Me ya sa wasu ke fargaba kan ƙirƙiro ƴansandan jihohi a Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 2

Batun samar da ƴansandan jihohi a Najeriya na ci gaba da haifar da cecekuce a ƙasar musamman bayan ƙaddamar da sabon kwamiti da zai bayar da shawarar yadda za a samar da su.

A ranar Laraba ne sabon Sufeto Janar na 'yansandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya kaddamar da kwamitin mutum bakwai da zai fito da hanyoyin tabbatar da ƴansandan jihohi a ƙasar.

Tun da farko shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya bukaci majalisun tarayya guda biyu da su yi wa kundin tsarin mulkin 1999 kwaskwarima domin samar da tsarin doka da zai bayar da damar kafa 'yansandan jihohi.

Sai dai ƙungiyoyin farar hula musamman na kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya da ma na ƙasashen waje sun fito suna sukar matakin.

Kungiyar kare hakkin ɗan'adam ta ƙasa da ƙasa International Human Right Commission- Relief Fund Trust na cikin waɗanda suka fito suka fargaba game da matakin samar da ƴansandan jihohi a Najeriya.

Kungiyar ta yi suka ne saboda illolin da take ganin suna tattare da hakan ta fuskar tsaro da kare haƙƙin ɗan'adam, ciki kuwa har da fagabar ana iya yin amfani da 'yansandan na jihohi a harkokin siyasa wajen muzguna wa abokan hamayya.

Sannan ƙungiyar ta yi la'akari da yadda wasu jihohin ba su da ƙarfin kuɗin kula da hidimar ƴansanda.

"Muna ganin gwamnoni ko ƴansiyasa za su iya amfani da su wajen siyasantar da tsarin musamman wajen amfani da ƴansandan wajen murƙushe abokan hamayya da kuma haifar da rikici da bambanci na kaɓila da addini," kamar yadda Abdullahi Bakoji Adam, shugaban IHRC Relief Fund Trust reshen Najeriya ya shaida wa BBC.

Ya kuma bayyanar fargabar ƙaruwar take haƙƙin ɗan'adam a Najeriya musamman cin hanci da rashawa da kuma amfani da ƙarfi.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ana nazari kan batun samar da yansandan jihohi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da ƙasar ke yi na inganta harakokin tsaro.

A cewar Sufeto-Janar na 'yansandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu, aikin kwamitin da ya kafa shi ne nazarin batun samar da 'yansandan jihohi a wani ɓangare na kokarin karfafa tsarin tsaron cikin gida na Najeriya da inganta ayyukan 'yansanda ta hanyar kai shi kusa da jama'a.

Ya ƙara da cewa an ɗora wa kwamitin alhakin yin nazari kan ayyukan yansanda a ciki da wajen Najeriya da tantance buƙatun tsaro na al'umma da kuma bayar da shawara kan tsare-tsaren da suka dace wajen kafawa.

Kwamitin zai bayar da shawara kan tsarin da ya dace a bi wajen ɗaukar aikin ƴansandan na jihohi da bayar da horo da kuma tsara ka'idojin aiki.

Shugaban Tinubu ya sha nanata cewa gwamnatinsa za ta samar da ƴansandan jihohi a matsayin wani mataki na magance matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta.

Kuma tuni majalisar tarayyar ƙasar ta fara bin tsarin yin gyara ga kundin tsarin mulki domin samar da damar kafa yansandan jihohi.

Wasu masu sharihi na ganin samar da ƴansandan jihohi zai iya haifar da matsaloli da dama fiye da gyaran da ake tunanin za a samu ta fuskar tsaro.

Suna ganin idan har gyara ake so ana iya inganta jami'an tsaron da ake da su tun daga ƴansanda da masu tsaron farin kaya ƴan civil defence ta hanyar ƙara masu makamai na zamani da horo da kuma inganta rayuwarsu.