Bayanan kwarmato: Dakarun Ƙasashen Yamma suna taya Ukraine yaƙi a cikin ƙasar

Asalin hoton, Reuters
Gomman takardun bayanan sirrin Amurka ne da aka kwarmata a yanzu suke ci gaba da yawo a intanet.
Kwafe-kwafe na takardun sirrin sun bayyana a shafukan sada zumunta na manhajoji kamar Discord tun cikin watan Fabrairu.
Cike har da bayanan lokaci da gomman zaurancen sojoji, wasu takardun ma an buga musu hatimin "babban sirrin ƙasa", sun yi bayani dalla-dalla game da yaƙin da ake yi a Yukren, sun kuma ba da bayanai game da ƙasar China da kuma manyan ƙasashen ƙawancen Amurka.
An ambato jami'ai a ma'aikatar tsaron Pentagon suna cewa takardun sahihai ne.
BBC da sauran kafofin labarai sun yi nazari kan wasu daga cikin takardun bayanan ga kuma wasu daga cikin muhimman abubuwan da aka gano.
Dakarun tsaron Ƙasashen Yamma na musamman na aiki a Ukraine
Wata takarda mai kwanan watan 23 ga watan Maris ya yi bayani game da kasancewar wani ƙanƙanin adadi na dakarun musamman na Ƙasashen Yamma a cikin Yukren.
Ba ta dai yi ƙarin haske a kan taƙamaimai irin ayyukan da suke yi a can da kuma a inda suke ba. Burtaniya ce take da dakaru mafi yawa guda (50), sai Latvia mai (17), Faransa (15) akwai Amurka mai dakaru (14) sai ƙasar Holland mai dakare (1).
Gwamnatocin ƙasashen Yamma suna kauce wa yin ƙarin bayani a kan irin wannan batu mai matuƙar muhimmanci, sai dai mai yiwuwa Rasha cikin gaggawa za ta yi amfani da waɗannan bayanai
A 'yan watannin nan dai hukumomin Moscow sun bayyana cewa ba da sojojin Yukren kawai suke yaƙi ba, har da na ƙungiyar tsaro ta Nato.
Sauran takardun sirrin sun yi bayani a kan lokacin da wasu rundunonin yaƙin Yukren - da ake shiryawa don ƙaddamar da hare-hare, nan da 'yan makwanni za su kammala shiri. Sun bayyana lissafi dalla-dalla na tankunan yaƙi da motoci masu sulke da makaman atilare da Ƙasashen Yamma abokan ƙawance ke samar wa Yukren.
Wata taswira ta ƙunshi bayanan canji yanayi a tsawon lokaci da ke ƙididdige yanayin ƙasa a faɗin gabashin Yukren daidai lokacin da bazara ke ci gaba.
A cewar jaridar Washington Post, wata takardar bayanan sirri daga farkon watan Fabrairu ta bayyana wasu-wasi game da yiwuwar samun nasarar Yukren a hare-haren mayar da martani da za ta ƙaddamar, tana cewa matsalolin tattarowa da kula da isassun dakarun soja tsawon lokaci na iya sanadin "'yar taƙaitacciyar nasarar ƙwato yankuna".
Ko wanne ƙarin haske agarumin kwarmaton bayanai kan yaƙin da Ukraine ke yi mana?
An yi zuzzurfan nazari kan wahalhalun da Ukraine ke sha wajen kare sararin samaniyarta, da kuma gargaɗi a watan Febrairun cewa maƙaman rokan Kyiv za su iya ƙarewa.
An kuma bayyana irin asarar da aka yi a yaƙin. Wasu bayanai na cewa sojojin Rasha 223,000 aka kashe ko kuma aka jikkata, yayin da Ukraine kuma ke da soji 131,000 da ko dai aka kashe ko kuma aka raunata.
Wasu jami'an Ukraine sun musanta waɗannan bayanai da aka kwarmata, inda suka ce kaddamar da wani kamfe na yaƙi da labaran ƙarya daga Rasha. Sai dai akwai kuma alamun fushi a tattare da su.
Wani mai taimaka wa shugaban ƙasar Ukraine, Mykhailo Podolyak, ya wallafa a shafin twita cewa "Bai kamata mu mayar da hankali kan waɗannan bayanai da ba na gaskiya ba, illa kawai hankali ya koma kan yadda za a samo manyan maƙamai don kawo karshen yaƙin baki-ɗaya."

Asalin hoton, Getty Images
Masar na shirin aika wa Rasha makaman roka cikin sirri
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wasu takardu da jaridar Washington Post ta samu a tsakiyan watan Febrairu, ta gano cewa Masar na shirin aika wa Rasha maƙaman Roka guda 40,000 cikin sirri.
Jaridar ta ce shugaba Abdul Fatah al-Sisi ya faɗa wa jami'ai cewa su ci gaba da yin aikin samar da maƙaman da kuma aika su cikin sirri "don guje wa matsaloli da ƙasashen yamma".
An ruwaito wani jami'i na cewa zai tabbatar wajen ganin mutanensa sun yi aiki tukuru idan ta kama, saboda shi ne abun da Masar za ta iya yi don biyan Rasha kan taimakon da ta yi wa ƙasar tun da farko". Sai dai ba a san wane irin taimako ne Rashar ta yi wa Masar ɗin ba tun da farko.
A watan Janairu, kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya bayar da rahoton cewa, kason Rasha na shigo da alkama daga Masar ya karu a shekarar 2022.
Babu wata alama da ke nuna cewa Masar ta ci gaba da shirin sayar wa Rasha alkaman.
Ba a sani ba ko hakan ya faru ne sakamakon gargaɗin da ya fito daga Washington ba.
Sai dai Masar na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samun tallafin tsaro daga Amurka, wanda kuɗinsa ya kai kusan $1bn a shekara, wanda ke baiwa gwamnatin Amurka damammaki.
Wani jami'i da ya nemi a sakaya sunansa da ya yi magana da kafar yaɗa labaran Masar, ya bayyana zargin da ke cikin takardar a matsayin "marasa tushe balle makama" inda ya ce Alkahira ba ta da wani ɓangare a yakin.
A halin da ake ciki Kremlin ta bayyana zargin a matsayin "jita-jita ne kawai".
Kan Koriya ta Kudu ya rabu game da aika wa Ukraine maƙamai
Wata takardar sirri, wanda BBC ta gani, ya nuna cewa kan jami'an Koriya ta Kudu ya rabu game da sayar wa Ukraine maƙaman da za ta yi amfani da su.
Rahoton, bisa ga bayanan sirri, ya ba da cikakken bayani game da tattaunawa mai mahimmanci tsakanin masu ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa.
An yi ta ce-ce-ku-ce kan matsa wa da Amurka ta yi na aike wa da maƙamai zuwa Ukraine da kuma manufarsu ta kar a ba wa ƙasashen da ke yaƙi makamai.
Ɗaya daga cikin masu ba da shawara, ya ba da shawarar a aika da harsasai zuwa Poland, don kaucewa bayar da kai ga Amurka.
A wani ɓangare na yarjejeniyar mayar da kayayyaki a bara, Seoul ta dage cewa Amurka ba za ta iya miƙa harsasan ga Ukraine ba.
Ita dai Seoul ta ki amincewa da bai wa Ukraine maƙamai, saboda fargabar fushin da Rasha za ta yi.
Wannan leƙen asiri ya sa an fara nuna damuwa kan tsrao a birnin Seoul, inda 'yan siyasa na ɓangaren adawa ke nuna shakku kan yadda Amurka ta samu damar shiga irin wannan tattaunawa mai girma.
China ta yi gwajin maƙamai mai karfin gaske a watan Febrairu
Jaridar Washington Post ta kuma gano cewa, Beijing ta yi gwajin ɗaya daga cikin maƙami mai linzami na DF-27 - a ranar 25 ga watan Febrairu.
Maƙamin ya yi tafiyar minti 12 a nisan kilomita 2,100, a cewar takardun.
Jaridar The Post ta ruwaito cewa akwai yiwuwar gwajin maƙamin da aka yi, ya iya kutsawa zuwa cikin makamai masu linzami na Amurka.
Binciken su ya kuma haɗa da cikakkun bayanai kan wani sabon jirgin ruwan yaƙi na ƙasar China da harba makamin roka a watan Maris wanda zai kara karfin taswirar ƙasar China.











