Harin ramuwar gayyar da Ukraine ke kai wa na tafiyar wahainiya

Tankunan yaki

Asalin hoton, TELEGRAM

Yakin da ake yi a Ukraine ya kai makura, inda ya kai an fara hasashen makomar kasar da kuma yadda zai shafi bangaren tsaron nahiyar Turai.

Tun bayan watanni 18 da Rasha ta fara mamaya a Ukraine din, kasar ke kare kanta daga dakarun Rasha da ke kwace mata iyakoki.

To amma, a baya bayan nan,Ukraine tare da taimakon wasu kasashen yamma na mayar da martani ga hare-haren Rasha inda har ta ke kokarin fatattakar sojojin Rashan daga yankunanta da suka mamaye a gabashi da kuma kudancin kasar.

To ko a cikin watanni biyun da Ukraine ke mayar da martani a hare-haren da ake kai mata kwalliya ta biya kudin sabulu?

BBC ta yi nazari a kan wani bidiyon yakin Ukraine da kuma tattaunawar da ta yi da kwararru ta gano amsar wannan tambaya.

Bisa la’akari da irin fafatawar da aka yi a gabashi da kuma kudancin Ukraine, na gano cewa babu wani sauyi sosai da aka samu a yankunan saboda har yanzu sojojin Rashan na rike da garuruwa da dama na Ukraine, illa dai akwai wasu garuruwa kalilan da sojojin Ukraine din suka kwato.

Har yanzu Rasha na rike da kashi daya bisa biyar na Ukraine ciki har da biranen Donetsk da kuma Mariupol.

A takaice dai a cikin watanni tara wato tun daga watan Nuwambar 2022 kawo watan Augustam 2023, ba a samu wani sauyi ba, domin a tsakanin wannan lokaci ne Ukraine ta yi ta kokari ta kwace kudancin birnin Kherson da kuma wasu yankuna a arewa maso gabashin kasar.

A baya bayan nan Ukraine ta ce dakarunta sun kwace kauyen Staromaiorske da ke yankin Donetsk.

Taswira

BBC ta tabbatar da bidiyon da Ukraine din ta ce ta kwato wasu yankuna a kusa da Bakhmut, inda aka gwabza kazamin fada.

Kazalika Ukraine din ta dan yi rawar gani a yankin Zaporizhzhia da ke kudanci