Yaya yanayin hunturu zai shafi yaƙin Ukraine?

Asalin hoton, Getty Images
Nan da ɗan wani lokaci kaɗan ake sa ran shiga hunturu mai tsanani a Ukraine, wannan kuma na iya zama babban kalubale ga dakarun Ukraine yayinda suke kokarin ƙwato yankunansu daga hannun Rasha.
Rasha na kuma iya jefa al’ummar Ukraine cikin yanayin sanyi mai muni ta hanyar kai hari cibiyoyin makamashi da defon man fetur.
Yaya yanayin sanyi a Ukraine?
Tsakanin watan Disamba zuwa Maris, yanayin na kai wa tsakanin kashi 4.8 zuwa 2 na ma’aunin salshiyos.
A matsakaicin yanayi, ana shafe kwanaki 14 ana zubar dusar kankara a Disamba, kwanaki 17 cikin watan Janairu da kuma 15 a cikin watan Fabarairu. A cikin wadannan shekaru adadin kankarar da ke zuba na kai miliyan 1.5.
Sai dai, sanyin bai fiya tsanani a kudancin kasar ba, da kuma yankin tekun Black Sea da arewacin kasar.
Ta yaya hunturu zai shafi yaƙin Ukraine?
A arewaci yankin Kyiv, yanayin sanyi ya soma sosai.
A Janairu, sanyin yana kai wa maki -3.8 a ma’aunin salshiyos sannan cikin dare yanayin na tsanani sosai domin yana kai wa har maki -6.1C.
Sai dai, a yankin Kherson da ke kudancin, yanayin sanyi na kai wa har maki -0.9. Idan an samu sauki yakan tsayawa a kan maki -3.7 na ma’aunin salshiyos.
Wannan na nufin a yankunan da ke arewa maso gabashin Ukraine, yanayin sanyi na kaɗawa sosai da kankare kusan ko ina.
Ko da yake, a Kherson hunturu na tafe da kuma ruwan sama ne a wasu lokutan.
Me hakan ke nufin ga sojojin da ke yaƙi?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsananin sanyi da zubar dusar kankara za su jefa ayyukan dakarun cikin yanayi mai matsanancin gaske musamman ta fanin kai-komo da tuka ababben hawansu cikin hanzari.
Wannan zai zama nakasu ga dakarun Ukraine, a cewar Forbes Mackenzie, shugaban cibiyar tattara bayanan sirri ta Mackenzie, saboda hakan zai haifar da tsaiko wajen kai farmaki ko samun nasara a yakinsu.
"Ukraine za ta so yanayin ya kasance mai sanyi gaske, ko ina ya kankare saboda su ci-gaba da samun damar dabarun daƙile dakarun Rasha," a cewarsa.
"Sai dai, Rasha za ta so yanayi ya kasance mai ɗumi, saboda idan ana samun yanayi na ruwa Ukraine za ta fuskanci koma baya.
Ayyukan Ukraine a Kherson tuni ya soma fuskantar barazana saboda tsananin ruwa a watan Oktoba.
Babbar kalubale ga Ukraine da Rasha shi ne yadda za su ci-gaba da kai wa dakarunsu makamai.
"Sojoji na bukatar abinci sosai a lokacin hunturu, sannan suna bukatar fetur saboda su dumama kansu, a cewar Ben Barry, wani babban masani kan harkokin yanayi.
"Kodayake, kowanne bangare ya saba da yanayin sanyi, kuma kayayyakinsu da makamai an ƙerasu ta yarda sanyi baya musu lahani, don haka hunturu ba zai hana dakarun yakar junansu ba," a cewarsa.
Yaya za a yi yanayin hunturu ya shafi yaƙin?
Kwararru da dama a fanin tsaro na ganin a lokacin hunturu, dakarun Rasha da Ukraine za su mayar da hankali kan amfani da makaman artilary maimakon sauran makamai.
"A lokacin hunturu, ana shan wahala wajen iya kai mu su kayayyaki, sannan sojoji sun fi tsintar kansu cikin wahalar karancin makamai da abinci," a cewar Marina Miron, kwararriya kan harkar tsaro a Jami’ar Kings da ke Landan.
"Bangarorin biyu za su ke amfani da artilary mai cin-dogon zango da jirage marasa matuka domin isa ga yankunan da za ake shigar musu da kayayyaki da defon ajiya, domin cin karfin makiya.
Sai dai kuma, yanayi na gajimare da dusar kankara na iya shafar kowanne ɓangare – sai dai idan za su ke amfani da na’urorin kiyayye hadura.
Rasha za ta farwa fararan-hula a lokacin hunturu?

Asalin hoton, Getty Images
Rasha ta sha kaddamar da hare-hare kan fararan-hula da unguwannisu da abubuwan amfaninsu irinsu tashar wutar lantarki da ruwan sha.
Orysia Lutsevych, wata shugaban al’umma ce ta Ukraine a Chatham House, ya ce akwai yiwuwar wannan tsari ya ci-gaba har zuwa bayan hunturu.
"Fararan-hula za su ci-gaba da fuskantar hare-hare kan gine-ginensu, saboda a hannsu dumama jiki, a cewarta.
"Yanzu mutane sun raja'a wajen amfani da itattuwa maimakon fetur, sannan suna ta sayen risho da acibalbal. Wurare irinsu asibitoci na sayen janarata na kansu".
Tsare-tsaren Rasha yanzu haka na karkashin kulawa Janar Sergei Surovikin, saboda mutumin da aka naɗa a matsayin babban hafsan sojojin Ukraine.
Ana masa laƙabi da "General Armageddon" saboda kwarewarsa a lokacin yaƙin da ya jagoranta a Syria da wasu muhumman wurare.
Burinsa shi ne ruguza duk wata al'umma ta Ukraine a cewar Ms Miron.
"Rasha na ganin cewa idan mutane suka shiga yanayi na tsananin sanayi da takura, za su iya yin bore ga gwamnatinsa,"a cewarsa
Sai dai Ms Lutsevych ta ce Ukraine ta shiryawa wannan hunturu.
"Sun cike rumbun ajiyarsu ta gas, sannan sun tanadi man fetur da dizal, a cewarsa.
"Mutane sun fahimci cewa Rasha ba za ta yi nasara a wannan yaƙi ba, kuma idan har suka iya jurewa hunturun, za su samu gaggarumar nasara kan Rasha.











