Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Mojtaba Khamenei, wanda ake hasashen zai zama jagoran addinin Iran?
- Marubuci, BBC News Persian
- Lokacin karatu: Minti 4
Bayan kashe jagoran addinin Iran, Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila a Iran, sai aka fara tunanin ko ɗan marigayin Mojtaba wanda shi ma yake da ƙarfin faɗa a ji ya rasu.
Sai da aka yi kwanaki ba a ji ɗuriyarsa ba, kuma babu tabbaci. Sai a ranar Talata 3 ga watan Maris ne kafofin watsa labarai suka tabbatar da cewa Mojtaba yana raye, kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai har yanzu bai fito ba.
Yanzu yana cikin na gaba-gaba a cikin waɗanda ake hasashen za su iya maye gurbin jagoran addinin ƙasar, kamar yadda kafar Reuters ta ruwaito daga wasu majiyoyi guda biyu a Iran.
Bayan haka, majalisar ƙwararru mai mambobi 88, wadda ke da alhakin naɗa sabon jagoran addinin ana cewa ta yi nisa a aikin naɗin sabon jagoran, duk da cewa zai yi wahala a sanar da sabon jagoran kafin a yi jana'izar marigayin.
Mojtaba, ba kamar mahaifinsa ba ne, domin ba a san shi sosai ba, kuma bai taɓa riƙe wani muƙamin gwamnati ba, sannan bai taɓa zantawa da menama labarai ba ballanta jawabi a wajen taro. Haka kuma tsirarun hotunansa da bidiyo ne kawai aka gani.
Sai dai duk da haka, raɗe-raɗi na nuna cewa yana da ƙarfin faɗa a ji a gwamnati, inda wani rahoton ofishin jakadancin Amurka, wanda WikiliLeaks ya fitar a tsakankanin 2000s ya bayyana shi a matsayin "jagora mai ƙarfin faɗa a ji, kuma jigo a gwamnatin mahaifinsa," in ji AP.
Amma dai naɗin Mojtaba zai iya zuwa da ƙalubale. Kasar ta zama Jamhuriyar Musulunci ne a shekarar 1979 bayan kifar da mulkin sarauta, inda aka tsara jagoran addinin ya kasance mutum mai ilimin addini da fasahar shugabanci, ba gado ba.
Khamenei ba ya so ɗansa Mobtaba ya gaje shi, kamar yadda wani mamba a cibiyar ƙwararru ya bayyana kimanin shekara biyu da suka gabata, duk da cewa shi bai taɓa faɗa ba.
Don haka wane ne Mojtaba Khamenei?
An haife shi ne a ranar 8 ga watan Satumban 1969 a arewa maso gabashin birnin Mashhad, kuma shi ne na biyu a cikin yaran Khamenei guda shida. Ya yi karatun sakandare ne a makarantar addini ta Alavi da ke Tehran.
Yana shekara 17 ne ya shiga aikin soja a lokacin yaƙin Iran da Iraq, kamar yadda kafar watsa labaran Iran ta bayyana. Yaƙin wanda ya yi matuƙar muni na cikin abubuwan da suka ƙara lalata alaƙa tsakanin Iran da Amurka da sauran ƙasashen yamma saboda yadda suka goyi bayan Iraqi a yaƙin.
A shekarar 1999 Mojtaba ya koma Qom, wanda wani birni ne mai muhimmanci wajen karatun aƙidar Shi'a.
Ana dai ganin Mojtaba a matsayin malami mai matsakaicin ilimi, wanda hakan zai iya zama ƙalubale a gare shi wajen zama jagoran addinin ƙasar.
A ƴan kwanakin nan ne dai wasu kafofin watsa labarai da ke kusa da gwamnatin ƙasar suka fara bayyana Mojtaba da "Ayatollah", wanda matsayi ne babba na malanta a ƙasar.
Sai dai wasu na ganin ana haka ne domin a ɗaga darajarsa a fagen ilimi domin bayyana shi a matsayin wanda ya cika sharuɗan zama jagoran addinin.
Amma shi Ali Khamenei ya zama "Ayatollah" ne bayan ya zama jagoran addinin ƙasar na biyu a shekarar 1989.
Zargin shiga siyasa
An fara jin suna Mojtaba ne a zaɓen 2005 na shugaban ƙasar Iran, wanda Mahmoud Ahmadinejad mai ra'ayin mazan jiya ya lashe.
Bayan nasarar ne, Mehdi Karroubi ya rubuta wasiƙar zuwa ga Khamenei, inda ya zargi Mojtaba da katsalanda a zaɓen ta hanyar amfani da dakarun juyin juya-hali da dakarun Basiji, waɗanda suka riƙa raba kuɗi ga masu zaɓe domin taimakon Ahmadinejad.
Bayan shekara huɗu, Mojtaba ya sake fuskantar wani zargin, inda sake lashe zaɓen Ahmadinejad ya haifar da zanga-zanga a ƙasar da ake kira da gwagwarmayar Green Movement.
Mostafa Tajzadeh, wanda mataimakin ministan harkokin cikin gida ne a lokacin ya bayyana sakamakon zaɓen a matsayin "juyin mulkin zaɓe." An ɗaure shi shekara bakwai saboda wannan, wanda kuma ya alaƙanta da "umarnin Mojtaba Khamenei".
Haka kuma an yi wa wasu masu sauƙin ra'ayi guda biyu Mir-Hossein Mousavi da Mehdi Karoubi ɗaurin talala bayan zaɓen. A watan Fabrairun 2012, Mojtaba ya gana da Mousavi, inda ya buƙace shi da ya haƙura, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.
Masana suna tunanin Mojtaba zai ɗaura daga inda mahaifinsa ya tsaya na ɗaukar matakai tsaurara, wasu ma suna ganin mutum da ya rasa mahaifinsa da mahaifiyarsa da matarsa a hare-haren Amurka da Isra'ila, zai fi zafin rai da ƙin amincewa da ƙasashen yamma.
Amma zai fuskanci ƙalubalen tabbatar da wanzuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma bayyana wa mutane cewa zai iya aikin, musamman fitar da ƙasar daga matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki da siyasa.