance da Iran a yankin da kuma waɗanda za su ci gaba da alaƙa da ita.
Iran ta rasa ƙawancen Syria
Syria ta kasance abokiyar Iran ta kusa a zamanin Bashar al-Assad, wadda ta yi amfani da shi wajen samun ƙarfin faɗa a ji a yankin larabawa. Sai dai, ƙawancen na su ya samu tasgaro bayan an hamɓarar da gwamnatin Assad a shekarar 2024.
Sabon shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa, wanda Musulmi ne mabiyi aƙidar Sunni, ya janye daga cikin haɗakar masu adawa da Amurka, inda ya fara alaƙa da Trump, har da kai masa ziyara a fadar White House.
Ƙungiyar Hezbollah, da ke tada ƙayar a Lebanon ta kasance aminiyar Iran a baya, amma yanzu ta samu koma baya tun bayan da aka koma kai kayan agaji ta Iraƙi da Syria
'Yan tawayen Houthi a Yemen
'Yan tawayen Houthi na daga cikin ƙawayen Iran a yankin gabas ta tsakiya, inda ƙungiyar ta ƙara ƙarfi tun bayan karya lagon Hezbollah a Lebanon.
'Yan tawayen Houthi mabiya aƙidar Shia na juya kashi 30 na Yemen, kuma ana zarginsu da cin zarafin jama'a da take haƙƙin bil'adama a zamaninsu.
An kafa ƙungiyar ne a shekarar 1990, kuma yawancin mambobinta 'yan mazahabar Zaidi ne, waɗanda ba su da yawa a mabiya aƙidar Shia a Yemen. Yawanci suna zaune ne a arewacin ƙasar mai yawan mutum miliyan 33.
Hare-haren da wannan ƙungiyar take kaiwa kan Amurka sun zafafa tun bayan yaƙin Gaza da ya ɓarke a ranar 7 ga watan Oktoba 2023.
Sau da dama wannan ƙungiyar tana harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila, duk da yake Isra'ilan tana harbo su.
A shekarar 2025, Amurka ta kai hari kan sansanonin Houthi sama da 1000 a Yemen, a yunƙurin ta na ƙarya lagon ƙungiyar.
Hezbollah
Ƙungiyar Shia ta Hezbollah a Lebanon, babbar aminiyar Iran har zuwa shekarar 2024.
An kafa Hezbollah a shekarar 1982, domin yaƙi da Isra'ila, amma ta ƙara faɗaɗa da mayaƙa sama da 30,000 a Lebanon.
A tsawon shekaru da dama, Hezbollah tana samun tallafin kuɗaɗe da samun horo daga gwamnatin Iran.
Sai dai yaƙin Gaza ya hargitsa komai a yankin.
A lokacin da Hamaza ta kaiwa Isra'ila hari a shekarar 2023, Isra'ila ta maida martani masu zafi ta hanyar yin ruwan bama-bamai a Gaza, inda Hezbollah ta kai hare-hare a kusa da iyakar Isra'ila da Lebanon.
Isra'ila ta maida martani mai zafi ta hanyar kai hare-hare ta sama, inda ta kashe shugaban ƙungiyar Hassan Nasrallah tare da dubban mayaƙan ƙungiyar.
Karya lagon Hezbollah ya taimaka wajen kifar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Sai dai duk da haka, Hezbollah na da ƙarfin kaiwa Isra'ila hari.
Ƙungiyoyin 'yantawaye a Iraƙi
A ƙarƙashin wannan ƙawance, akwai ƙungiyoyi tawaye na 'yan Shia da suke da kyakkyawar alaƙa da Iran, wadda take ba su kuɗaɗe da makamai.
Waɗannan ƙungiyoyin da ake kira da Public Mobilization Forces (PMF), wata haɗakar ƙungiyoyin 'yan tawaye ne da ke da alaƙa da sojojin Iraƙi, kuma yawancinsu suna karɓar umarni ne daga jagoran addinin Iran Ali Khamenei.
A baya-bayan nan ana kiran su da da "Dakarun Musuluncin Iraƙi", kuma sun kai hare-haren jirage marasa matuƙa a Isra'ila.
An kashe mayaƙan ƙungiyar da dama a yayin fashewar wani abu a yankin Jurf al-Sakhar da ke Baghdad a ranar Asabar, kamar yadda kakakin ƙungiyar ya shaidawa Reuters.
Daya daga cikin jagororin ƙungiyar Kataib Hezbollah ya shaidawa mayaƙansa su shirya fafatawa a dogon yaƙi idan har Amurka ta kaiwa Iran hari.
Hamas
Ƙungiyar mayaƙan Falaɗinawa, ta daɗe tana samun kuɗaɗe da horo daga Iran, amma ita ma an karya lagon ta a yaƙin da aka yi a Gaza a tsawon shekaru biyu.
Duk da yake ƙungiyar na ci gaba da iko da zirin Gaza, amma ba ta da ƙarfin ƙaddamar da hare-hare masu ƙarfi.
Isra'ila ta kashe jagoririn siyasa da na sojinta da dama ciki har da Ismael Haniya, wanda aka kashe shi a wani harin da Isra'ila ta kai a Tehra a shekarar 2024.
Sauran sassan duniya
Iran na ci gaba da yauƙaƙa alaƙarta ata soji da tattalin arziki da Rasha a 'yan shekarun nan, inda take samun makamai da kuma fasaha daga Rashar da kuma kaucewa takunkuman ƙasa da ƙasa.
Rasha dai ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Isra'ila suka kai Iran a ranar Asabar, inda ta ce ƙasashen biyu sun jefa yankin gabas ta tsakiya cikin gagarumin rikici.
Bugu da ƙari, Kremlin na son inganta alaƙarta da wasu ƙasashe masu muhimmanci a yankin irinsu Saudiya da UAE.
Yanayin danganta tsakanin Rasha da Amurka tun bayan komawar Trump kan mulki na iya zama dalilin da ya sa Moscow take jan ƙafa wajen maida martani game da harin da suka kai Iran.
China ma ta buƙaci a yi gaggawar tsagaita wuta inda ta yi kiran a mutunta 'yancin ƙasar Iran.
Beijing ta zama babbar abokiyar kasuwancin Tehran.
A shekarar 2025 n e China ta saye kashi 80 na man Iran, lamarin da ya haifar da kakkausar suka da Amurka.
Duk da wannan alaƙa, Beijing tana da tata buƙatar a matakin ƙasa da ƙasa wanda ya sa ta ƙi shiga yaƙin dumu-dumu.
Iran na da kyakkyawar alaka da Koriya ta Arewa, kuma alaƙarsu ta fara ne tun a shekarar 1980 a lokacin yaƙin Iran da Iraƙi.
Iran ta kuma ci gaba da hulɗa da Venezula tun a shekarar 2000 bayan da Caracas da Tehran suka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci.